Koh da ya koma gefen su, straight ya nufi master bedroom dinsu inda nan Khayri ke zama dan ya duba ta. Tun daga qofar da ta bari a bude yike hango ta tsaye a gaban mirror da farar towel daure a jikinta, ta futo wanka tana shiri. Murmushi yayi, ganinta cikin gidansu brightening his mood. Finally the house had felt like a home to him, Khayrin sa ta dawo and he was going to make things right with her.Khayri da ke tsaye gaban mirror tana ta shirin ta koh kadan bata ji shigowar Kabeer ba, sai hannaye kawaii da taji an rungume ta. Wani irin sound tayi making kan tace "Subhanallah".
"Tsoro kika ji? It's just me". Ya fadi, closing all gaps between them. Kan sa ya kwantar a shoulder din ta, if only time would stop and trap them in that moment. Khayri kam rufe idanun ta tayi ta ja wani irin dogon numfashi, tana jin zuciyar ta na nema bata wata sabuwar labari na daban.
'You can't forgive him. He doesn't deserve it'. Ta fadi a zuci.
Shi kam Kabeer be sake ta ba. Hannunsa da ke wrapped round kirjin ta ya kai zuwa kan cikin ta. "Why's your abdomen swoll...". Be gama mata tambayar ba maganar da Adda Manga ta yi ya fara dawowa masa.
"Allah sarki baiwar Allah. Cikin nan har yanzu be daina wahalar da ita ba".
Abunda Adda ke nufi kenan da tayi maganan yayi tunanin koh nufinta khayri na fama daga ciwon ciki ne? Dama ciki khayri be sani ba?. Sakin ta yayi kan ya sa hannaye biyu ya juyo da ita to face him. Qarara ya ga dan bump dinta da ya fara futowa.
Gasping Kabeer yayi kan yace "Khayri is that what I'm thinking it is?". Khayri bata ansa shi ba kan ta a qasa, koh hada ido da shi ta kasa "Ciki kike da shi?". Still bata ansa shi ba hasalima ma sai wucewa da tayi da ta sama space din wucewan bayan ya dan matsa baya.
"Da ke nike magana fa" ya fadi "Where are you going?". Ya tambaya following her into the closet. Dube dube ta shiga yi har ta sama kayan barcin da take nema. Hannu ya sake sawa ya juyo da ita yana fadin "I am talking to you!".
"Ina jin ka ai ba kurma bace ni". Khayri ta maida masa, her tone matching his.
"Why am I just knowing of this?" Ya tambaya, abun koh kadan be basa dariya ba "Everyone's aware sai ni koh? Dan ban isa ba khayri. Koh ban kai ki fada mun ba. Which one is it". Shuru Khayri tayi tana ta harkokin gaban ta, koh kallo be ishe ta ba bare kuma ta tanka shi.
"Answer me!". Ya fadi da tsawa.
"Dan Allah ka futa" ta fadi muryar ta qasa qasa "In ihu zaka mun a kai ka futa. Barci nike so nayi". Kabeer ji yayi kamar khayri ta kai masa wani irin wawan mari. Wai yau shi take gayawa ya futan mata daga daki? Yana damun ta?. Be ce komi ba ya juya ya wuce ran sa gaba daya a dagule. Bin bayan sa tayi yana futa ta saka lock a qofar ta dawo ta zauna gefen gado, hannayen ta akan cinyar ta sai rawa suke yi. Hawayen da bata so yi a gaban sa ba suka fara zubowa. Kabeer ya gama dagula mata rayuwa, she wasn't going to let him mess with the remaining sanity she had. What did the baby mean to him after all, ba wai ya damu da ita bane bare abunda ke cikin nata. He was planning to leave them for another woman in just a few month's time.
Shikam Kabeer living room ya koma ya dinga juye juye, ya rasa abunda zai yi. Khayri was pregnant, she was going to have his baby and she didn't think it was important to let him know. Kowa ya san da labarin cikin kenan sai shi? Wannan tunanin ya sa ya dau key ya wuce gidan Maamah dan yaji dalilin su na boye cikin from him.
Tun daga yadda ya shigo cikin gidan Maamah ta san ransa a dagule yike. Riqo hannun sa tayi suka zauna kujera daya kan tace "Habibi na. Wa ya taba mun kai?". Kabeer ya dan dau lokaci kan yayi magana.
"Khayri is pregnant. Kin san da haka Maamah?".
"Ohh dalilin haushin kenan?". Maamah ta tambaya dan dama ta dade tana suspecting cewar Khayri bata sanar da Kabeer maganar cikin ba.
ESTÁS LEYENDO
SANADI
Ficción GeneralThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...