Babi Na Goma Sha Bakwai (17).

1K 146 2
                                    

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Kano, Nigeria.

A guje ta bi ta kamosa dan gaba daya ba cikin hayyacin sa yike ba, ya miqe ya nufa hanyar qasa. A corridor din hanyar dakinsa ya zube qasa ya fara kuka me qara wanda hakan har yasa Khayri taji zuciyar ta ta karaya. Ba karya ita Ya Kabeer tausayi yike bata, duk fadan da zai mata da tsana da yike nuna mata duk sun daina damunta dan taga yadda yike yi cikin yan uwansa, ta san mutum ne shi mai sanyi amma with a temper as fiery as a fire ball. Zamewa tayi qasa gefensa ta zauna shuru nata hawayen na zuba, ta rasa me ke sata kuka. Kwanciya Kabeer yayi ya dora kansa kan cinyar ta sannan ya kamo hannun da ta sa tana share masa hawaye.

"My Zulaikha" ya kira sunan a hankula. Dan runtse idanu Khayri tayi saboda wani irin zafi da ta ji kirjin ta na mata lokaci daya.

"Dan Allah karki bari na aura Billie. Only you can save me. I can't imagine a life without you, ina son ki wallahi". Kan kunnen Dattijo Kabeer ya fadi wannan kalaman nasa da be ma san ya fadi ba.

"Nima ina son ka Ya Kabeer" gaba daya a wannan lokacin Khayri bata san what took over her ba har ta iya bayyana sirrin da take ta faman boyewa a zuciyar ta "Son da nike maka na neman haukata ni Yaya" ta sake fadi hawayen ta na qaruwa.

"Toh ki aure ni". Dan gasp inda Mahra tayi ne ya sa Khayri dago kai. Koh sanda ta daga kanta, idanunta basu fada kan na kowa ba sai na Dattijo hakan ya sa kunya ya rufe ta miqe a guje ta ruga zuwa dakinta. Rufe kofar tayi ta ciki ta zube kan gado, zuciyar ta sai faman bugu yike ta yi.

Dattijo kam rai a bace yayiwa Mahra umarni da ta wuce ta kwanta. Wucewa tayi zata daga Kabeer ya daka mata tsawa "cewa nayi ki wuce! Barshi a wajen" a firgice ta saki hanunsa da ta riqe ta wuce.

"Mutumin banza kawai" Dattijo ya fadi kan ya wuce shima rai a bace, koh kallo na biyu beyi wa Kabeer ba ya barshi a wajen ya wuce.

A ranar da kwana biyun da Dattijo ya bawa Kabeer suka cika, tun safe ya fita be kuma dawo ba har sai can da yamma. Malam Mansur yayi matukar murna da ganin abokin nasa sai dai kuma labarin da yazo masa da shi da ya matukar basa mamaki, ya kuma jefa zuciyar sa cikin rudani.

Sanda Dattijo ya miqe zai tafi, har waje inda driver yayi parking Malam Mansur ya rako Dattijo suna qara tattaunawa akan maganar da ya kawo Dattijo dutsen safe. Sake assuring Malam Mansur yike cewa komi zai daidata kuma bazai taba dana sanin decision inda su biyun suka dauka ba a wannan ranar.

"Sai kaji daga gareni" Dattijo ya fadi bayan ya shiga gidan baya ya zauna. Sallama sukayi driver ya ja mota. Basu sake tsayawa koh ina ba sai garin Kano. Fitar da yayi ba wanda ya fadiwa inda zashi haka kuma da ya dawo, dakinsa kawai ya wuce ya watsa ruwa ba tare da ya ci abinci ba dan dama ya cika cikinsa da dambu me dadi a can garin dutsen safe. Tea kawai ya buqaci a kawo masa sannan a barshi ya huta.

A hanyar dawowa masjid bayan sallar asubah kashe gari ya riske Kabeer. Da saurin sa ya taho kusa da jikan nasa suka jero tare. Bayan gaisuwa ba abunda Kabeer ya sake cewa Dattijo dan dama shi ransa gaba daya kwanakin nan a dagule yike. Ga auran da Dattijo ya nace sai yayi, gashi haushin taurin kan Zulaikha wadda ta tsaya akan words dinta na cewa ita bata shirya aure ba a wannan lokacin. Gaba daya ya rasa mafita cikin al'amarin.

"Jiya ban ji daga gare ka ba, koh ka mance yarjejeniyar mu ne?" Dattijo ya fadi, breaking the thick silence between them. Shuru Kabeer yayi dan bayi da excuse inda zai bada. "It's okay, qila nauyin yi mun magana kake" Dattijo ya fadi yana masa murmushi.

"Kana da wadda kake so koh?" Kai Kabeer ya gyada, curious to know where the convo was heading "Madallah, nayiwa magabatan ta magana kuma sun amince da kai" cak Kabeer ya tsaya maganar da Dattijo ya fadi na masa yawo a kai. Yayi magana da magabatan Zulaikha? Yaushe toh? Kuma ya aka yi ya san cewa ita yike so?. Yana cikin wannan tunanin yaji Dattijo ya riqo sa "Ya ka tsaya, muje mana" ya fadi kan suka cigaba da tafia.

SANADITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang