Babi Na sittin Da Biyu (62).

650 134 57
                                    


Koh juyawa bata yi ta kalle sa ba ta cigaba da abunda take yi. Hakan ya sa ya ja kujera ya zauna be kuma ce mata komi ba ita kuma ta cigaba da heating up leftover food inda ta ciro daga fridge kamar bata san yana cikin kitchen din ba tare da ita. Tana gamawa ta zuba a plate ta dawo table ta zauna ta fara ci. Matsowa kusa da ita yayi ya fara mata magana. Ba zatto ba tsammani yaga ta miqe ta daga plate din abincin da kwata kwata spoon basu wuci biyu ba tayi ta kai sink ta ije ta juya ta dau apple zata wuce.

"Ina zakije?". Ya tambaya.

"I think I just lost my appetite thanks to a certain someone". Ta fadi ta wuce. Saurin janyo hannun ta yayi ita kuma khayri da karfin ta ta fisge hannun "Na fadi maka kada ka kuskura ka kuma taba ni". Ta juya ta wuce dakin ta. Kabeer yana jin qarar key inda ta juya ta rufe qofar dakin dan ma kar yace zai biyo ta.

Wayar ta da ke kashe ta dauka ta kunna. Messages uku ne suka shigo daga number din Maamah dan haka Khayri ta kwanta da niyyar kiran Maamah in gari ya waye. Kwanciya tayi shuru tana ta tufka da warwara. Abubuwa daban daban suka yi ta zuwan mata zuciya akan auran ta da Ya Kabeer. Wata zuciyar na bata cewar kawai ta ma Maamah bayanin komi su maida ta gida zai fi mata, wata zuciyar kuma na bata cewar kawai tunda ta fadin masa abunda ke ranta ta tsaya ta ga koh zai sanja towards her or not.

Khayri bata tashi da asubah ba sabida al'ada da take yi amma sai kiran Maamah ne ya tashe ta da safiyar Allah. Tana dagawa Maamah ta fara kwararo mata tambayoyi akan abunda ya faru "Futa fa muka yi na bata Maamah, ba wani babban abu bane" khayri tayi iya kokarin ta dan ta nunawa Maamah abunda ya faru ba wani babban abu bane.

"Kun dore mun kai fa. Ya abunda kike fadi mun daban da wanda shi ya fadin mun. Yanzu cikin ku wa ke mun karya?". Shuru khayri tayi bata ce komi ba Maamah ta cigaba "Da ki fada mun abunda ya faru gara kin mun qarya koh khayri, sabida Kabeer koh?". Maamah ta fadi playing with khayri's emotion amma duk da haka Khayri tace mata ba wani serious abu ya faru tsakanin su ba.

"Shikenan. Zan aiko mommy tazo ta ji mun koh ma menene, in ta kama koh ni da kaina sai nazo wallahi na koya muku hankali duka" masifa Maamah ta cigaba kan yadda suke ta mata wasa da hankali, khayri kam sai aikin bata haquri tayi ta yi har suka yi sallama suka ije waya. Su Baffah khayri ta kira dan taji ya suke, sosai suka yi murnar ji daga gare ta itama sosai taji ta sama kwanciyar hankali da tayi magana da su.

Yammacin ranar kuwa sai ga mommy tazo gidan ita daya. Luckily throughout ranar Kabeer na gida ba inda yaje, khayri kuma tana dakin ta zaune. Zuwa yayi ya mata knocking tare da fadin mata cewa mommy ce tazo, baa jima ba yaji ya buda qofar ta futo koh kallon fuskar sa bata yi ba ta wuce living room suka gaisa da mommy. Kitchen ta wuce dan hado ma mommy coffee kamar yadda ta buqata, shima tambayar sa tayi me zai sha kan ta wuce ta dawo tayi setting musu mugs biyu na coffee da box na cookies a gabansu ta dawo ta zauna.

"Rumaisa tace fada kuke, hakane?". Mommy ta fadi cikin muryar ta me sanyi, idanun ta kansu.

"Eh" inji Kabeer. Khayri kuma ansawa tayi da "aah". Dariya mommy tayi kan tace yanzu wa ke karya cikin su. Juyawa Kabeer yayi ya kalle ta ita kuma ta dauke kanta daga direction dinsa.

"Toh me ya hada fadan?". Nan dukan su suka yi shuru ba wanda ya ce komi. Kabeer yana tunanin ta ya zai fara ma mommy bayanin abunda ya faru. Khayri kuma tana nauyin ta fadin mata abunda ya faru, kuma in ma zata fara fadin mata tun daga ina zata fara bata labarin irin abubuwan da dan su ke ta mata?.

"Allah ya shirya mana ku toh" ta fadi kan ta fara musu nasiha akan haquri da juna. Sun fi one hour suna shan lecture daga gun mommy kan ta miqe tace zata wuce "Dan ana fadan ne aka qi zuwa barbecue dina jiya?". Mommy ta tambaya.

'Your barbecue started this whole mess' Kabeer ya fadi a zuciya dan da basu futa siyan gift inda zasu kai gidan mommy ba, da duk rigimar nan be faru ba. Iya qofa khayri ta tsaya da rakiya shikam Kabeer har bakin mota ya raka ta. Koh da suka isa motar ta fada ta sake ije shi tana masa.

SANADIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora