Abuja, Nigeria.
Dogon numfashi ta ja, tayi ijiyar zuci kan ta sauka daga motar ta ta shiga cikin gidan. She didn't need to knock on the door, Niima just went in. Downstairs din was eerily quiet. The whole house felt lifeless as if it could feel the sadness sipping right out of the people who lived in the house. Da ta kai living room din sama bata sama Ummin ta a nan ba tana kallon tv, wayar ta a hannu tana dannawa kamar yadda ta saba kawai ta wuce straight bedroom dinsu. A bude ta sama qofar and Karimatu sat on the bed, her back to the door. Akwati ne a bude kan gadon da alaman hada kaya take yi ta tsaya ta zauna. Gefen ta kuma hotuna ne baje kan gadon and Niima didn't need to be told whose photos were splayed out on the bed. Ba tare da tace komi ba ta matsa gefen Ummin ta.
Karimatu bata ankara ba taji an zauna gefen ta har an dora kai saman shoulder dinta. Dan gasping tayi tana fadin "Ni'imatul..." Bata qarasa ba ta tsaya midway unsure of what name to call her.
"It's me Ummi" Niima ta fadi tana kwantar da kan ta kan cinyar Ummin ta tana fadin "I'm home. Your Niima is home". Hawaye Karimatu ta fara zubarwa suna faduwa kan fuskar Niima da ke kwance jikin ta.
"Niima. My Niima". Miqewa zaune tayi suka runguma juna Niima tana fadin "I'm so sorry Ummi. I was ungrateful. Dan Allah ki yafe ni, na muku butulci. I got blinded by rage na mance duka alkhairin ku a gare ni". Kankame ta sosai Karimatu tayi a jikinta tana jin kamar yanzu rayuwar ta ta dawo gare ta, a yan kwanakin she was just living like a lifeless corpse, life had no meaning for her but now all the spice and colour in her life was back; her Niima was back.
"Bani da uwar da ta wuce ki. Bani kuma uban da ya wuce Abba. Dan Allah kuyi haquri".
"Ya na ga kamar kin rame? Baki cin abinci koh" Ummi ta fadi tana jan ta "Muje, I'll cook for you".
.
******************
Kano, Nigeria.
A ranar da Bakhtiar tare da mutanen sa suka zo ganin Alhaji Sadiq Yakasai, basu bar garin kano ba sai da suka bada sadaki, kudin gaisuwa har ma da lefen Billie aka tsaida aure in a week time za a hada tare da na su Ahmad ayi. Komawa Abuja suka yi suka fara shirye shiryen su, suma nan gidan suka cigaba da nasu.
A ranar Maamah ta sama Uncle Sadiq bayan Adda Manga ta mata fadan da tayi ta kuma buda idanu har tayi realizing mistakes dinta, Maamah ta sama Uncle Sadiq ta basa haquri ta kuma sanar da su duka cewar ta amince da Sudais, she was 100% in support of the marriage. Hakan ya ma kowa dadi.
Shikam Kabeer dama sai da suka yi kwana uku daga shi har khayri basu saka su a ido ba dan honeymoon sabuwa suka yi. Duka wayoyin su a kashe suna spending time tare, making up for all the months they stayed apart.
A kwana a tashi ba wuya aka cika one week. Rana ya zo aka daura auran Ahmad Sadiq Yakasai tare da amaryar da Mahra Muhammad Dikko da kuma auran Sudais Abdul-Gaffar Arab tare da tasa amaryar Bilkisu Sadiq Yakasai. Biki ne gagarumi Maamah ta hada duk wani da ta hulda da shi Maamah ta gayyata har ma mutanen da basu sani ba, whoever wanted to attend the wedding was welcome to.
Dinner inda Maamah ta hada kam a garin Kano an dade ba a yi taron da aka kashe kudi ba irin wannan. Masu kudi kawayen Maamah, matan mazan da suka ansa sunan su masu kudi duk sun zo wannan taro. Naira ce kawai ke gogar naira, dollar na gogar dollar. Artistes kam iri iri an gayyace su da na Hausa da na turanci duk dan su zo su qayata bikin. An ci an sha, masu tafia da item 7 gida sun tafi da shi.
Amma cikin duk wannan festivities da aka yi gaba daya Zulaikha Al-Fayeed wata abun tausayi ta zama ganin yadda Kabeer ke ta ririta matar sa. Ita koh kallo bata ishe sa ba, kamar be san da irin ta ba a duniya. Da ta kasa riqe takaicin ta ranar dinner barin event din tayi koh tashi ba a yi ba. Dama tun da ta ga yadda khayri ta futo shigar ta ta alfarma, ta hadu, tayi kyau, ta caza kwakwalar Zulaikha dan koh kadan bata yi kama da khayrin da shekaru uku da suka wuce aka kawo daga kauyen Dutsen safe ba, wannan khayrin goggiya ce, ta hadu kamar wani irin qusa ne uban ta. Sai ranar Zulaikha ta qara tabbatar da shakka babu Allah yayi halitta a wurin, khayri ta hadu ta koh ina bare kuma da yar uwar ta Niima Abdallah El-Yaqoob take ta qoqarin pimping dinta ta zama Yar gayu sosai.
ESTÁS LEYENDO
SANADI
Ficción GeneralThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...
