.Kano, Nigeria.
.
°°°°°°°°°°°°°°°°°
.
Koh da ta shiga cikin gidan, kai tsaye babban living room inda ke qasa ta wuce dan ta san a nan zata sama mutan gidan zaune. Aikam tana shiga ta sama Adda Manga zaune da Mahra da kuma wata yarinyar da bata san ta ba. Da fara'a Adda Manga tayi mata maraba kan tace mata ta matso kusa da ita ta zauna. Sai da tayi hugging Mahra kan ta nema wuri kusa da Adda Manga ta zauna.
"Zulaikha ina kika shiga. Kwana biyu bamu ganinki".
"I travelled to Paris for work, I just returned some few weeks ago and I've been catching up on my rest" tayiwa Adda Manga bayani in her polished English kan ta matsa kusa da Mahra ta fara nuna mata some of the shots na recent work dinta.
Hakika Zulaikha Al-Fayeed ta kasance mace me kyau, irin matan da baa musu kallo daya kawai a dauke kai. Harta mata yan uwanta yabawa suke da tsananin kyaun da Allah ya mata. Hakan ya sa tun shigowar ta khayri ke ta satar kallonta. Fatar jikinta har wani walkiya yike, ga ta siririya da dogon gashi baqi wuluk. She possessed everything, ga wani murya me dadi da Allah ya bata. Ba abunda ya burge Khayri kamar yadda turanci ke fita daga bakinta kamar dama don ita aka yi yaren. Yawancin maganganunta ba ganewa Khayri ke yi ba saboda accent dinta.
"Where's MKD?" Ta tambaya bayan ta dan yi zama na wani lokaci da su "He has been ignoring me ever since he ditched dinner with me" ta sake fadi fuskar ta dauke da murmushi.
"Check him upstairs in his room" Mahra ta fadi mata. Miqewa tayi ta haura sama bata tsaya koh ina ba direct sai a bakin kofar dakin Kabeer. Ta daga hannu kenan zata buga kofar kawai sai gashi ya buda kofar. Sanye yike da kaya all black from head to toe, kansa a jiqe.
Murmushi sosai ta saki ganinsa, shima murmushi yayi mata kan ta kankame sa in a very tight hug "Amore" ta fadi a muryar ta wanda Kabeer yaji ya kwantar masa da hankali, all his worries long forgotten "Amishu" ta fadi in a playful voice.
"Amishu too" shima ya fadi yana qara jawo ta jiki. Dago kai tayi zata kai masa kiss yayi dodging dinta "What are you doing. So kike a ganmu" ya fadi.
"And so? We're in the twenty-first century".
"I wish my grandfather would understand that" ya fadi "Anyways I was on my way to see you".
"And now I'm here. Mu fita, let's hang out". Ta fadi. Har qasa suka sauko hannunsu cikin na juna. A hanyar su na sauka suka ci karo da Khayri tazo hawa sama. Tambayar sa Zulaikha tayi wacece ita.
"No one important. Mu je" ya fadi. Sosai Khayri taji wani irin zafi a ran ta ba wai dan ta gane abunda ya fadi ba sai dan yadda taga Ya Kabeer nawa Zulaikha dariya, gashi sun sauko qasa hannunsu cikin na juna. Suna wuce ta ruga daki ta rufe ta zube kan gado ta fara kuka. Daga gani wannan yarinyar da tazo soyayya suke da Ya Kabeer kuma Khayri a ganinta ba yadda zaa yi Ya Kabeer ya bar yarinya me tsananin kyaun nan, ga ilmi da wayewa for someone like her, Yar kauye wadda bata san komi ba game da zamani.
Sukam Kabeer suna fita basu tsaya koh ina ba sai favourite tea shop dinsu. Kabeer yayi ordering for coffee and waffles while ita Zulaikha tayi ordering for chamomile tea kawai, a cewar ta tana diet. Sun dan jima suna hira catching up on the while they were away. Sosai Zulaikha taso dago zancen date dinsu da yayi cancelling at the dying minute amma kuma sanin waye Kabeer ta san in ta basa time zai mata bayani yadda zata fahimta.
"Marry me Zulaikha". Zaro idanu tayi, saura qiris ta shaqe da tea inda take sha saboda tsananin mamaki. Wai Kabeer ne ke mata zancen aure, tun yanzu? Bayan sun riga sun yarda cewa zasuyi focusing on careers dinsu for a while kan su fara tunanin taking things further.
YOU ARE READING
SANADI
General FictionThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...