Dutsen safe, Katsina.
"You did well. So proud of you". Bakhtiar ya fadi yana qara showering Niima da kisses "My little warrior". Murmushi ta masa tana qara langwabewa jikin sa.
"Ni dai bana so ka tafi". Ta fadi a shagwabe tana pouting lips dinta.
"Awwnn you poor baby" Bakhtiar fadi yana qara jawo ta "It'll be five days before you know. Zan dawo na dauke ki mu koma gidanmu".
"Five days without you is like a thousand years in the desert". Maganar ya ba Bakhtiar dariya yace mata "Allah koh? How's a thousand years in the desert?".
"Ga zafi ga immense thirst" ta fadi sitting up to place a kiss on his lips "I'll miss you. Ka qara kwana mana. Kaji mijina".
"Amma dai kin san they're like your grandparents. Last night was already awkward, bazan iya qara kwana ba" ya fadi "Because I can't stand seeing you close yet so far from me, I can't stand the thought of not having you close to me Niima so gara na koma cikin gari na jira ki". Wasa ta fara yi da yatsun hannunsa, enjoying the warmth that emanated from him.
"Shikenan B, ya na iya da kai". Yar dariya yayi yana jin dadin shagwabar da Niima ke masa.
"It's just five days ai. In je in dan side chick dina nima". Tashi tayi ta dan dake shi on his chest playfully tana fadin
"Ka ma isa!" With an eye roll "Wata ta kalle ka ba sai na cire mata idanu ba".
"Ke haba dai?" Ya tambaya tickling her. Dariya ta fara tana ya daina mana mutane suna wucewa suna kallon su tunda ta windows din motar ba ana ganin komi da ke faruwa a cikin motar "Let them watch. I don't care".
"But I do" ta fadi tana dariya.
"Shikenan na daina" Ya fadi kan ya qara da "Bari na zo na tafi tunda ana kora na". Sabon sallama suka fara suna ji kamar kada su rabu "Sudais will come with the jet, sai mu koma duka koh?". Tace masa toh shikenan. One final kiss tayi placing on his lips kan ta futa daga motar driver da ke jiransu a waje ya shiga ya fara jan motar. Bata koma ciki ba har sai da ta daina ganin motar tukun.
Surprisingly cikin kwana dayan da Niima ta yi har ta dan fara sakin jiki da kakannin nata. Freely take hira da su filling them in on all that had happened in the past nineteen years of her life. Hotunan cikin wayar ta kam tas ta gama nuna musu explaining the occasion or circumstance that had led to each photo that was taken. Haka ya qara nunawa su Mal Mansur irin kaunar da Karimatu da Abdallah suka nunawa Khayri. So ne wanda koh dan da ka haifa iyakar kauna da kulawar da zaka nuna masa kenan, Niima ta tashi a rayuwa bata san rashi ba, bata san kunci ba, ba kuma ta san wahala ba. Duk sun tabbatar cewa she grew up without any hardships. They couldn't have thought of better parents for their grandchild than the ones fate and circumstances had led her to. Hakan ya sa su Mal Mansur suka ji gaba daya they had harboured no ill feeling towards the El-Yaqoob's kuma har Baffah ya dau ma kansa alwashin zai kokarin ganin Niima ta sasanta da iyayen nata. Whilst her anger was justified, ya san in har ta juya musu baya ta butulce su sabida irin sacrifices inda suka yi making for her.
Bakhtiar be yi koh one hour da tafia ba motar Kabeer ya tsaya a exact spot inda tasa ta daga a qofar gidan Mal Mansur kaita. Yana sauka da saurin gaske ya juyo ya budawa khayri qofa ya miqa mata hannu dan ya taya ta futowa daga motar. Gidan baya ya bude ya dau yar jakkan da ta hada kayan ta already har tayi gaba ya bi ta a baya. Koh da suka shiga khayri tayi mamakin ganin yadda Niima da Inna ke zaune suna ta hira kamar wasu kawaye koh wasu wanda suka dade da sanin juna. Gaba daya kan ta ya dore amma basu mata bayanin komi ba har sai da aka kira Baffah ya dawo gida daga wurin sana'ar shi. Zaunar da khayri yayi har ma da Kabeer wanda suka tattaro kaf hankulan su suka basa. Nasiha ya fara musu akan yadda bawa baya taba wuce qaddarar sa a rayuwa da kuma tawakkali da duk abunda ya faru da bawa a rayuwar shi kan ya shiga basu labarin bayin Allahn da suka zo gidansa just a few days ago da wani labari me wuyar fahimta. Tun kan ya gama basu labarin khayri ta fara hawaye, tunda ta gane inda labarin ya dosa ta fara zubar da silent tears. Hawayen ta basu qaru ba sai da Niima ta fara narrating nata part of the story, khayri na kuka Niima na kuka. Haka suka riqe junan su suna kuka khayri tana tunanin so many memories of them and the pull she felt the first time they met, lallai kam jini ba abun wasa ba. Dama shi sa tun farko da ta fara ganin Niima taji tana kaunar ta, tun suna yara da suka fara haduwa a gidan mai har kuma haduwar su lokacin bikin Niima a Abuja da kuma yadda circumstances ya kuma leading dinsu to each other a England, all the while she had been interacting with her sister, the very flesh of her own flesh amma bata sani ba.
ESTÁS LEYENDO
SANADI
Ficción GeneralThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...
