Babi Na Talatin Da Hudu (34).

796 142 17
                                    

Abuja, Nigeria.

Zaune take gaban Abban ta, ta sha adon alfarma in an off white coloured lace liffaya. Wa'azi yike mata me tsuma zuciya tare da fadi mata how proud he was of her kuma ya san a duk inda taje bazata basu kunya ba. A karshe ya mata addu'a da fatan neverending happiness and peace in her new home da kuma yara masu albarka. Ta dade jikin Abbanta, ta kwanta lamo kamar kar ta bar jikinsa wani sabon son sa ne ke qara shiga zuciyar ta.

"Ke ni daga ni kar wannan painting fuskar naki ya bata mini jallabia". Abdallah ya fadi playfully. Tare suka miqe ya riqo ta har dakin Ummin ta wadda tun safen ranar take ta sharar kuka, kukan rabuwa da sanyin idanunta. Her one and only beloved daughter zata tafi ta bar ta.

"Wai karima baki bar wannan kukan ba har yanzu". Abdallah ya fadi da ya shiga ya ganta zaune bisa kilishi ga sisters dinsa gefe sai faman rarrashin ta ake.

"Ina zan bar kuka Niima na zata tafi ta bar ni, ya zanyi da raina Alhaji. Ina zan iya rayuwa a qaton gidan nan ba tare da Niima na ba". Dariya sosai ta bashi dan haka yace mata.

"Toh ai sai ki maza ki hada kaya ki bi ta". Ita dai Niima tunda suka shigo ta wuce ta zauna gefen mahaifiyar ta ta dora kanta a shoulder din Ummin ta tana jin wani strong separation anxiety na kamata. Juyawa Abdallah yayi ya wucewar sa abunsa ya bar su. Da kadan da kadan mata suka dinga qaruwa a dakin aka farawa Niima nasihohi iri iri, na haquri da na zama a kind and loving wife to her husband and his family. Karfe biyun rana on the dot motocin gidan ango suka iso dan daukar amaryarsu. Yasmeenah ita tayi jagoran tafiyan, ita kam Begum Sahar tana can gida tana shirye shiryen isowar amarya da Jama'an ta. Sosai hawayen Karimatu suka qaru da taga da gaske rabuwa zata yi da diyarta, daki ta shige ta rufe kanta ta ci kukanta bazata iya jure ganin barin Niima gida ba. Itama Niima kuka take ci dan bayan zuwa University bata taba nisa da iyayenta ba, kuma koh a lokacin ma kusan duk wata sai Ummi ta taho US musamman dan ganinta amma yanzu gidanta zata tafi, gidan auran ta, gidan da zata zauna har abada kuma zata yi zaman ne karkashin wani. Ta san ba lallai a duk lokacin da ta so ganin iyayen ta ta samu hakan ba, babban abunda ya fi daga mata hankali kenan saboda shaquwa ne me tsanani tsakanin wannan rayuka uku wato Niima da iyayenta Abdallah and Karimatu.

Familyn ango sun zo da motocin da suka fi karfin ashirin dan daukar amaryarsu, duk me son bi kawai ya sama mota ya shiga a wuce Al-Haydar Estate da su inda nan za a fara kai amarya ayi budan kai, sannan a daren ranar ayi dinner party inda Begum Sahar ta hada musu kan the following day the newly wedded couple su wuce Turk and Caicos Island for their honeymoon, zasuyi one week can kan su wuce Saudi Arabia suyi two weeks daga nan kuma su qara sati guda a Abu Dhabi kan su dawo gida Nigeria suyi settling in their home to start their new life.

Musamman Niima tayi requesting Khayri da ta shiga mota daya da ita. Dan haka motar da amarya ta shiga daga driver a gaba sai Niima da ke ta shararar kuka a gidan baya da kuma Khayri da ke gefen ta zaune shuru, at a loss of words to say to comfort her. A hankula ta zira hannunta cikin na Niima ta dinga squeezing palm dinta reassuringly. Sosai Niima taji hakan ya kwantar mata da hankali har ta tsayar da hawayen da take ta zubdawa. Juyawa tayi ta kalla Khayri suka hado sukawa juna murmushi ba tare da sunyi magana ba. Niima ta rasa me sa take jin wani irin strong attraction na pulling dinta towards wannan Khayri, ta dade bata taba jin affection for someone haka ba. Zata iya cewa bayan iyayenta da kuma Bakhtiar a yanzu haka babu wanda take matukar kauna a duniya kamar wannan Khayri wanda kwata kwata basu fi kwana biyu ba kacal da sanin juna.

Itama Khayri tunani take me sa take jin kaunar wannan Niiman sosai cikin ranta. Me sa in ta ganta cikin hawaye koh damuwa take jin ba dadi, meyasa take jin wani bittersweet feeling a zuciyar ta a duk lokacin da suka kasance tare. A haka suka zauna shuru kowa na nasa tunanin har suka isa Al-Haydar Estate. Biki sosai ake yi a gidan, koh ina waqa ne irin na native Arabs ke tashi. Tun shigar motar su cikin gidan suka hangi mata tsaye jiran isowar su. Makada da maroqa kam tun shigowar su estate din suke biye da su ana ta koro kirari. Sauka tawagar amarya suka fara daga motocin su amma ita amarya ta na cikin motar da ya dauko ta wanda ya sha tints hannunta riqe gam da na Khayri wadda ta maida mata veil dinta to cover her face well. Laylah Al-Haydar cikin shiga ta alfarma ta dinga qarasowa inda suke tare da Jama'an da ke biye da ita wanda duk mata ne na alfarma, ga makada nata wasa ta tana rawa irin na manyan mata tana watsa kudi. Kusa da Yasmeenah ta fara zuwa suka yi dan rada kan suka yiwa juna dariya Yasmeenah ta riqo hannun surukar tasu suka cigaba da rawa tare. Takawa suke irin na manyan mata wanda Allah ya riga ya basu duniya har suka yi wanda ya ishesu Laylah ta qarasa ta buda motar da Niima ke ciki ta riqo hannunta, aka juya aka nemo wata mace me goyo ta matso ta riqo dayan hannun Niima aka fara raka ta cikin gida (this act is believed in many cultures as a ritual for fertility. Al'adu da yawa sun yarda da cewa in mace me goyo ta riqo hannun a newly wedded bride ta rakata zuwa dakinta hakan zai kawo fertility, amarya bata wani jimawa a sama qaruwa. Something like that😁). Guda kake ji na tashi ta koh ina. Duk yadda gidan su Ni'imatullah Abdallah El-Yaqoob ya  kai ga haduwa wasan yara ne akan wannan haddaden gidan na the Al-Haydars. Komi na cikin gidan screams money and power. Chamber upon chamber aka dinga wucewa da Niima da mutanen ta har aka iso da ita Qasr-Al-Begum inda nan ne personal chamber din Begum Sahar Al-Haydar. Wani daki suka shigo me Arabian setting, ba abunda ke tashi in ba kamshi ba, ga kuma mata nan zaune surrounding a very beautiful lady wadda ta sha ado cikin wani shadda da ya sha aiki na azo a gani, hannu sun sha awarwarayen gold, wuyan ta wani mahaukacin gold necklace ne wanda ya kai abdomen dinta, kunne ma ya sha yan kunne har qafafun ta gold ne, sai walkiya take abunta. Cike da fara'a take ta lale da amarya da tawagar ta. Gab da ita Laylah ta matso da Niima ta zaunar da ita. Itama Laylah samun wuri tayi ta zauna bayan ta riqo right hand din Begum Sahar ta liqa mata kiss. Juyawa Sahar tayi to face the bride ta rangado guda abunta ta fara lale da shigowar ta family dinsu, tana ta kwararo addu'o'i ana Ameen. Ba tare da wani bata lokaci ba wata kawarta tayi wa'azi da nasihohi akan zaman aure kan aka yi budan kai according to culture dinsu. Cika Niima aka yi da kyaututtuka dan a ciki harda mota da expensive jewelry sets da kuma atamfuna just as culture demands. Nan kuma aka sake ruda kawayen amarya da aka basu kyautar two million naira in cash, sauran yan kawo amarya aka bisu da kyautar super wax vlisco kan aka kira masu aiki suka wuce da su dinning hall inda aka tanadar musu kayan ci da sha sannan su huta kan su koma. Itama Niima da kawayen ta can wani chamber haddade aka kai su aka sauke su can.

"Za a kawo abinci very soon, feel very at home". Laylah ta fadi musu kan ta wuce bayan ta bayar da number dinta cewar duk abunda ake buqata a neme ta. In dakunan chamber din bazai ishe kawayen da zasu taya amarya kwana ba za a making musu provision a wani chamber din. Nan da nan yan mata suka saki jiki suna ta kalle kalle ana cewa Niima ba karamin sa'a tayi ba da ta shiga wannan refined and regal family din sai kace wasu royalties. Abinci kala kala aka shiga musu da shi suka ci suka sha suka yi qat kan Laylah ta kira dan ta sanar da su cewar su dan huta dan by 5 on the dot make up and dressing crew zasu zo a fara shirin event din daren ranar. Fadawa bandaki Niima tayi ta yi wanka kan tazo ta nema light dress cikin kayan da aka mata packing wanda zata yi using dinsu a lokacin da kuma wanda zatayi tafia da su suma an mata packing dinsu daban a wani trolley din. Kwanciya tayi shuru tayi ta tunanin halin da Ummin ta ke ciki har barci ya dauketa.

Su Billie da basu da wani nisa da Al-Haydar Estate, gida suka koma dan dama ba suzo da niyyar kwana ba. Abu da yan mata har an saba da sauran kawaye da cousins din amarya. Sallama suka musu suka wuce gida akan cewa a gida zasu shirya zasu hadu a venue din event din kawai. Suma suna zuwa gida hutawa suka shiga yi dan dama make up artist inda Maamah ta daukar musu sai can da yamma zata zo by 6pm dan event din by 8-9pm ake niyyar farawa zuwa midnight. Daki daya dukansu suka baje aka shiga hirar irin mahaukacin arzikin da family din Al-Haydar/Arabs suke da shi har barci yayi awon gaba da su. Ba su suka tashi ba sai to 5 da Mahra ta farka ta tashe su suka yi sallah banda ita da ke fashin sallah. 6 daidai aka kirasu daga qasa cewa make up artist din ta iso, luckily tazo da asst dinta dan haka aikin yayi sauri sosai, kuma dama ba wani heavy make up zasuyi ba. Make up artist na make up, asst dinta na daura musu dankwali har aka gama suka shiga daukar hotuna duk sunyi kyau abunsu, Maamah ta futo da yan matan ta dan dukansu dinkunan su sunyi kyau, ga takalman su da jewelries dinsu na alfarma da ka gansu suma ka ga arziki har Khayri da ta futo daga kauye jikinta ya gogu ta zama kalar hutu da ita (AC ba wasa ba😂). Tun tana jin kunya har ta saki jiki abun ta. Suna gama shiri su ka sauka qasa inda su Ya Ahmad ke jiransu. Qiris ya rage numfashin Khayri ya dauke da taga Ya Kabeer yayi wani dan banzan kyau cikin kayansa farare qal shi da Ya Ahmad duk sun sha all white sai dai Ahmad hular kansa da aikin jikin kayan sa navy blue ne shikuma Kabeer nasa black ne yayi wani shegen haduwa.

Wani ihu Billie ta fasa tana "yes o, I have handsome brothers". Ta matsa kusa da su bayan ta miqawa Mahra wayarta wai ta daukar musu hoto. Kabeer na zaune kamar sarki kan wani armchair yana zuqar cigar dinsa Billie ta matso ta zauna arm din kujerar aka musu hoto, itama Mahra shigowa hoton tayi suka yi ta dauka daga baya Ahmad yace ya Khayri ta tsaya gefe itama ta shigo a daukar musu, sosai suka hadu a pictures din kan aka fara neman fita waje.

Tazo zata wuce Khayri kawai taji an kamo hannunta, ba zatto ba tsammani. Koh da ta juya Kabeer ta gani fuskar nan nasa a hade ba alamun wasa. "Ahmad zo ka mana hoto". Ya fadi. Be sake magana ba hannu kawai ya saka ya jango Khayri kusa da shi tana shaqar musky scent din turaren sa mixed with the sweet smell of his cigar. Wani son sa ke qara fisgar ta.

'koh dai da gaske so na Ya Kabeer yike?'. Tayi nazarin cikin zuciyar ta amma a fili bata ce komi ba sai murmushin da take ta yi for the camera su kam su Mahra da Billie sai tsalle suke suna swooning over the couple.

"Kun gan ku kuwa?". Billie ta fadi "yaran ku ba karamin kyau zasu yi ba. I'm having baby fever already". Juyawa kawai Kabeer yayi ya kalla Khayri suka hada ido ya kashe mata ido daya ya rada mata cikin kunne "kinyi kyau". Kan ya wuce hanyar waje. Shi dai Ahmad mamaki ne ya kamasa saboda massive change inda ya gani in Kabeer. Amma sai dai koh kadan ya kasa buying this new act of Kabeer, ya san dan uwan nasa is up to something kuma duk Zulaikha itace director din wannan sabon drama din.

************

Menene shirin Kabeer? Koh dai da gasken ya fara having change of heart ne?

SANADIWhere stories live. Discover now