Check out the new cover people, designed by my sweetest heart TheOmoope. Thanks babe, you're a darling 😍💖😘. Love you loads🤩
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Borno, Nigeria.
Fitar motocin Bakhtiar Al-Arab yayi daidai da shigowar Sudais Abiso gida. Sanda motar sa yazo daidai da wanda Bakhtiar ke ciki dan slowing down yayi yana kallon mutumin da ke zaune gidan baya yana ansa waya. Bakhtiar on the other hand wanda ke waya da lawyer dinsa yaji wani force na pulling dinsa towards the opposite direction. Juyawa yayi suka hada ido da Sudais ya dan masa nodding kai alamar gaisuwa shima Sudais din dan nodding masa kai yayi kan ya wuce yayi parking a spot inda ya saba parking motar sa. Da sauri ya fito ya ruga ciki da gudu dan tambayar mahaifiyar sa waye baqon da ya gani yanzu yanzu yana barin estate dinsu.
Da gudun sa ya hau sama inda ya san Inno Marte tana karban manyan baqin ta, amma halin da ya sama dakin ya daga masa hankali. Broken pieces of glass ya gani ta koh ina ga kuma drops din jini. Da gudu ya ruga next floor dan zuwa wajen Inno amma koh da ya hau tun daga qofa most trusted maid dinta ta fadi masa cewar tana shiri ne, ya jirata a drawing room dinta she'll join him shortly.
Ba gardama Sudais ya wuce drawing din bayan yayi kira qasa can kitchen cewar a aiko masa da tea sama. Sudais Abiso matashi ne dan shekaru ashirin da uku wanda Allah ya azurta da matukar kyau, ga kwarjini ga arziki da Allah ya azurta shi sa shi, nasa na kansa dan at a very young age ya riga yayi owning nasa business din, one of the top restaurant and viewing center a Borno. Sudais irin mutanen nan ne wanda da ka gansu kasan they're arrogant, amma kuma sai ka zauna da shi zaka gane mutum ne me matukar sanyi da tausayi unlike his mother wadda ya dau son duk duniya ya dora mata. Shine da namiji na farko na kuma karshe a wajen Inno Marte kasancewar yaya mata uku kawai Allah ya bata. Aisha Abiso itace diyarta ta fari, sai Hadiza Abiso wanda tun suna yara suke kasar waje, basu wani girma hannun mahaifiyar ta su ba unlike her last daughter Suraiya Abiso wadda daga ita sai Sudais Wanda Inno Marte ta haifa a lokacin da shekaru suka fara ja mata dan bayan Suraiya sai da tayi shekaru ashirin da uku kan ta sama Sudais. Her one and only heir.
Murmushi Sudais yayi wa me aikin da ya kawo masa tea dinsa Kan yace "Thank you". Fitan me aikin yayi daidai da shigowar Inno Marte sanye da wata fara lace lifayya fari qal, ta sake wanka. Lifayyan ya rufe mata wuya dan kar Sudais yaga marks inda Bakhtiar ya bar mata a wuya. Tana ganinsa ta saki wata yar murmushi, a plan slowly forming in her head. Sai da ya fara tambayar ta mesa yaga dakin karbar bakin ta in a mess, ta hado karya ta fadi masa cewar it was just a small accident.
"Ammi wane baqon da naga ya fita gidan nan da zan shigo" ya tambaya bayan ya kwanta ya dora kansa a kafafunta.
A hankula take ta shafa lallausar gashin da ke kansa wanda koh kadan be yi Kamar da gashin yan Nigeria. Gashin nada matukar baqi ga laushi sai kace na buzaye koh larabawa "Oh that" ta fadi a hankula "That was Bakhtiar Al-Arab. Yazo kawo mana gayyatar zuwa bikinsa wanda ke gabatowa" ta fadi. Uhmmm kawai Sudais ya fadi, a ransa yana ji Kamar ba haduwar su na farko kenan ba da Bakhtiar ba.
"Amma ya taba zuwa estate dinmu koh Ammi?". Ya tambaya.
"Me ka gani?".
"Ji nayi Kamar na taba ganinsa, kuma a nan gidan".
Sai da ta dan sauke ijiyar zuci kan ta basa ansa "Zuwan sa na farko kenan Abiso estate qalbi" kissing gashin sa tayi "Ai zaka je bikin sa koh?".
"Indai zaki".
"Masha Allah. But qalbi akwai maganar da ya kamata muyi, game da wadda zai aura". Ta fadi. Hakan ya jawo hankalin Sudais.
A fusace ya miqe zaune da Inno ta sanar da shi wadda Bakhtiar zai aura. Sosai yaji ransa na wani quna dan tun be kai shekara ashirin ba aka sanar da shi cewa Ni'imatullah Abdallah El-Yaqoob ita ce matar da zai aura, kuma tun ranar da ya sa ido ya ganta yaji ya kamu da son ta.
VOCÊ ESTÁ LENDO
SANADI
Ficção GeralThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...
