I thought zan iya gama labarin in 50 chapters but here we are 60 chapters and counting😂 kuma ina ganin dole in rage tsawon labarin, last week I made a last minute decision to make major changes to the plot sabida in gama da wuri. SANADI was initially written in English before I converted it into Hausa kuma labari ne me so many angles, has romance, mystery, abuse blah blah and so many major characters so labari ne me tsawo amma dai dole I had to change the beautiful plot I had in mind😪 ba dan na so ba sai dan ban so na rubuta takarda me 100 or so chapters 😂🤣 so hopefully we'll finish at chapter 70 kuma kan 2022 da yardan Allah 😁 Allah sa na iya🤣😂After jirwaye I didn't think zan iya rubuta wani book in hausa but I fell in love with hausa writing even tho I'm not perfect at it. So now I'm still wondering if I should write another book in hausa after SANADI🤔 Ya kuka gani? Should I write another hausa book koh in koma rubutun turanci na?😂
Anyways I hope you enjoy this unedited chapter! 😁
********************
London, England.
Zuwa 12 noon suka futa. Wurare daban daban sukaje Ya Kabeer yayi ta nuna mata gari. Duk inda suka zo wucewa zai fada ma sunan wurin da kuma irin activities inda went on in that particular place. Kan su je gida ya kai su wani restaurant babba hadadde suka ci abinci, a nan ne ya miqa ma waiter inda yayi serving dinsu abincin su wayar sa ya daukan musu hotuna dan dama dalilin da ya sa ya futa da ita kenan sabida Maamah tana ta matsa masa akan maganar hotuna.
Sanda suka dau hanyar gida dare ya riga yayi dan kan su isa ma har barci ya fara dauke Khayri a cikin mota. Da suka isa gida suka shiga cikin godia khayri tayi masa for the wonderful day ya ansa ta fuska babu yabo ba fallasa. Tare suka shiga master bedroom Kabeer ya wuce closet da bathroom ya kwashi kayan sa da toiletries inda tayi moving sabida zuwan su mommy ya yi wucewar sa sama. Khayri kam da kyar ta iya yin wanka tayi nafila dan dama tun a hanyar suka gabatar da salloli. Tana iddawa ta kwanta sai barci.
Tun ranar khayri bata qara ganin Kabeer ba sai da suka yi kwanaki goma sha daya daidai. Zuwa lokacin khayri ta riga ta saba and she wasn't doing to turn the situation around kawai ta dorawa sarautar Allah ido ne ta kuma maida hankali sosai akan karatun ta. Ranar da suka hadu finally khayri tayi na annabawa ta futo daga daki ta same shi a inda yike zaune a living room tace masa alfarma take nema daga gare sa.
"Ina jin ki" yace mata ba tare da ya dago ya kalle ta ba. Cikin nutsuwa khayri ta fara gabatar masa da case dinta cewar dama so take ta roqe sa in ba matsala da yamma zata dan dinga futa shan iska around the block sabida ta gaji da zama cikin gida kullum. "Toh shine sai kin tambaye ni. Kiyi duk yadda kike so, I don't give a flying fuck what you do with your time". Ya fadi dismissing her. Khayri bata ji dadin manner inda yayi addressing dinta ba amma ta kasa ce masa komi kawai ta miqe ta tafi. The next day sai gashi ya dawo da yamma ya kirata, credit card ya miqa mata tare da fadin mata cewa in Mrs Lee tazo the next day zata je da ita ta nuna mata how to use shikuma zai dinga sa mata kudi koh da tana da wata buqata. Karba tayi ta masa godia ta wuce.
Tun daga lokacin da yace mata tana iya yin duk yadda ranta ya so khayri ta dan fara futa zagaye unguwar su har gradually ta fara gane wurare close to them ta kuma fara sabawa da maqotan su. Akwai dan park kusa da su da take jin dadin zuwa da yamma ta zauna tayi ta kallon yara suna wasa da kuma mutane kowa na harkar gabansa. Haka rayuwa ta cigaba da kasance ma khayri, kullum daga karatun ta sai dan strolls inda take yi. Yan hausawan da suke zama kusa da su da ta dan saba da su suka qulla zumunci da ita har jefi jefi suna zuwa ma juna ziyara. Mrs Lee kuma tana kokarin itama debe ma khayri kewa sai Asmaa wadda always suna magana ta waya wasu lokutan kuma ta kan dan zo dukda inda su suke da zama da nisa da su khayrin. Haka suka kwashi wata shidda khayri na zama da mijin da sai jefi jefi take ganin sa, in kuma yana nan ba ruwansa da ita sai abunda ya zama dole. Lura tayi cewar kamar tun around lokacin da su mommy suka fara zuwan musu ziyara Kabeer ya qara bada himma akan ignoring dinta, baya cika son abunda zai hada su duk da ya rage yawan zagi da ihu da yike mata kawai sabgar ta ne kwata kwata be cika shiga ba.
VOCÊ ESTÁ LENDO
SANADI
Ficção GeralThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...