Any reader from Abuja? This chapter for you guys. I hope you enjoy it. (NB- unedited chapter).*****************
Kano, Nigeria.
"Are you girls sure you packed everything?" Maamah ta tambaya, masu aiki na shigar da boxes bayan wani bakin Ford edge. Duka su uku suka ansa mata da eh. "Toothbrush? Pyjamas? Everything?".
"Yes Maamah, komi mun dauka". Suka ansa ta all so eager to leave. One by one ta bi tayi kissing foreheads dinsu tace su kula da kansu and they should their mini holiday.
"Na sa an gyara muku gidan. Have fun". Ta fadi kan ta wuce zuwa waken dayan motan da ake shigar da kayan Kabeer da Ahmad suma ta tambaya koh sun dau komi da komi. Hugging dinsu tayi tana fadi masu su kula mata da yan matan ta kuma a gaida mata Hajia Karimatu. Ba tare da Bata lokaci ba suka shiga mota. Da Mahra da Khayri suka shige baya, ita kuma Billie ta zauna a passenger seat din motar da aka saka boxes dinsu, sai Ya Ahmad kuma da Ya Kabeer suna dayan motar, duk sun shiga gidan baya. Motar su ta fara daga kan motar da ke da yan matan ya bi baya. Maamah bata koma cikin gida ba sai da ta ga ficewan su. Shuru motar yayi dan dukansu da tunanin da suke yi, Billie kuwa earpiece ta saka kunnen ta tana sauraron waqa. Ita kuma Mahra tunowa take ta yi da wayar da suka yi da Ya Ahmad the previous night, it was the first time he was calling her as someone other than her older brother. Sun dade suna magana, kuma sosai suka sha hira wanda da physical meeting ne basa iya magana haka. Da ta tuno wasu abun sai ta saki yar murmushi, zuciyar ta na mata wani irin dadi. Ita kam Khayri ta zauna shuru tayi resting kanta on the headrest, idanunta a rufe sai tunani iri iri take ta yi amma overall tsoron shiga jirgi take dan dama bata taba shiga ba, karon farko kenan da zata shiga. Kwata kwata bata tunanin zuwan ta Abuja idea ne me kyau saboda tunda aka ce za a je da ita gabanta ke wani irin faduwa, bata san me yasa ba take tsoron zuwa, sai dai akwai wani part of her that really wants to go.
Motar su Ahmad ma haka tsit ba me cewa komi. Shima Ahmad tunanin Mahra ne ya cika masa zuciya, these days bayi da wani aiki da ya wuce na tunanin ta. Shikam Kabeer waya suka dan yi da Zulaikha kan ya kunna dan karamin TV inda ke gabansa, the one attached to headrest din passenger seat. Koh da ya duba CD plate inda ke ciki cartoon ya gani, driver ya masa bayani cewar last su Zayd da Zayn aka kai birthday party a motar that's why.
"It's okay, I don't mind". Kabeer ya fadi dan dama shi masoyi cartoons ne. Kallo ya fara yana cin dariya abun sa.
In no time suka isa Aminu Kano international airport, about an hour early. Samun waje suka yi suka zauna to kill time kan finally aka yi announcing flight dinsu is ready to board. Kwata kwata cikin minti arba'in sun isa Abuja. Motoci biyu da drivers na Argon corporation suna jiransu already. Kamar yadda suka taho airport a Kano, haka aka yi mata suka yi sharing mota daya suma mazan suka yi sharing daya. Suna shiga mota, kan su fara tafia, Billie da ke zaune a passenger seat ta lura da layin motoci kusan biyar zuwa shidda wanda duk suke dauke da special plate number. So take taga wanene aka zo dauka da wannan convoy din. Ta dai san baya wuce wani politician koh dan sa koh kuma wani babban industrialist. Tana cikin wannan tunanin taga an buda ma wani dan saurayi da kwata kwata ta san koh shekaru ashirin da biyar be kai ba qofa ya shiga daya daga cikin motocin wanda dukan su Peugeot ne amma haddaden ciki duka daya aka buda ya shiga.
"Isn't that Sudais Abiso?". Taji muryar Mahra.
"Wane?". Billie ta tambaya.
"Sudais Abiso, karki gaya mun baki san shi ba on IG".
"Anya na san shi kuwa. I don't think so".
"Bari mu isa gida I'll show you his page. He's a total hottie, do you know he's one of Nigeria's richest bachelors. And he's just 23". Mahra ta fara kwararo mata hirar Sudais Abiso. Ita dai Billie hankalinta baya wani kan hirar, hankalin ta na can kan mutumin da ke zaune gidan bayan motan da ke kusa da nasu. Murmushi ya mata da suka hada ido hakan ya sa tayi saurin kauda ido. Horn din motar su Ya Kabeer suka ji, horn din sign ne na cewa su taso. Zuwa wannan lokacin su ma convoy dun motocin Abiso sun fara tashi. Volume din radio Billie ta qara bayan ta yi connecting wayar ta sannan ta qara gudun A.C sannan ta gyara zaman ta.
BINABASA MO ANG
SANADI
General FictionThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...