Babi Na Goma Sha Biyu (12).

1K 178 11
                                    

Abuja, Nigeria.

"Abdallah, Abdallah, Abdallah". Bakhtiar ya kira sunan Abdallah El-Yaqoob cikin muryar sa me tsananin sanyi.

"Please Bakhtiar i need you to help me, Dan Allah".

"Meyasa ranar da nace maka mu hadu baka zo ba. I hate people who have little respect for commitments". Wannan karan rai a dan bace yayi maganar kasancewar Bakhtiar mutum wanda ke matukar respecting commitments.

"Kayi haquri, I've been in a fix Bakhtiar and right now ban tunanin akwai wanda zai iya fitar dani daga cikin matsalar da nike ciki face kai da taimakon Allah". Duqar da kai Bakhtiar yayi ya kalla board inda suka gama playing chess. Yar murmushi yayi kan ya dago ya kalla Abdallah.

"I love your daughter, so much". Takaici ne ya dan fara kama Abdallah dan shi gaba daya ba wannan zancen bane a gabansa, matsalar da ke gabansa was far greater than zancen wani soyayyar tsakanin Niima da Bakhtiar.

Lura da fuskar Abdallah yayi yaga yadda expression dinsa ya sanja. Haqiqa koh ma me ke damunsa ba karamin abu bane dan haka yike gani ya kamata yayi using opportunity dinsa wisely.

"It has to do with Ni'imatullah" Abdallah ya fadi, finally having Bakhtiar's attention. Tabbas sai a lokacin Abdallah ya hango irin soyayyar da Bakhtiar ke wa diyarsa.

"We had an agreement with Inno Marte a few years back. I......" Be gama ba Bakhtiar ya katse sa.

"Inno Marte?" Sai da yayi wani dariya me tsananin qara kan ya juya ya kalla Abdallah "This is getting fun. Me ya hada ka da Inno Marte?" Ya tambaya before sipping the expensive wine they were served by one of his kitchen staffs.
.

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
.

KANO, NIGERIA

Cikin zafin rai Kabeer ya miqe yana wurgawa Dattijo wani irin kallo me cike da bacin rai. Dan runtse idanu Maama tayi, haqiqa abun da tayi gudun faruwar sa tun farko ke shirin aukuwa, ita dama ta san babu yadda zaayi Kabeer ya taba yarda da wannan shiri na Dattijo.

"I'm not marrying Billie" ya yi announcing with finalty in his tone. Sosai Billie taji wani faduwan gaba, murnar ta tuni ya juya ya koma baqin ciki. Khayr wadda har zuwa lokacin bata ce komi ba ta dan dago kanta, directly idanunta suka fada kan Kabeer sai ji tayi wani irin tausayin sa na ratsa ta. Gaba daya ta rasa meyasa a rayuwa take matukar tausayin Kabeer duk da irin muguntar da yike mata. A hankula ta duqar kanta da hawayen da take ta kokarin riqewa suka fara saukowa kan kumatun ta a hankula. Maamah kam sosai ta maida da attention dinta kan khayr wadda ta lura cewa tana cikin baqin ciki.

'Oh Allah, protect my family from the war which is threatening to start' ta fadi a cikin zucin ta. Sosai yar autar ta ta fara bata tausayi dan zuwa wannan lokacin Rumaisa ta gama believing cewar akwai wani affection tsakanin Khayr da Kabeer.

"You will marry her and my words are final" Dattijo wanda shima ya miqe ya zo eye level da jikan nasa ya fadi. Duk su biyun su kowa naji da taurin kansa.

"Not in this life, and definitely not in the hereafter" Kabeer ya yi declaring, idanunsa kan na Dattijo koh kiftawa baya yi.

"Zamu gani" Dattijo ya fadi..Yana fadin haka ran Kabeer ya qara baci kawai ya fara takawa zuwa hanyar sama. Shima Dattijo cike da bacin rai ya nema hanyar study dinsa, Uncle Sadiq ne ya bi bayansa a guje dan ya san sosai ran sa ya baci. Mahra itama sama ta wuce dakinta ta rufe kanta, while Billie ta ruga a guje zuwa garden din gidan Ahmad na biye da ita a baya dan kwantar mata da hankali bayan shi yama fi kowa experiencing heartbreak amma tsananin zurfin ciki ya sa ya kasa nunawa. Khalid kam kamar Allah Allah yike a watse ya yi wucewar sa, he needed to celebrate that night dan judging from outcome din meeting din da alamun zai ci nasara akan Kabeer, dan ya san muddin be yi abunda Dattijo ya umurce sa da ya yi ba, babu yadda zaayi Dattijo yayi handing over business empire dinsa over to him.

SANADIWhere stories live. Discover now