chapter 1

264 19 2
                                    

Godiya ta tabbata ga Allah mai kowa mai komai mahaliccin sammai da kassai, salati da aminci su tabbata ga annabi Muhammad (s a w) da ahlin gidansa da sahabbansa da masoyansa baki daya.
Wannan littafi sadaukarwane ga dukkanin wani almajiri dake doran duniya, Wanda dole ta saka almajiranta ba son rai ba, ina fata da rokon ubangiji ya tallafi rayuwarsa yasaka haske cikinta ya kareshi daga dukkan fituntunin rayuwa ameen.

Wannan littafi nawa kirkirarren labarine babu wani labari ko suna da nayishi domin wani duk wanda yaji wani abu daya danganci rayuwarsa dacene.

Ina neman alfarmar kar wanda ya copy labari domin kirkiratace mallakinane.

Ina barar addu'arku ga daya daga cikin twins dina da Allah ya dau ranta ( Safeena Muhammad) Allah ya jikanta yasa mai cetoce ameen

.............................

Zamfara State.
Kauyen gidan ajinna dan karamin kauyene dake cikin surkukin daji a garin kauran namoda dake jihar zamfara, kauyene mai albarkar noma da kiwo mazauna kauyen yawancinsu fatakene daga kasar Niger tun shekaru da dama da suka wuce, dan haka kauyen ya kasance kusan kowa dan uwan kowane kuma sun dauki junansu a matsayin yan uwan suna mutunta juna tare da hadin kai.

Bayan wasu zamaninnika gomnatin ta zamfara ta gina musu makarantar primary tare da basu malamai duk da malaman nasu ma manoma ne dan haka ana cewa ruwa ya sauka karatu ya kare idan ka tura dankama sai dai yaje ya taya malam noma a tasa gonar, secondary kuma sai dai yaran kauyen suyi tafiya Mai nisa zuwa babban garin na kauran namoda. Makarantun addini kuwa babusu so, idan wani dan alaramma ya tayar da Yar tsangayarsa damuna nayi shikenan babu mai sake zuwa koda ko damunar ta wuce tofa an watsar da wannan tsangaya babu mai komawa sai dai a bude wata.

A takaice dai wannan kauye babu abinda suka dauka da muhimmanci Kamar noma shine babbar sana'arsu babban jigon rayuwarsu.

Can gaba da kauyen na gidan ajinna wasu gidaje ne jefi-jefi irin na ruga dinnan wadanda zakaga mutum ya Gina gidansa cikin gonarsa, gidan mal musa na daya daga cikin wadannan gidaje, gidane typical gidajenmu na karkara ginin kasa rufin kasa da dangar kara, mal musa na da mata guda biyu Jaru wacce take uwar gida mai 'ya'ya biyar uku maza sale habu da mudi sai biyu mata salama da bintu sannan kubra mai yara biyu maza yan biyu sai kuma tsohon cikin jikinta haihuwa yau ko gobe.

Kamar kusan kowanne gida na kasar hausa mai mata sama da daya haka gidan mal musa yake, akwai kishi mai tsanani tsakanin Jaru da kubra Wanda koyaushe laifin daga Jaru yake kasancewar Allah ya bawa kubra hakuri ba dan kadanba duk abinda Jaru zatayi mata abune mawuyaci kaga ko kai ta daga ta kalleta balle ta bata amsa, akwai banbancin shekaru sosai a tsakaninsu dan d'an mal musa ma na farko wato sale ya girmi kubra wannan dalilinne yasa Jaru ta tsaneta tana ganin an kawo mata yarinya Yar cikinta a matsayin kishiya, a haka da dadi ba dadi har Allah ya bawa kubra juna biyu, Jaru tayi bakin ciki sosai da wannan ciki tana ganin idan kubra ta haihu shikenan ta ragewa 'yayanta yawan gado duk da batasan gawar fariba.

Babu irin sulkullen da Jaru batayiba akan wannan ciki na jikin kubra Amma Allah cikin ikonsa sai da kubra ta haifesu, cikin tsananin wahala ta haifi yaranta maza masu kama daya tamkar an tsaga kara, fadin tashin hankalin da Jaru ta shiga sakamakon wannan haihuwa ma bata lokacine ita da bataso a haihuba sai gashi an haihun ba daya ba kuma har biyu gasu duk maza, Amma haka ta danne ta nunawa duniya tamkar tana murna akasha shagali yara sukaci suna Abdul Rahman da Abdul Rahim.

Tun daga kan su Abdul Rahman sai ya zamana duk cikin da kubra ta samu sai ya bare, duk sanda ta sami ciki zatayi ta mafarke mafarkene tana zabura bazata kuma lafiyaba har sai cikin ya fita, a haka har yan biyunta suka shekara takwas sannnan ta samu wannan dake jikinta tunda ta sameshi take cikin wahala shi bai zubeba bata kuma huta da wahalar ba, cikin ikon Allah gashi yanzu har yakai watan haihuwa duk da bakar wahalar da sukesha ita da cikin dama yan yaranta a wajen Jaru.

ALMAJIRI MA 'DA NE (Editing)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt