Babi Na Goma Sha Hudu (14).

1.2K 151 13
                                    


Kindly say a prayer for me as you read this chapter. Thank you 😊

Kano, Nigeria.

.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
.

A sauri saurin ta na saukowa qasa ta kusa cin karo da Ahmad wanda ke haurowa sama. Maamah dama tun da Dattijo ya buqaci zantawa da yaran one on one tayi kiran sa da yazo.

"Khayri, ina zaki da saurin nan haka" ya mata magana.

"Ya Ahmad ina kwana"

"Ina kwana, Ina Maamah?". Ya tambaya ita kuma ta daga masa hannu sama dan sai faman sauke numfashi take ta yi. Dariya yayi kan ya dan shafa mata kai ya wuce. A dakin Kabeer ya same su suna magana da shi. Hakan ya sa kawai ya gaida su ya juya zai wuce.

"Ahmadu na, ka sama Dattijo in his room". Adda Manga ta fadi shikuma ya ansa da toh kan ya wuce. Koh da ya sauka kai tsaye hanyar dakin Dattijo yayi, daidai yana shan kwanar dakin Mahra ta fito daga dakin. Jingina bayanta tayi da wall din dakin, idanunta a runtse ta dora hannunta daya kan kirjin ta kan ta sauke ijiyar zuci. Ahmad na kallo hawaye suke fara zirya kan kumatun ta. Idanunta a rufe bata ma san yana kallon ta ba. Shikam Ahmad zuciyar sa ta gama karaya ganin yar uwar sa wadda yike so tamkar yadda yike son kanwar sa da suke uwa daya uba daya cikin wannan hali. Sanin cewa a dalilin sa take cikin wannan halin ya sa shi matukar damuwa. Bata ankara ba kawai taji muryarsa cikin kunnenta.

"Was it that hard?" Ya tambaya kan ya sa manyan yatsun sa biyu ya share hawayen da ke saukowa a hankula. A hankula ta buda manyan idanunta ta same sa ya qure ta da idanunsa. Kamar dama jira yike ta bude nata idanun. "Your tears are too expensive habibty. Ki daina kuka, I never want to be the reason for your tears kin ji koh". Ya fadi kan ya dan shafa mata kumatu ya wuce.

Freezing Mahra tayi a wajen idanunta akan retreating figure dinsa. Tana kallo ya buda dakin Dattijo ya shigo ta kuma ji qaran lock din dakin sanda yayi clicking. 'I wonder what his response to Dattijo's questions will be' tayi tunani a zuciyar ta kan mind dinta ya sake komawa ga ansar da ta ba Dattijo. Tana gama nazarin ta ta wuce sama. Direct dakin Khayri ta shiga. Samun ta tayi kwance a kife tana kuka. Da sauri ta matso kusa da ita ta zauna tana tambayar ta abunda ya sa take zubar da hawaye. Koh da Khayri ta dago ta kalli Mahra sai qara fashewa da kuka tayi tana tunanin wannan baqon lamarin da zuciyar ta ke kokarin welcoming.

"Ki fadi mun me ya faru Khayri" kasa cewa komi tayi kawai ta fara share hawayenta a hankula. Taya ma zata fara fadi mata tsananin tausayin Ya Kabeer da take yi ne ke saka ta wannan kukan, taya zata fadi mata cewa dolen da Dattijo ke kokarin yiwa Ya Kabeer ke sa ta kunci, taya zata mata bayanin wannan baqon lamarin da take ji a zuciyar game da Ya Kabeer. Taya ma zata fara fadi mata yadda yanzu farin cikin Ya Kabeer ya zama nata, haka ma baqin cikin sa. Taya zata iya fara mata bayanin son Ya Kabeer da ya riga ya ci karfin zuciyar ta. Ita kanta ta rasa ya aka yi haka ya faru. Shi dai Ya Kabeer dinnan ba shiri suke ba, hasalima duk duniya tana ganin bayi da wadda Kamar ta, ita kuma ba wanda take tsoro irinsa dan koh ganin sa tayi ji take Kamar numfashinta zai tsaya amma kuma sai gashi Allah ya jarabci zuciyar ta da son sa. Allah ya jarabci zuciyar ta da son wanda be ma san tana yi ba, mutumin da ya tsane ta, koh kan inuwar sa baya kaunar ganinta.

"Kewar gida nike" kawai ta fadi ma Mahra kan ta miqe ta wuce bandaki dan ma Kar Mahra ta cika ta da tambayoyi. Mahra dai ba wai ta wani gamsu da ansa inda Khayri ta bata bane amma haka nan ta rabu da ita. Samun kanta tayi da tuna nata damuwar hakan ya sa ta miqe ta wuce dakinta.

Shikam Ahmad koh da ya shiga samun wuri yayi ya zauna. Bayan sun gama gaisawa da Dattijo sai da yayi zaman jiransa for like 15 minutes ya gama making call da wani abokin business dinsa kan ya maido attention dinsa kan jikan nasa.

SANADIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora