Dutsen safe, Katsina.Kabeer jiki na rawa ran jumu'ah bayan sallah ya kama hanyar Dutsen safe. Tun da khayri ta ce masa weekend and Friday was the beginning of the weekend kawai sai yayi deciding ya tafi ya dauko ta.
"Kan na kuma laifi" ya fadi yana tuqi.
Sabida hold up sai bayan la'asar, yamma yayi sosai ma tukun ya isa garin.
"Yau nace ka zo?" Khayri ta tambaya "Wallahi na mance. Ai koh shiri ban yi ba".
"Na shiga uku". Kabeer ya fadi yana dora hannayen sa a kai "Me kike nufi kenan sarauniyar mata?". Sunan da ya kira ta ya kusa sa ta murmushi amma khayri ta danne ta ce masa
"Gaskia ban shirya ba. Duk tunani na gobe zaka zo".
"Yanzu ya kike so nayi? Dan darajar Allah me zan yi?" Ta nuna masa hannu irin oho itama bata san me zai yi ba "Yamma yayi. In koma in dawo kenan nufin ki. Haba baby, ki tausaya mun mana".
Dariya tayi kan tace masa "Ban ce lallai ka je ka dawo ba. Kana iya tafia, ni koh Ya Ahmad ne zan roqa ya zo ya dauke ni. Bazai ce aah ba, koh na hau na hay...". Bata qarasa ba Kabeer ya fara Godforbid!
"Matata, sarauniyar mata bazata hau motar haya ba. Kina dauke da baby na zaki hau motar haya kina hada jiki da gardawa? Haba Allah ma ya sutura". Ya fadi.
"Toh kace kai baza kaje ka dawo ba". Juyawa Kabeer yayi ya studying environment din da kyau kan yace mata "Ana samun wuta da dare?".
"Me yasa kake tambaya?".
"Zan kwana. Gobe sai mu koma tare". Dariya tayi kan tace
"Dan Ingila ya kwana a dutsen safe". Rolling idanu yayi kan yace.
"Ke da baby na kuka kwana bare ni".
"Shikenan" ta fadi "Amma sai dai ka kwana waje". Baki Kabeer ya sake yana kallon ta with his 'Are you serious' look. Bata kula da shi ba ta cigaba "Kan tabarma". Kai kabeer ya fara shafawa yana tunanin yadda zai yi kwanan waje, a kan tabarma. Wani irin kallo ya ma khayri har taji tausayin ta ya dan kama shi.
"Shikenan. Allah ya kaimu goben lafia sai mu tafi".
Daren kwana Kabeer yayi juye juye. Inna da tace ma khayri ta shirya masa extra room din gidan inda sukewa baqi maza masauki sai ce ma Inna tayi ai yace zai fi son ya kwana a waje sabida zafi dan haka Inna ta sa aka futa masa da wata Yar karamar katifa irin ta student da suke da ita, marabar ta da tabarma kadan. Aka masa shimfida aka saka masa net ya kwanta. Ruwa khayri ta ije masa gefen sa da Torchlight tare da maganin sauro na qonawa. Daga window din dakin ta tana kallon shi duk sanda ta farka cikin dare wani lokaci yana juye juye kan yar katifar, wani lokacin yana zaune yana koron sauro duk da net inda yike ciki yana kullum surrounding dinsa warily sai kace wani abun zai zo ya cinye shi koh ya dauke shi. One time da ta farka zuwa futsari ta leqa shi har ya sama barci amma har yayi rolling daga Yar katifar zuwa qasa. Dariya ya ba Khayri gami da tausayi da kuma sabon kaunar sa da take ji cikin zuciyar ta.
Gari da waye Kabeer na ganin irin bathroom din gidan yayi kwaskwarima ya futo. Fasan wankar yayi yace sai ya koma gida tukun. Extra pair of clothes da yike ijewa a motar shi for emergency kawai ya ciro ya sanja ya shirya ya zauna jiran khayri. Sai da ta gama jan jiki ta bata musu lokaci tukun ta futo suka kama hanyar Kano.
Koh da suka shiga garin Kano sabon drama suka fara da khayri taga ya dau hanyar gida da ita. "Ina zaka je da ni?". Ta tambaya ba tare da ya kalle ta ba yace "Gida mana".
"Gidan Maamah zaka kai ni nidai". Sai lokacin Kabeer ya juya ya kalle ta
"Sabida Maamah kike aure koh?" Ya fadi tayi shuru bata ansa shi ba "Nace Maamah kike aure koh!". Tabe baki tayi bata ce komi ba.
![](https://img.wattpad.com/cover/162179064-288-k222121.jpg)
KAMU SEDANG MEMBACA
SANADI
Fiksi UmumThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...