Kano, Nigeria.Da khayri ta ga how adamant Niima was sai ta ji ta fara karaya. Bare kuma da Niiman ta tabbatar mata da cewar ba wani tashin hankali bane ya sa take son ganin Mal Mansur din. Ce mata tayi sai ta yi shawara da Maamah da kuma Kabeer tukun zata iya bata answer.
"Ina! Sam baza a yi haka ba" Maamah ta fadi tana jin zancen "Ki bi ta ina? Ta je ta masa mene? Ina ta san shi. Ah haba a ina ma ake haka. Ai ba ma sai kin kira Kabeer ba bazakije ba khayri". Maamah ta fadi tana qara jaddada ma khayri cewar "Ba inda zaki je".
Tare suka sauko da Maamah. Nan da nan khayri ta ga expression din Maaman ya sanja kamar ba wadda ta gama tijara ba a few minutes ago. Fuskar ta dauke da fara'a take ma Niima bayani. "Kin ga shekaran jiya ta dawo daga asibiti. Jikin ba dadi, likita ya hanata yin komi ciki har da tafia, shi sa ma take nan gidan dan ta sama hutu da kulawa. Kinga koh zancen tafia be taso ba".
Wani irin disappointment Niima tayi wa khayri hakan ya kuma sa mamaki da kuma tunani akan dalilan da zasu iya sa Niima neman Baffan ta. Toh koh dama sun san juna ne tun can? Tayi tunani.
"Shikenan" Niima ta fadi tana qarawa da "Nagode. Zan wuce".
"Da wuri haka. Koh abinci baku ci ba". Alhamdulillah Niima ta ce Maamah kan suka yi sallama ta wuce. Khayri har waje bakin mota ta rakata suna tafe shuru ba wanda ke cewa komi har sai da suka isa bakin motar, Bakhtiar na ciki yana jiran futowar Niima. Kallon juna suka yi khayri bata san abunda zata ce ma Niima ba.
Rungumar ta Niima tayi tana fadin "We will meet very soon. In Shaa Allah". And with that she released her from the hug "kuma khayri ki san bazan taba cutar da ke koh wani naki ba. Za kuma kiji dalilin ya kawo ni gare ki, soon". Tana gama maganar ta shige gidan baya tare da Bakhtiar driver ya ja su.
Gaba daya ranar haka kawai khayri taji ran ta a dagule. Kan yamma wani irin wawan ciwon kai duk ya dame ta, tun tana iya jurewa har ta koma daki ta kwanta kan gado ta ci kukar da bata san dalilin sa ba. Billie ce ta shiga ta sama khayri na kuka ta wuce ta kira Maamah. Duk yadda aka yi da khayri akan ta fadi abunda ke damunta ta qi sai ce musu kawai kanta ne ke ciwo sosai. Maamah ta tausayawa khayri musamman sanda ta duba mata BP dinta ta ga ya hau, ta san ciki ne ya kawo mata haka tare da kuma damuwan da take ciki. Takaicin Kabeer ya kuma kama Maamah tana tunanin koh tun yaushe Khayri ke zaman qunci a gidansa da basu yi noticing ba.
"Kabeer na neman ja mana abun a zagi".Maamah ta fadi, talking to herself "Kai Allah ya shirya mana yaran yanzu".
Shi din ta kira ta sa shi zuwa samowa khayri magunguna amma koh da ya kawo ya buqaci ya gan ta da yaga ya jikin nata hanashi Maamah tayi. Karshe ta kore sa daga gidanta. Khayri kuma tunda ta sha maganin ta dan sama relief har barci ya dauke ta.
Tare da Ahmad suka futo waje suka shiga mota. Suna shiga koh gama rufa qofar motar Ahmad be gama ba Kabeer ya fara masa magana "Dan Allah Ahmad ka roqan mun Maamah. Dan darajar Allah, na gaji". Dariya Kabeer ya ba Ahmad.
"Me ka ma Maamah?".
"Haba Ahmad wai ni na zaman maka abun dariya? Wallahi da gaske nike" Kabeer ya fadi kamar zai kuka "Ka taya ni roqan ta khayri ta dawo gida. Kaji dan uwana". Yayi ta kokarin lallaba Ahmad.
"Aikuwa dai Maamah da wuya ta saurare ni. Ni da naji tana fadin har ta haihu tana wurin ta".
Kan sa ya dora kan steering wheel yana fadin "Innalillahi wa inna ilayhi raji'un. Na shiga uku ni Kabeer. Wai me na ma Maamah ne haka?".
"Kana da sauran aiki tunda baka ma san abunda ka mata ba". Ahmad ya fadi kan ya sake wata maganar wayar Kabeer ya fara ringing. Kabeer na daga wayar yaga sunan Zulaikha a kan screen ya saki tsaki, hakan ya sa Ahmad ya kwashe da dariya.
![](https://img.wattpad.com/cover/162179064-288-k222121.jpg)
YOU ARE READING
SANADI
General FictionThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...