Dutsen Safe, Katsina State.
"Damn!" Kabeer ya fadi "Is this the place?". Ya tambaya, nodding kai kawai Ahmad wanda ke tuqi yayi, dama ya san hanyar kasancewar akwai wani zuwa da Malam Mansur yayi, shi Dattijo ya sa ya maida shi gida. Shikam kabeer tunda suka bar kano ran sa a hade yike dan shi a ganin sa an shiga haqqin sa, gashi be sama barci yadda yike so ba gashi plans in sa da Zulaikha had to be cancelled.
"I cancelled my plans with Zulaikha just to come to this chicken hole!". Ya fadi da qarfi "For a village rag?".
"Mind your language" Ahmad wanda ke gyara parking yayi warning dan uwan nasa who was acting like a typical spoilt brat. Yana gama gyarawa ya buda mota ya sauko shikuma kabeer ya zauna a ciki yaqi fitowa, wai shi dai a nan cikin mota zai zauna ya jira fitowar su kan ya shiga yayi contacting infection. Harara sosai Ahmad ya galla masa kan ya zago side dinsa ya buda kofar ya ce masa ya fito.
"I'll count to 5, wallahi KB in baka fito ba daga ka zanyi and kamar Dattijo ya gama ji. You rude human being". Rolling idanu kawai kabeer yayi kan ya tuna ma Ahmad cewa shine babba, "Babban banza ba". Ahmad ya fadi, hakan ya sa kabeer fitowa ya biyo sa da gudu. Haka suka fara zagaya motar, kabeer yana qoqarin kamo Ahmad. A haka Malam Mansur ya fito ya same su suna guje guje kamar yara. Ahmad ne ya fara hango sa hakan ya sa suka tsaya, kabeer ya gyara murya kan yayi faking wani irin smile that although fake, made him look breathtakingly amazing. Murmushi shima Malam Mansur din yayi kan ya miqa musu hannu for a handshake, reluctantly kabeer ya miqa hannunsa a mind dinsa yana taking mental note to use a hand sanitiser as soon as he could. Shi dama tun asali mutum ne me shegen kyama, obsessive compulsive disorder (OCD) a yaren bature. Koh da suka shiga filin gidan tsaf tsaf an share, an shimfida babban tabarma a tsakar gida. Zama suka yi suka fara dan taba hira, mostly Malam Mansur da Ahmad ke magana, shikuma kabeer yana kan wayar sa yana chatting da sahibar sa.
Basu jima ba Inna ta fito riqe da kwarya wanda fura ne me sanyin gaske wanda aka tanada musamman dan zuwansu. Ije wa tayi a gabansu kan ta koma gefe ta zauna suka fara gaisuwa. Ganin yadda kabeer ke ta gumi ya sa ta shiga ciki ta dauko mafici ta basu kan tace ma khayri ta fito ta gaida baqi. Itama cike da fara'a ta fito ta gaida su. Koh da kabeer ya dago ya Kalle ta sai da ya dan jawo shades dinsa zuwa kan hanci ya sake kallon ta da kyau kan ya kira sunan Ahmad.
"Bro". Ya fadi a hankula "Is she the one going back to kano with us". Cikin fara'a Ahmad ya daga masa kai alamar ehh "This fat hippo! No way". Kabeer ya fadi yana dariya. Wani irin kallo Ahmad ya juya ya dan masa kan ya dauke gaze dinsa from him ya cigaba da shan furar sa, kabeer kam koh kallon kwaryar be yi ba. Suna zaune basu gama shan furar ba aka dire masu kayan abinci, taliyar hausa ce wadda ta sha kayan hadi, ga kifi an zuba a ciki amma koh da kabeer ya kalla sai wani irin fuska yayi kamar abincin ya basa kyama.
"You don't expect me to eat that shit". Ya fadi in a low voice wanda ya tabbata Ahmad ne kadai zai ji sa, koh da Inna ta masa magana akan ya be cin abinci sai ce mata yayi azumi yike. Shikam Ahmad din koh ta kansa be bi ba ya miqe ya wanko hannunsa ya dawo ya zauna ya fara ci har da santi, yana ta praising din Inna.
"Kai Inna wannan taliyar taki tayi dadi, ban taba cin taliyar hausa me dadin wannan ba". Murmushi Inna tayi tana masa fifita tace ai ba ita tayi ba, khayri ce tayi. A haka suka cigaba da hira Ahmad yana fadi mata cewar yafi shekara goma be ci taliyar hausa ba. Yana gama ci ya wanke hannayen sa kan suka miqe dan gabatar da sallah su kama hanya. Ana fara sallama kabeer ya wuce ya shige mota koh jaka daya na khayri be dauka mata zuwa mota ba.
"Haka nan in kwaso kudin cizo". A fadin sa.
Ita kam Khayri dama tun daga lokacin da aka yi concluding komawar ta kano Inna ta fara hada mata kayan ta. Sabon akwati Baffah ya bada kudi aka sayo aka wanke kayan ta tas aka guga su kan aka jera mata su a ciki. Ana gobe zuwansu Ahmad dama ta riga ta gama sallama da duk wani wanda take mutunci da shi, kitso ta tafi aka kwashe mata, tana dawowa Inna ta kwaba lalli me taki aka mata tsohuwa ta fada kwata.

YOU ARE READING
SANADI
General FictionThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...