Kano, Nigeria.
Koh da suka isa kano yamma ya riga yayi dan ana kiran sallan maghreb suka isa gida, already su Rumaisa da su khalid sun isa gidan Dattijo, dama al'adar su ce, duk ranar Saturday gidan Dattijo suke taruwa dukan su sai bayan dinner kowa ke komawa gidan sa. Koh da suka isa da sauri kabeer ya fito daga motar. Zayd da Zayn ne suka fara rugowa da gudu suka tare sa. Duka su biyun ya dauka, ya riqe daya a right arm dinsa, daya a left ya shige ciki da su yana complain wai zasu nakasa shi saboda nauyin su, su kam sai murna suke dan dama sun qosa ya dawo.
Khayri ta sauko daga mota bakinta ya kusa kaiwa qasa, ta tsaya tana kallon makeken ginin da ke gabanta, sai nazari take akan yawan mutanen da ke zama a gidan. A zuciyar ta tana fadi ai gidan zai isa kaf mutan garinsu. Wai nan shine gidan da zata dinga zama. Sai juye juye take tana duban irin hadadden design din gidan, ba abunda ya fi burge ta kamar fountain inda ke tsakiyar harabar gidan, wanda a tsakiya akwai statue din mace da goyo ta riqe tulu, ruwa na zubowa daga tulun. Sosai abun ke mata dadi har bata san lokacin da Billie da Mahra suka iso inda take ba.
"Barka da isowa" Mahra ta fadi tana murmushi, hakan yasa ta juyo towards direction dinsu.
"Ya Allah! She's prettier than I imagined Mahra". Billie ta fadi tana jawo ta zuwa Jikin ta "Look how chubby she is". Billie ta fadi tana taba mata kumatu, duka dariya suka yi kan Mahra ta yi introducing kanta, itama Billie tayi introducing kanta. Sosai khayri taji hankalinta ya kwanta da taga akwai sa'o'in ta a gidan and they seemed nice. Ahmad da ya shiga ma khayri da babban box dinta ne ya dawo ya same su inda ya bar su. Daukar kananun bags in yayi kan yace musu su wuce ciki, Maamah na ciki na jiran su kuma su bari khayri ta shiga ta huta. Suna isa foyer din gidan da Maamah suka fara karo tana tafe Anisa na bin ta a baya da kuma wata yarinya biye dasu.
"Look, look Anisa she's so pretty, ya Allah". Maamah ta fadi in a dramatic way, hannunta kan kumatun ta tana ma khayri murmushi. Har qasa khayri ta durkusa ta gaida su amma Maamah tace mata ta miqe. Sai da suka gama gaisuwa suka yi introducing kansu kan Maamah tace su Billie su wuce sama da ita ta watsa ruwa ta dan huta kan a gama shirya dinner.
"Ahmad, yalla habibi". Maamah ta tsayar da shi bayan ya kai last bag din khayri ya sauko zai koma waje dun dauko nonon da aka basu su kawo ma Addah Manga "This Amaal. Amaal Baffah" Ta yi introducing dayar yarinyar da ke tare dasu amma sai ta lura da facial expression din Ahmad kamar be gane ta ba "ka tuna wannan kawar tawa? The one that used to come visit from Gombe when you boys were little?". Maamah ta masa kwatancen mahaifiyar Amaal har sai da ya gane. Suna gama gaisuwa Anisa ta ja hannunta suka wuce dan dama sun fito suna ba Amaal tour din mansion din ne. Barin Maamah suka yi tare da Ahmad dan Anisa taga alamar conversation din nasu will need a bit of privacy.
"She's so pretty, don't you think?". Maamah ta tambaya tana kallonsa, murmushi yaga tana yi hakan ya sa shi susa qeyar sa.
"Maamaaaaaaah" yayi stressing sunan.
"It's okay. Take your time, she'll be here for 6 months. She'll intern at your brother's firm. Get to know her, she'll make a lovely wife, na yadda ta tarbiyyan gidansu". Maamah tayi whispering masa a kunne kan ta fara tafia. Har ta kai bakin qofa ta juya ta dube sa "Ka shigo da wuri yanzu zaa kira sallah".
Kauyanci sosai khayri tayi da taga dakin da aka kaita wai nan ne dakinta. Daki ne qato sosai, yana facing dakin Mahra. Akwai qaton gado a dakin, walk in closet wanda already har wata me aiki ta fara jera mata ýan kayakin ta a ciki, ga vanity table wanda an riga anyi arranging duk wani abunda ýar budurwa zata buqata. Cabinets din bathroom dinma komi an ije, from toiletries to a first aid kit. Sosai su Billie suka ji dadi da tace musu dakin ya hadu dan dama su da kansu suka yi arranging komi da komi a dakin. Dama room din spare room ne wanda in Billie tazo take sauka, amma kuma kasancewar in tana tare da Mahra ba me iya raba su ya sa most times in tana gidan tare suke kwana.

KAMU SEDANG MEMBACA
SANADI
Fiksi UmumThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...