Babi Na Hamsin Da Uku (53).

672 108 24
                                        


"I moved from the UK to the States for college and a nan na hadu da Hadiza Abiso through a friend who had introduced us" murmushi yayi yana tuno memories dinsu. A lokacin da aka fara hadashi da Hadiza akan suyi dating ne, but after trying for a while they decided they were better off as friends dan haka suka yi breaking up sai suka cigaba da friendship. Da wasa da wasa har suka zama really close har wani hutu ta taba tafia UK da shi tayi hutu a can gidan iyayensa.

"We were young, rich and stupid Niima. We did things we're not proud of saying we did duk a sunan yarinta da kuma hauka irin na yara who are born privileged". Labari ya fara bata na that fateful day, ranar da suka tafka babbar kuskure. Suna dawowa cikin dare daga birthday party din wani school mate dinsu. They were both high, shi da Hadiza who had insisted on driving them. "It all happened so fast, one minute we were giggling and singing along to the music that was playing. He appeared from nowhere... this man..." Ya fadi kan ya yi shuru. Sai da ya ja wata doguwar numfashi ya cigaba amma tun kan ya cigaba ma Niima ta riga ta gane inda labarin ya dosa. Tunda ya yi mentioning man kawai mind dinta went back to the clippings she received. Yanzu ta san identify in wanda ya aiko mata da clippings din.

"Tamer Wahab" ta fadi sunan sa quietly kamar tana tsoron fadin sunan "You hit him". Runtse idanunsa yayi, too ashamed to look at her. "He was a son to a sick mother, husband and father to two young children and you hit him and left him there to die. You killed him".

Da saurin sa ya ce "No!" Yana kallon cikin idanunta, urging her to look at him, to hear his side of the story and to believe him.

"I did my best Niima. But I'm only human". Duka suka yi shuru ba wanda ya sake magana sai kamar bayan minti biyar Niima ta ce masa ya cigaba da bata labarin, she wanted to know everything that happened.

"She didn't see him early. Sanda kuma ta hango shi it was too late. The high left us immediately, we were suddenly sober". Futowa sukayi daga motar, Bakhtiar na ganin jinin da ke futowa daga kan mutumin ya koma gefe ya fara kwaro amai. Ya dawo ya zauna yana ta kuka ya rasa abunda zai yi. Hadiza ce ta dinga jan sa wai they have to leave before anyone came and saw them.

"Amma baza mu bar shi a nan ba. We have to call the police Hadiza, he could die if we leave him here". Hadiza who was a medical student ta riga tayi checking pulse dinsa sanda Bakhtiar ke ta kwaro amai.

"He's already dead Bakhtiar. We have to leave".

"Shit!" Bakhtiar ya fadi kukansa na qaruwa Hadiza na jan sa su tafi "Baza mu iya barin sa ba Hadiza we have to tell the police. What have we done?". Ya fadi yana kuka.

"And what Bakhtiar? We go to prison? I loose the chance of ever becoming a doctor? No! Let's go".

"Hadizaaaa" Bakhtiar ya fadi.

"I can't be a bloody felon you understand Bakhtiar! Koh baka san zaa mana gwaji ba? What do you think will happen when they trace the drugs in our systems. We will bloody go to jail and that's the end of us so we're going ka gane, get that straight!".

"Zasu yi bincike zasu gano mu".

"Don't worry my mom will take care of everything. Yanzu mu tafi muna komawa gida I'll give her a call, don't worry okay?" Ta fadi tana hugging dinsa to comfort him. Bin ta yayi suka shiga mota suka ja suka wuce suka bar gawan mutumin da suka buge a wajen. Suna komawa gidan Bakhtiar kam Hadiza ta kira mamanta wadda tace mata gari na wayewa she was coming to the States.

"That was the first time ever da na hadu da Hajja Fadime Abiso". Ranar Inno tana isowa tare da lawyer dinta and her handy man who carried out all her dirty laundries suka shiga closed meeting tare da su Bakhtiar. Abunda ta fara tambayar su was motar Bakhtiar inda Hadiza ta tuqa.

SANADICerita yang bikin terobses. Temukan sekarang