Kabeer na barci kiran Dattijo ya tashe sa. Koh da ya farka sai da ya duba time yaga koh takwas na safe be yi ba tukunna ya daga wayar."Ina son ganinka a sama". Kawai Dattijo ya fadi.
Immediately Kabeer ya miqe ya dan kintsa ya futo dan shi a tunanin sa ma duk akan maganar rikicin da ke tsakanin sa da khayri ne. A living room din sama ya sama Adda da Dattijo suna zaune suna breakfast. Qasa ya zauna gefen qafan Dattijo bayan ya gaida su, yayi shuru yana jiran abunda zasu fadi.
"Surukin ka ne ya kira ni yanzu". Dattijo ya tsaya yayi sipping shayin sa kan ya cigaba "Yana da buqatar ganin Khayri dan haka nike so ka dauke ta ku tafi can Dutsen safen".
"Toh" Kabeer ya ce "Amma lafia yike son ganin ta?". Gaban sa ba qaramin fadi yike ba, tunani iri iri na zuwa masa mind. A zatton sa koh khayrin ta kira Baffan ta tayi qarar sa ne ran sa ya baci yike so ta dawo gida. Muryar Dattijo ne ya katse masa tunanin da ya shiga yi.
"Aah toh be fadi mun dalili ba. Ya dai ce a roqan masa kai ka bari taje yana son ganin ta urgently".
"Toh Allah sa kiran na alkhairi ne". Duka suka ansa Kabeer da Aamin.
"Na riga na kira Rumaisa ta sanar da ita ta shirya kaima sai ka shirya ka je ku tafi kada ayi tafiyar yamma".
Kabeer be wani bata lokaci ba ya yi wanka ya shirya tsaf, ya sa wata navy blue kaftan da suka masa kyau sosai. Sauri sauri ya dinga yi koh breakfast be tsaya yi ba dan koh ba komi ranar zai ga Khayri, Maamah bata da yadda zata yi sai dai tayi haquri. Less than an hour da maganar su da Dattijo har ya isa gidan Maamah. Da sallaman shi ya shiga ya jiyo muryar Maamah a kitchen ya bi ta har can.
Ta baya ya rungumo ta yana fadin "Good morning my sweetest Maamah".
"Wai duk dan na dawo maka da mata ka ke neman kalallame ni Kabeer" Maamah ta fadi tana juyowa "Toh baka isa ba!". Juyawa tayi ta cigaba da tuyan da take yi.
"Ni dai na shiga uku. Maamah kiyi haquri".
"Ai baka riga ka shiga uku ba yaro". Maamah ta fadi. Shikam kabeer ya san yana ruwa tsundum dan Maamah na da haquri amma fa in ka tabo ta sai ka ji jiki ka wahala kan ta saurare ka, gata da taurin kan gaske.
"Ke Billie zo ki dauki abinci ki hau ma khayri sama da shi". Billie bata miqe ba Kabeer yayi saurin isa wurin kayan abinci yana fadin
"Zan kai mata".
Buge hannunsa Maamah tayi tana fadin "Ba kai nace ba Malam". Koh kula ta be yi ba yayi saurin daukan tray din ya fice daga kitchen din. Yar murmushi Maamah tayi a zuci tana fadin
'Sai ka ji jiki yaro'.
Khayri ta gama sa riga kenan ta zauna tana tazan dogon gashin ta sai ga shigowar Kabeer riqe da tray. Tun kan ta daga kai su hada idanu ta san shi ne ya shiga sabida kamshin turaren sa da ya mamaye hancin ta da kaf dakin. Kan nightstand ya ije tray din ya matsa kusa da ita akan gado ya zauna. Yana zama khayri ta matsa gefe, creating space between them. Kabeer ne ya fara mata magana "Kin tashi lafia?" Ta ansa shi da lafia lau. "Ya karfin jikin".
"Alhamdulillah da sauki". Daga nan duka suka yi shuru har sai da yace mata ga breakfast nan Maamah tace ya kawo mata. A hankula ta dinga yin breakfast dinta har sai da ta qoshi tukun ta jawo tray din drugs dinta ta sha all the while Kabeer na zaune in ba kallon ta ba ba abunda yike yi. Daga ya kalla fuskar sa sai ya kalla cikin ta which had his child in it. Wannan tunanin ba qaramin dadi yike ma Kabeer ba, the thought of him becoming a father.
Qara matsawa yayi kusa da ita yana janyo ta zuwa jikin ta yana fadin "Khayri na. I've missed you".
"Ka sake ni". Ta fadi "Dan Allah". Fuskar ta a yatsine tayi maganar hakan ya masa ba dadi ganin gaba daya yanzu khayri bata so koh da kusa da ita ya zo. In ta gansa kamar bata jin dadi.
YOU ARE READING
SANADI
General FictionThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...