Abuja, Nigeria.
"Duba ta mirror ka ga me Kalthum ta ke". Clearly taji sanda matar da ke zaune a gaban motar ta fadi mijin kuma ya dan juyo duban diyar sa.
"Aliyu loooook". Ba a wani jima ba ta sake jin matar tayi magana amma wannan lokacin a cikin fargaba da tashin hankali.
Firgigit tayi ta tashi daga barci. Salati tayi kan ta miqe zaune. Wai me ya sa yan kwanakin nan take yawan yi wannan mafarki ne? Kuma a cikin mafarkin nata komi iri daya, mutanen cikin mafarkin basu taba sanjawa ba, sannan abunda ya faru cikin mafarkin be taba sanjawa ba, har ta hanyar da suke iri daya ne a ko wani mafarki. Me ke faruwa da ita ne? Me ya sa take mafarkin mutanen da bata san su ba. Ta jima a zaune shuru tana nazari iri iri kan can wani abu ya fado mata a rai. Da sauri ta sauko daga kan gado ta zura flip-flop dinta kan ta futa daga dakinta ta nufa hanyar drawing room din Abban ta. Ba tare da ta tsaya wata wata ba ta wuce directly zuwa drawer din da ta boye hoton da ta tsinta a qasa earlier, hoton iyayen Khayri. Bayan hoton ta duba ta sake duba sunayen da taga an rubuta a jiki da kuma shekaran da aka yi hoton. Kan ta taji yayi wani mugun nauyi da ta sake duba fuskokin su, koh shakka babu wannan mutanen sune wanda take gani a mafarkin ta. Toh amma kuma iyayen khayri ne su, meyasa take mafarkin su? Menene hadin ta da su, kuma is she really having a dream or is an old memory coming back to her?.
Daga kanta tayi ta maida attention dinta zuwa ga trestle table inda Umminta ta jera hotunan ta. Kan hoton 4th birthday dinta idanunta suka fada. Miqewa tayi ta qarasa zuwa table din ta daga hoton a hannunta ta kalla sannan ta kalla hoton iyayen Khayri.
"Why do I so much look like this dead girl?" Ta tambaya kanta. Sosai ta qurawa hoton kallo tana tunani akan how possible it is for two different people to bear such an uncanny resemblance, tamkar mutum daya.
Bata ankara ba taji an buda qofar an shigo cikin dakin, haka ya sa ta rude har ta saki hoton da ke riqe hannunta. Shikuma frame dinta ta ije shi inda yike. Koh da ta juya Abbanta ta samu tsaye, sanye yike da kayan barci.
"Niima na, baki kwanta ba". Ya tambaye ta with concern laced in his voice.
"Kai ma baka kwanta ba Abba".
"Can't sleep". Ya fadi a hankula. Da hannu yayi mata signal cewar ta zo su zauna tare. Ba musu ta taho ta zauna kusa da mahaifin ta. Sun dade ba wanda ya ce wa kowa komi hasalima shi Abdallah wayar sa ya shiga latsawa. Daga baya Niima ta zame ta kwanta, ta dora kanta akan cinyoyin Abdallah. Kallonta yayi ya mata murmushi kan ya sake maida attention dinsa to wayarsa.
"Abba". Ta kira sunan sa a hankula. Kallonta yayi be ce komi ba "Are you worried?". Ta tambaye sa still be yi magana ba ya juya mata kai alamar no.
"Toh me ke damun ka?". Ta tambaya.
"Kewar ki na fara". Ya fadi a shagwabe hakan ya sa Niima dariya.
"Ai ba barin gari zanyi ba".
"Amma zaki bar gida".
"Zaka iya zuwa gani na ai anytime you miss me".
"A gidan mijinki Ni'imatullah, ni mahaifin ki sai nazo gidan mijinki ganin ki". Dariya duka suka yi dan Abdallah be saba kiran sunanta completely ba.
"Why that name? Of all the names in this world, why Ni'imatullah?". Ta tambaya.
Sai da Abdallah ya dan murmusa kan ya bata ansa "Because you are Allah's blessing to us". Hannunta da ya riqe ya yi kissing kan ya cigaba "God gave you to us after ten years of waiting, in bamu kiraki Ni'imatullah ba? Me zamu ce miki". Murmushi tayi wanda ya bayyana dimple dinta na gefe daya.
YOU ARE READING
SANADI
General FictionThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...