Abuja, Nigeria.
Tun wayewar garin ranar Khayri taji gabanta na wani irin fargaba. Ji take kamar akwai abunda ke shirin faruwa da ita. Sosai zuciyar ta ke wani irin bugu furiously. Koh da ta yi wanka ta shirya bata sauko qasa ba yin breakfast har sai da Mahra ta leqo ta mata magana akan ta sauko suyi breakfast.
"Gani nan zuwa". Ta fadi a hankula ita kam Mahra ta maida qofar ta rufe ta yi saukanta qasa. Waya ta dauka ta danna kiran su Baffah, yana ansawa suka gaisa yaji muryar ta ya san da akwai abu. Tambayar ta yayi koh da wani matsala ne amma tace aah kawai ta tashi ne bata jin dadi. Bayanin yadda take ji ta masa Baffah yace ba wani abu bane kawai tayi ta azkhar. Sosai taji dadin magana da kakanin ta, lokaci daya taji discomfort dinta ya ragu.
Koh da ta sauka Ya Ahmad kawai ta sama a kitchen yana taya chef hada breakfast. Da fara'a ta shiga ta gaida sa shima ya ansa mata da fara'a harda shafa mata kai yana tambayar ta ya gajia da kuma baqunta.
'Shi kam Ya Ahmad akwai saukin kai'. Tayi tunanin cikin zuciyar ta. Taimaka masa tayi suka yi setting table, komi aka yi arranging dinsa yadda ya kamata. Ba da jimawa ba sai ga Mahra da Billie sun sauko aka yi breakfast. Ita dai Khayri wasa tayi ta yi da abinci dan koh kadan bata da appetite, gashi bata ga Ya Kabeer ya futo ya ci abinci ba, ba abun tace zata dauka ta kai masa ba hakan ya jawo mata laifin a wajensa.
"Oya oya muje mu shirya koh, driver na jira already. Gashi munyi late, event inda aka ce by 10 za a fara". Mahra ta fadi. Duka suka miqe aka wuce sama ba a jima ba suka sauko duk sun ci ado sunyi kyau. Duka atamfa suka sa super wanda suka sha dinki na alfarma, musamman Maamah ta sa aka musu dinkunan saboda zuwa bikin nan. Mahra da Billie aka dinka musu skirt, ita kuma Khayri aka dinka mata gown dan sun fi mata kyau saboda yanayin jikinta kuma Maamah ta lura Khayri ta fi son gowns din. Duka silk veils suka sa medium sizes ga expensive jeweleries inda suka sa, sai kamshi ke ta tashi daga jikinsu.
Ya Ahmad har mota ya rakasu, ya ce su kula da kansu sannan ya miqa musu parcel inda Maamah ta basa yace in sunje su ba Hajia Karimatu, Hannunsu hannunta. Khayri da ke zaune a gaban mota ya miqawa saboda ita ce babba a cikinsu. In no time suka isa wani makeken gida da ke Asokoro, a girma gidan zai kai gidansu na Abuja girma sai dai design din gidan is different and more modern than theirs. Sosai gidan ya burge Khayri, amma kuma bata san meyasa the more they got closer to the house take jin wani irin faduwan gaba ba.
Already gidan ya fara cika da mutane ga motoci nan kala kala, duk manya anyi parking dinsu harabar gidan, wasu kuma a waken gidan. Sauka suka yi su ukun su suka fara jerowa, takun su cike da kasaita har suka isa entrance din gidan. Ita dai Khayri gabanta sai fadi yike ta yi. Ma'aikaciyar gidan ce tayi musu maraba da zuwa ta zaunar da su a wani hadadden living room, qato.
"Hajiyar na nan zuwa". Me aikin ta dawo ta fadi musu kan tayi wucewar ta dan cigaba da harkokin da ke gabanta.
"La la su wa zan gani haka". Hajia Karimatu ta shigo fuskar ta dauke sa fara'a. Arms dinta ta bude su Mahra suka miqe suka yi kissing dinta. Khayri kam tunda bata san ta ba Bata miqe ba. "Yaushe rabona da ganinku, duk kun zama yan mata. Kai amma naji dadi". Ummi ta fadi murna bayyane a fuskar ta "Gaskia Hajia Rumaisa'u ta kyauta. Na ji dadi kwarai". Ta riqo hannunsu aka zauna, kujera daya suka zauna da ita aka fara gaisuwa tana tambayar su gida, da karatu da sauransu. Khayri kam ta saki baki tana ta kallon ta, tana mamakin irin kyaun da Allah yawa wannan matar da taji ana cewa Hajia Karimatu, ga ta da fara'a, ga arziki da Allah ya mata dan kana ganin gidan da take zama da yanayin skin dinga kadai ka san akwai hutu da wadata ga wata lace da ta saka me tsananin tsada, jeweleries din jikinta ma da ka gansu kaga arziki.
"Wannan fa?". Ta tambaya moving her attention to Khayri.
"Yar uwar mu ce" Mahra ta ansa Billie kam ta qara da cewa "It's Ya Kabeer zai aura".
CITEȘTI
SANADI
Ficțiune generalăThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...
