Babi Na Hudu (04).

1.8K 267 7
                                    

JULY 2012.
Dutsen Safe, Katsina State.

Yarinya ce ýar shekara goma sha shidda ta shigo cikin gidansu ta gudu tana waqa, yarinyar ýar lukuta da ita sai dai fara ce tas kyakyawa gashi in tayi murmushi koh dariya dimple dinta da ke kumatu daya na fitowa. Tsayuwa tayi gaban Kakarta da ke hura wutan icce tana mata rawa tana karkada bangles dinta to make a jingling sound.

"Allah ya shirya mun ke khayriyya da tsananin son awarwaron ki". Inna ta fadi tana dariya. Suna cikin haka kakanta namiji ya shigo cikin gidan tare da babur dinsa. Da gudu ta ruga ta masa sannu da zuwa. Dariya yayi ya miqo mata ýar leda wadda tsire ce a ciki, a Kullum in Baffan ta zai dawo kasuwa sai ya mata tsaraba koh kosai koh tsire, wataran ma duka biyun yike hadawa ya saya mata. A wasu kwanakin kuma biscuits zai siya mata da kayan kwalama dai irin na nasara.

"Wallahi Baffah kai ke bata Khayriyya. Ace komi take bida ka dauka ka bada, yarinya bata san babu ba". Gwamandi ta fadi tana cigaba da hura wutan ta.

"Nidai Baffah kace ta daina bata min suna. Khayri sunana". Ta fadi tana dan tabe baki.

"Toh kin ji ai Gwamandi. Ki daina bata wa ýar lele na suna. Khayri sunanta".

"Oh ni Gwamandi! Yanzu biye mata zaka yi? Toh ance Khayriyyan". Ta fadi da wasa.

So da kauna na sosai Baffah da Gwamandi ke nunawa ýar jikar su don duk duniya basu da irin ta. Gashi dai a kauye ta taso amma ta tashi ne cikin wadata dan komi da take buqata na rayuwa kakannin ta suna iyakar kokarin su dan ganin an sama mata. Harta karatu tana daya daga cikin very few girls inda ke karatu a kauyensu, sai dai yadda karatun kauye ba daya ba da birni ba, iyakar ta primary school kasancewar babu makarantar secondary a garinsu nasu sai an tafi can kaita. Hakan ya sa Baffah yanke hukuncin yi wa abokin sa Alhaji Dikko magana koh in zai yarda sai ya kawo ta kano ta zauna karkashin sa dun samun Ilimi saboda khayri yarinya ce wadda Allah ya dora mata son karatu, ga shi tana da burin zaman nurse. Tun faruwar wannan hatsari da ya dauki ran iyayen khayri, wani abokan ta ya shiga tsakanin Alhaji Dikko da malam Mansur. Akai akai yana kiran malam Mansur din zuwa wajen sa a kano kasancewar shi he's a very busy man, zuwa ziyara na masa wuya amma yana kokarin kiran sa yazo. In dai yazo sha tara na arziki ake masa ya koma kauye, haka duk Karshen wata sai ya aika da dan aiken sa da kudi dubu ashirin a kawo wa Baffah dun taimakawa wajen kula da khayri.

Tabarma babba khayri ta shiga daki ta dauko ta shimfida a filin cikin gidansu kan Inna tazo ta dire kwanukan samira wanda dauke suke da tuwon da ta gama tuqawa. Al'adar su ce zama a ci abincin dare tare, in sun gama a zauna ayi hira kan su shiga daki barci. Koh da suka gama cin abinci kwanciya khayri tayi ta dora kanta samar cinyar Baffah.

"So kike ki karasa masa kahahun". Fadin Inna amma sai Baffah ya gwale ta ya ce mata ba ruwan ta. Wai kawai kishi take.

"Yawwa nikam Baffah dazu kana hita sai ga dan nan yazo neman ka". Ta dan tsaya nazarin sunan tana taunan goron ta "Wannan da, dan wajen malam Zubairu tsohon masinja. Ya ike da suna ma ni Gwamandi".

"Isuhu?". Baffah ya tambaya shi kansa taunan goron yike.

"Yawwa shi" ta fadi tana dan tafa hannu "Yazo ne akan zancen dan wajen sa Qasimu, wanda ke sayar da gwanjo bakin kasuwa. Wai yaga ýar nan yana so shine yace yazo ya sanar da kai. Sai kuma gashi kun sha ban ban a hanya dun kana hita ya shigo shikam". Ta masa bayani.

"Tab! Khayrin yike so".

"Ee, ita wai".

"Toh ina fatan dai kin hidi masa karatu zatai". Baffah ya tambaya.

"Haba dai Baffah, ai koh can dakin ta ta yi. Baka gani duk sa'o'in ta suna dakin su har da masu yara. Shekaru qara ja suke".

"Ke ni bama wannan ba. Kema dai kin san karatu diyar nan take so tayi, wani zancen aure kuma. Haba Safiyya". Baffah ya yi magana yana furta sunan Gwamandi na asali.

SANADIWhere stories live. Discover now