Qaran buda qofar da taji ya sa ta farka a firgice. Salati tayi tana murza idanunta shikam Kabeer koh lura da ita be yi ba ya wuce yina tangal tangal. Ita dai Khayri bin sa kawai tayi da idanu tana mamakin irin wannan hali na sa, she didn't need anyone to tell her cewar Ya Kabeer a buge ya dawo gida. Dan runtse idanunta tayi ta ja dogon numfashi tana addu'a a cikin zuciyar ta dan yanzu sosai take ganin wautar da ta tafka da ta amince da auran Ya Kabeer amma ya zata yi? After the deed had already been done.
Khayri ta jima zaune living room din in banda tunani ba abunda take yi ga wani growling da cikinta ke ta yi saboda yunwar da ke damunta. Silently tayi ta zubda hawaye tana tausayin kanta da kuma nazarin yadda rayuwar ta zata kasance tare da Ya Kabeer. Sai da barci ya dan fara cin karfinta tukun tayi na annabawa ta miqe ta shiga bedroom din. Samu tayi har ya kwanta yana ta sharban barcin sa abunsa dan haka ba tare da ta cire hijaab inda ke jikinta ba ta kwanta ta matse kanta a gefe. Kamar a mafarki Khayri taji ta tib! a qasa cikin dare. Koh da ta juya ta samu Kabeer ne ya saka qafafun sa ya ture ta qasa.
"Ke har kin isa ki kwana gado daya dani" ya fadi yana gallo mata wani murderous look "Jaka kawai". Ya fadi kan ya juya ya kwanta ya ja bargo ya rufa kansa ya cigaba da barcin sa. Khayri kam kanta ta dora kan cinyoyinta ta fashe da kuka mara sauti. Wannan wana irin wulakanci da cin fuska Ya Kabeer ke mata haka ne, me tayi masa da ya tsane ta haka. Da ya san baya son ta tun farko ai da be amince da auran ta ba. Ta fi one hour tana kuka har ta haqura ta rarrashi kanta ta kwanta nan qasa inda ya tura ta kan cold tiles ga A.C ya kunna dakin ya dau sanyi sosai. Koh pillow babu ta kwanta a takure har barci ya sake awon gaba da ita. Sosai barcin khayri yayi nauyi dan bata farka ba sai around past 8 na safe, a lokacin har Ya Kabeer ya gama shiri ya futa abunsa. Da sauri sauri ta fada bathroom tayi alwala tazo ta gabatar da sallah, gabobin ta duk ba inda be mata zafi da zazzabi zazzabi da take ji coupled with the fact that rabon ta da abinci tun a Kano. Kukan da ta ci the previous night ta sake ci zaune kan sallaya tana gabatar da addu'o'i Allah ya kawo mata mafita. Ta dade a kan sallaya kan ta miqe taje tayi wanka. Living room ta dawo ta zauna ta kunna kayan kallo. Kayan da Ya Kabeer ya ci abinci ta ci karo da su sai taji wani irin takaici ya kamata. Wai wana irin mutum ne ta aura? Shi Ya Kabeer wa na irin azzalumi ne, ya iya ciyar da kansa amma ita kwata kwata koh tunanin ta be yi ba bayan ya san cewa ita ba sanin kowa tayi a Lagos ba, ba kuma kudin da zata siya abinci gare ta ba.
'Toh koh ma kina da kudin kin san inda ake sayarwa ne?'. Wata murya ta fadi cikin zuciyar ta.
Yan dankalin turawa kwara shiddan da ya rage a plate Khayri ta kalla hungrily tana tunanin cin su amma kuma ta san ba wani qosar da ita zasu yi ba and moreover tana tsoron taba duk wani abu da ya danganci Ya Kabeer saboda gudun rashin mutuncin sa. Salati tayi a hankula kan ta wuce ta zubo ruwa daga water dispenser ta zauna koh concentrating akan abunda take kallo ta kasa saboda tsananin yunwa. Ba a jima ba room service suka shigo gyaran suite din, shuru khayri ta zauna tana ta kallon yadda sukayi ta aiwatar da aikinsu, tana kallo bayan sun gama gyaran suka kwashe kwanukan da Ya Kabeer ya ci abinci. Kadan ya rage hawaye su zubo mata tana dana sanin rashin cin dankalin da ya rage, gashi yanzu an tafi da kayan.
Ranar yini Khayri tayi tana kuka, tayi ta huta ta cigaba har ta haqura daga baya. Zuwa lokacin da tayi sallar Isha, she was so weak koh miqewa bata iya yi da kyau sai taji jiri na neman deban ta dan haka ta dauko throw pillow daya daga living room ta kawo ta ije sannan ta shimfida zanin sallar ta kan sallaya dan ya rage mata sanyin tiles. Kwanciya tayi ta lulluba da qaton hijaab dinta. Ba wai dan tana jin barci ta kwanta ba sai dan zafin da jikin ta da kuma cikin ta suka yi. Sai wuraren goman dare barci ya dauke ta finally dan haka bata ma san lokacin da Ya Kabeer ya shigo ba.
Shikam Kabeer be san meyasa ba da ya ga Khayri sai yaji gaba daya mood dinsa ya sanja yana jin wani haushi hakan ya sa da ya shugo ya kalla inda ta ke kwance a takure ya take mata qafa ya wuce abunsa kamar be san abunda yayi ba. Taka ta da yayi ya sa ta farkawa, koh da ta gan shi ne bata ce komi ba ta maida kanta kan pillow ta kwanta shuru trying so hard to suppress her tears. Ta farka sanda aka kira sallan asubah amma sai dai taji bazata iya miqewa ta kai kanta bathroom dan gabatar da alwala ba. Tana kallo ya wuce ta ya shige bathroom yayi alwala ya futo yayi sallansa kan ya koma ya kwanta ya cigaba da barcin sa. Khayri kam sai around to six Allah ya bata ikon zuwa bathroom a daddafe tayi alwala tazo tayi sallah da kyar. Ranar ma fita yayi just like the previous day ya bar ta ita daya tana kwance kamar marainiya duk ta zama abun tausayi da ita. Da kyar ta iya miqewa ta nannade shimfidar kwanciyar ta ta dora kan box dinta kan taje tayi wanka da kyar ta shirya ta dawo ta zauna a living room. Kabeer ranar ana idda sallan la'asar ya koma hotel din ya same ta zaune kan kujera ta dora kanta a arm na chair din. Kallo daya yayi mata ya dauke kansa ya wuce ciki ita kam Khayri bata ce masa komi ba dan koh magana bata wani iya yi. Wanka ya shiga yayi ya futo yayi shirin sa fes-fes sai kamshin turare yike. Wucewa yayi ya sama Khayri zaune kamar yadda ya tarar da ita a lokacin da ya shigo.
YOU ARE READING
SANADI
General FictionThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...