Kano, Nigeria.Koh da suka bar gidan Maamah suka kama hanya, wata hanya daban suka yi ba hanyar gida ba hakan ya sa khayri ta shiga nazarin koh ina zasu je.
'Qilan abu zai siya mu wuce' tayi tunanin a zuciyar ta. Bayan yan mintoci kadan sai gani tayi sun iso wani makeken gida Ya Kabeer ya juya kan mota towards the house ya fara honking, baa jima ba megadi ya leqo, ganin Kabeer ne ya sa ya koma ciki a guje ya fara bude musu gate din suka shiga. Zuwa wannan lokaci khayri ta saba da irin manya manyan gidajen da take gani da kuma wanda suke zuwa sabida ilahirin mutanen da surukan nata suke hulda da su masu kudi ne living in expensive houses, driving expensive cars. Tun khayri na comparing houses din in suka je tace wannan ya fi wancan har tazo ta gaji ta daina. Samun wuri yayi ya parking motarsa megadin gidan ya taho a guje har inda suka yi parking yana gaida Kabeer, daga gani dai ka san sun san juna sosai.
"Suna nan koh?". Kabeer ya tambaya megadin ya fadi masa cewar suna nan.
"Oga Ilyaas ne kawai yayi tafiya dazu amma su Alhajin suna nan". Kudi Kabeer ya ciro wanda zasu kai dubu biyar ya miqawa megadin wanda ya fara kwararo masa godia.
A hankula suka fara taku zuwa cikin gidan. Suna isa bakin qofa Kabeer yayi ringing bell, baa jima da haka ba wata yar karamar yarinyar da kwata kwata bazata wuci ten years ba ta buda qofar.
"Yayaaaaa" Ta haye jikin Kabeer da tsalle.
"Look at my Amaani. When did you come back?" Ya tambaye ta.
"Three days ago". Ta fadi in smooth English khayri dai tana ta kallonsu dan da alama sun shaqu sosai. Gashi yarinyar ta bata sha'awa.
"So how was Italy?". Ya sake tambaya ita kam Amaani ta fara basa labaran abubuwan da ta gani da kuma wuraren da taje. Sai da khayri tayi attishawa tukun Amaani tayi noticing dinta. Rad'a tayiwa Kabeer cikin kunne cewar wannan itace amaryar tashi shikuma yana murmushi yayi mata magana a hankula yana fadin "Yes she is. You want to say hi?". Kai ta daga eagerly sai a lokacin Kabeer ya sauke ta qasa.
"Amaani this Khayri, Khayri this is Amaani... My first love". Hakan ya sa dukansu yin murmushi. Khayri bata tsammani ba taji yarinyar tayi hugging dinta, itama hugging dinta back tayi Kabeer na musu tsiya yana wannan kishiyoyin basu da kishi.
Suna isa wani hadadden living room a gidan wanda ya hadu sosai Amaani ta ruga a guje tana fadin "I'll go get Maman and Papa". Sai bayan da ta wuce Kabeer din yayiwa khayri magana cewa su zauna. In less than ten minutes Amaani suka dawo wani dan tsohon mutum yana dauke da ita a kafadar sa, sai a gefen sa kuma wata matace wanda a shekaru zasu zama tsara da Maamah, matar baturiya me kyau da ita da fara'ar su suka shigo suna ma Kabeer magana cikin harshen turanci. Introducing din khayri yayi to Carlissa and Taneem Al-Fayeed wanda suka tarbe ta cike da farin ciki. Carlissa ta matso ta manna mata kisses on both cheeks kamar yadda suka saba a al'adar su ta masu farin fata shikuma Taneem cikin harshen hausa ya fara mata magana. Carlissa bata zauna ba sai da tayi hanyar kitchen dan umartan masu aiki da su kawo refreshments ma baqi. Ita kam Amaani qafan Kabeer ta dawo ta zauna tana wasa da wayanshi.
"Let me go get Zulaikha" Carlissa ta fadi tana miqewa. Tunda tayi maganan gaban khayri ya fara faduwa taji zuciyar ta ta fara bugawa furiously sabida shakkar haduwar ta da Zulaikha Al-Fayeed. Carlissa zata kai minti ashirin da shiga ciki ta futo kan Zulaikha ta futo takun ta daidai kamar wadda ke tsoron taka qasa. Tun kan khayri ta ganta ta fara shaqar kamshin turaren ta me dan karen kamshi.
Zulaikha kam dama ta riga ta san da zuwan Kabeer dan haka she took all evening getting ready for the meeting. Gayu tayi sosai ta sanya atamfar ta riga da skirt wanda ya sha dinki na azo a gani tayi daurin dan kwalin ta me kyau ta sha turaruka sai kamshi take. Da fara'ar ta ta shigo living room, kai tsaye Khayri ta dosa tana fadin ga amaryar mu cikin hausar ta da be gama futowa, da tayi sai ka san ba tsantsar bahaushiya bace ita. Dago kai khayri tayi suka hada ido duka zuciyoyin su sai da suka fadi. khayri a nata gefen shakkar Zulaikha take don a ganinta Zulaikhan ta fi ta da komi; kyau, wayewa, ilmi ga kuma favour din Ya Kabeer tunda khayri ta riga ta gama sanin cewa Zulaikha itace asalin wadda yike so sai dai ta rasa dalilin da yasa ya cewa su Dattijo yana son ta har ya aure ta bayan ba ita ce a ran sa ba. Ita kam Zulaikha abunda ya sa zuciyar ta bugawa shine tsananin kyaun da taga Allah yayiwa khayri bare yanzu da ta ganta tana ta sheqin amarci, dama can bata taba tsayawa ta mata kallo ba sosai sai ranar. Dan tsoro ta fara ji kar kyaun khayri ya sa Kabeer ya fara kula ta.
ВЫ ЧИТАЕТЕ
SANADI
Художественная прозаThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...