Kabeer & Khayri?
Or
Kabeer & Zulaikha?
Which team do you belong to?..
*****************
.Kano, Nigeria.
"No! I won't be a part of this. Can you just yourself". Ahmad ya fadi yana miqewa ran sa a bace. Da sauri Kabeer ya kamo hannunsa yana kokarin hanasa tafia.
"Haba bro". Kabeer ya fadi. Itama Zulaikha marairaicewa tayi tana kallon Ahmad duk dan ya saurare su ya bada hadin kai.
"God Zulaikha, how absurd. Ya zaki kawo wannan shawaran, wannan ma ai ba mafita bane. How you destroy someone else's life for your own selfish reasons. Haba ita ba ku tunanin ta? She's still a kid literally, she has dreams, hopes, expectations and you'd be crushing them in kuka ida nufin ku akan ta. I won't be a part to this gaskia". Ahmad na gama magana ya juya yayi hanyar waje. Kabeer ya ruga a guje ya bi sa yana kiran sunansa amma koh juyawa Ahmad be yi ba bare ya tanka sa har sai da ya isa motar sa.
"Ahmad why're you taking this personal?" Kabeer ya tambaya. Juyowa Ahmad yayi ya kallesa kan ya basa ansa "Be honest with me Kabeer, da zan kawo maka irin shawaran nan in gaya maka zanyi ma Mahra haka zaka yarda?".
"Leave my sister out of this" Kabeer ya fadi ran sa a bace.
"I expected that" Ahmad yayi murmushi kan ya juya zai buda motarsa sai ji yayi Kabeer ya ce "fucking bastard". Runtse idanun sa yayi zuciyar sa na wani irin tafarfasa dan a rayuwa be taba jin bacin rai irin na wannan ranar ba, be taba jin Kabeer ya bata masa rai kamar wannan lokacin ba. Don yace bazai supporting haukar su ba shine Kabeer zai kira sa da bastard. Ahmad na juya ya kai ma Kabeer naushi da shegen karfi kan hancin sa. Abun ka da me farin fata nan da nan jini ya fara zubowa. Be gama farfadowa daga naushin ba Ahmad ya kai masa wani a ciki kan ya juya ya koma ga motar sa amma sai ji yayi Kabeer ya cafko masa riga ta baya haka fada ya kacame tsakanin Ahmad da Kabeer. Yan uwan da ke son junan su kamar me, Ahmad da ya dauke Kabeer tamkar uwa daya uba daya suke dan closeness dinsa da Kabeer koh rabin nasa na dan uwansa wanda suke iyaye daya be kai ba kuma koh da suke yara ba su taba dambe ba amma sai ga su yau da girman su, a parking lot din 'The Noble club for Elites' suna fada kamar 'ya'yan karnuka. Cikin dan qanqanin lokaci sunyi drawing attention na mutane an taru daga masu kallo, sai masu video sai masu kokarin raba su.
Zulaikha kam tana can ciki tana jiran dawowan su bata ma san abunda ke faruwa ba. Wani da ya san ta da su ne ya shigo ya ganta zaune yike fadi mata.
"Zulaikha Al-Fayeed?". Juyowa tayi ta kalla Bilaal Makama, yaron wani tsohon minister kuma abokin yayanta Ilyaas. Murmushi ta masa ta gaida shi. A gurguje ya ansa mata kan ya fadi mata abunda ke faruwa.
"Aren't they your friends? Kabeer Dikko and his brother" ya tambaya ta daga masa kai alaman eh. "Well they're out there fighting like dogs". Zulaikha bata tsaya sauraron wani bayani nasa ba kuma ta dau bag nata da shades tayi waje. Isowar ta yayi daidai da sanda securities suka raba su day kyar. Ahmad ya fasawa Kabeer hanci shikuma Kabeer ya fasa ma Ahmad baki. Shirts dinsu duk a bace with blood and dirt. Kallon su kawai ta harare su duka.
"I'm disappointed in you both, really. Bloody arseholes!". Tana fadi ta wuce hanyar motar ta buda ta shige ta ja da gudun gaske ta bar club din tayi hanyar gida. Suma kowannen su motar sa ya shiga. Ahmad ne ya fara driving off yayi hanyar gidansu da ke Bompai a garin Kano Kan Shima kabeer ya kunna motarsa yayi hanyar gida, can Nasarrawa G.R.A. koh da ya isa gida be shiga immediately ba sai ya kunna sigari ya zuqe a garden kan ya shiga cikin gida rai a bace.
Adda Manga na zaune tare da Mahra da kuma Khayri wadda taqi fitowa har sai da Adda ta bi ta sama dakinta ta fito da ita. Hirar su suke, Adda Manga na ta ba su labarin lokacin haduwar ta da Dattijo suna ta cin dariya kawai suka ji shigowar Kabeer. Basu ji sallama ba sai door da sukaji an yi slamming wanda duka sai da suka firgita. Yazo zai wuce foyer din zuwa hanyar sama Adda Manga ta hango sa ta qofar da zai sada ka da living room.
CZYTASZ
SANADI
General FictionThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...