Kano, Nigeria.
Dawowan su daga Abuja da kwana hudu su Kabeer suka fara shirin zuwa katsina state. Ran Alhamis bayan ya dawo gida da yamma after playing Polo with Ahmad da abokansu, yana shiga gida ya wuce daki yayi wanka ya sakko qasa cikin sabon shirin sa tsaf da shi. Mahra ya sama tare da Adda Manga zaune suna hirar su abunsu.
"Ke" ya kira Mahra a dake "Ina take?". Ya tambaya. Tun kan Mahra ta ansa Adda tayi magana.
"Ita wa fa?".
"Wancan yarinyar?". Ya ansa.
"Ke Mahra waca yarinya gare mu gidanga?". Da hannu Mahra tayi alama cewar itama bata sani. Abun be ba Kabeer dariya ba.
"Khayri nike nufi". Ya fadi da yaga dai they wouldn't let him be.
"Yawwa yanzu na ji zance. Amma ka zo kana ta mana wani gulma, kace kana son zantawa da sahibar ka". Adda ta kalla Mahra ta kashe mata ido suka kwashe da dariya. Kabeer be bi ta kansu ba yace Mahra dan Allah ina take ita kuma ta fadi masa cewar tana sama.
"Ke Mahra je ki sauko masa da masoyiya kan ya cinye mu". Adda Manga ta fadi tana yar dariya. Ba musu Mahra ta miqe tayi hanyar sama domin kiran Khayri.
Khayri na kwance shuru tana cikin nazarin ta, tana tunanin Ya Kabeer da kuma irin rayuwar da zasuyi bayan aure kawai taji sallamar Mahra wadda ta shigo dan ta fadi mata cewar Ya Kabeer na qasa yina jiranta. Mamaki sosai ya kama Khayri dan abu ne da ba a taba ba wai ace Ya Kabeer yina neman ta, ji tayi lokaci daya zuciyar ta ta fara wani irin furious bugu saboda tsananin tension da ta shiga. Toh ita yanzu me zata je tayi masa? Me zai gaya mata?
'koh dai ya fasa auran ne?' tayi nazarin a zuci.
A hankula ta sauko daga kan gado ta zura hijaab dinta dogo. Mahra na gani ta fara qorafi.
"Khayri, me zan gani haka? Zaki gun saurayi ne zaki zura hijaab qato? Kuma a cikin gida. Aah wallahi, ai gaskiyar Billie ne wallahi sai mun zaunar da ke mun miki lectures in ba haka ba haka zaki tafi London ki ta kunyata mu". Mahra ta fadi hannunta daya kan qugu "Yanzu dai kiyi haquri ki cire hijaab dinnan, Ya Kabeer ne fa, kuma cikin gida". Turo baki khayri tayi ta fara complain cewar ita gaskia bazata iya zuwa ba lullubi ba.
"Sabon al'amari" Mahra ta fadi kan tace mata toh ta nemo veil ne ta saka instead of hijaab. Hakan aka yi, wata medium sized kashkha da Adda Manga ta siya mata ta dauko Mahra ta fisge shi ta feshe shi da turare kan ta miqa mata. "Ji ki Khayri fuska koh kwalli babu, sai kace me takaba haka za a tafin ma Ya Kabeer". Ita dai Khayri koh a jikinta, share Mahra tayi dan ita ba wannan bane matsalar ta. Ita kam Mahra har suka sauka qorafi take tana fadin kiran Billie zatayi tazo su gyara Khayri kan ta tafi da kunyar ta da kauyancin ta London ta dinga basu kunya.
Koh da suka sauko basu same sa inda Mahra ta bar sa ba, Adda Manga kawai suka sama tana waya sai fulfulde take ta faman bugawa a waya. Da hannu ta nuna musu hanyar waje hakan ya sa suka gane yina waje, har bakin qofa Mahra ta raka Khayri kan ta juyo. Da sauri Khayri ta kamo hannunta.
"Dan Allah kizo muje tare. Dan Allah Mahra".
"Ni Khayri! Ni kike so Ya Kabeer ya yarfa. Haba sai kace baki san halin mijin naki ba". Hararta Khayri tayi tana fadin ita ba mijin ta bane.
"Toh kwana nawa ya rage? Just 26 days koh kin mance ne". Yadda ta ga Khayri ta dage tana ta bata haquri ya sa ta dariya "Kije sai kin dawo, da can da kike shigewa dakinsa kuke soyayyar wa ke raka ki".
"Haba Mahra" Khayri kamar ta saki kuka "Toh in naje me zan ce masa?". Ta tambaya Mahra hakan yasa dariyar Mahra ya qaru.
"Da ni ke tsara miki abunda zaki ce masa? Khayri je sai kin dawo". Ta fadi tana dan tura ta. Left with no option, haka nan Khayri ta fara taku a hankula har zuwa gazebo inda Ya Kabeer ke zaune da karan sigari a hannunsa.
ESTÁS LEYENDO
SANADI
Ficción GeneralThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...