Babi Na Hamsin Da Takwas (58)

707 118 34
                                        


London, England.

"Anya kuwa kana kyautata mata kuwa Kabeer". Tun kan Kabeer ya bata ansa Maamah ta qara jefo masa wata tambayar "Ya zaa ce yau kwanan ta kusan goma da zuwa amma kullum na kira baku tare eh, harda yau weekend? Wana irin zama kuke yi ne?". Excuses Kabeer ya fara bawa Maamah akan lately he's been very busy.

"Kuma har yanzu Maamah bata gama adjusting to change din ba. She's mostly sleeping". Uhmm kawai Maamah ta fadi ba wai dan ta gamsu da bayanan da yayi ta mata ba.

"Toh yau dai ka tabbata ka hada ni da ita. Koh barci take in na kira ka tashe ta inyi magana da ita". Toh kawai yace yana shirin sallama Maamah ta katse shi "Ai ban gama ba malaman". Dan rolling idanu Kabeer yayi, shi duk Maamah tana neman takura masa takan wata khayri wadda zuwanta da rashin sa duk daya suke a wurin sa.

"Ka saman mata layi yadda zata dinga kiran gida sannan ka dinga kokari kana zama da ita kana dan futa da ita ta gan gari yadda zata saba kaji? Ba abu ne me sauki mutum ya bar qasar sa ba inda ya saba ya koma wata qasa inda al'adu da kuma yanayin rayuwar su kwata kwata sun banbanta da namu. Ga kuma kadaici, baiwar Allah. Kayi kokari ka kai ta gidan mommy su saba". Toh Kabeer ya dinga fadi mata da dan occasional In Shaa Allah duk dai dan Maamah ta rabu da shi. Sai da ta gama masa bayanin yadda suka yo planning din cigaba da karatun khayri da sukayi kan tayi sallama da shi ta ije waya.

Ranar tun da rana Kabeer ya koma gida. Kan ya koma kam sai da ya siyo mata layin waya tukunna. Koh da ya shigo shuru yaji gidan kasancewar ranar ba ranar aikin Mrs Lee bane. Har cikin bedroom ya shiga ya duba ta be same ta can ba ya wuce kitchen dan shan ruwa.

Mamaki ya cika khayri da taji motsin mutum a kitchen. Ta san kuma ba kowa bane face Ya Kabeer tunda he's the only other person that lives in the house sai dai bata saba ganinsa da rana ba. Hasalima dai tun ranar da ta iso ya dauko ta daga airport bata qara sa shi a cikin idon ta ba. Miqewa tayi ta shiga cikin kitchen din ta same shi yana shan ruwa. Sai da taji cikin ta ya wani kada sabida wani kyau da Ya Kabeer ya qara mata, dan gudun bata masa rai ta dauke idanunta daga gareshi. Sunkuyar da kai tayi kan ta gaida shi.

"Uhm" kawai yace mata. Hakan be mata ciwo ba dan zuwa lokacin ta saba da irin wannan attitude din nasa. Wucewa tayi living room ta zauna shuru ya shigo ya same ta. "Je ki dauko wayar ki". Ya fadi kan ya zauna ita kuma ta miqe taje tayi kamar yadda ya ce. Tana kawowa ya buda baya ya cira tsohon sim dinta ya miqa mata tare da ce mata ta adana a inda bazai bata ba. Sabon da ya siyo ya saka mata kan ya kunna wayar. Wayar na kunnuwa ya hau dannawa yana kokarin setting mata abubuwa kamar time zuwa na London. Yana gamawa yayi dialling number din Maamah, call din na fara ringing ya bata yace mata ta saka a kunne Maamah yike kira. Da Maamah ta ansa sosai tayi murnar jin muryar khayri sai dai ji tayi kamar akwai yar damuwa a muryar dan haka ta fara mata tambayoyi wanda duk khayrin ta kasa ansawa sabida Ya Kabeer da ke zaune kusa da ita, koh da ma ace baya kusa ita khayri bazata taba iya buda baki ta cewa Maamah gashi gashi yadda abubuwa suke tsakanin su ba.

"Kewan ku ne Maamah". Khayri ta fadi da Maamah ta kuma tambayar ta koh da abunda ke damunta ne. Kabeer da yake yi kamar hankalin sa be kan ta yana ankare da sanda ta kai hannu ta goge hawayen da ya fara sauko mata. Can ba da jimawa ba ta miqa masa waya cewar Maamah na son tayi magana da shi.

"Kaji tsoron Allah Kabeer ka tabbata ba abunda kakewa baiwar Allahn nan". Maamah ta kuma tambaya dan sosai taji tashin hankali. Bata so ace khayri taje can Kabeer yana quntata mata. Rantsuwa Kabeer ya fara mata akan cewa ba abunda yike mata, homesickness ne kawaii ke damun ta ba komi ba.

"Bata riga ta saba bane. Ki kwantar da hankali Maamah". Toh kawai Maamah tace kan tace masa ya maidawa Khayrin waya. Sallama Maamah tayi mata kan tace mata zata ba su Billie number din dan su dinga kira. Tana gamawa wayan ta wuce ta shige daki dan bazata iya zama tare da Ya Kabeer ba sabida gudun ta bata masa rai. Shima Kabeer din sama ya haye ya cigaba da zane zanen sa. Basu qara haduwa ba har sai bayan wasu kwanaki hudu zuwa biyar. Ranar jumu'ah ne khayri na zaune bayan Mrs Lee ta gama aikin ta ta wuce tana kallon tashar girke girke dan tana ta kokarin koyan irin kalolin abincin turawa dan ta san she won't rely on Mrs Lee forever, dole as soon as possible itama ta fara girki da kanta duk da tana dan kokarin yin yan abubuwan da ta iya masu saukin yi. Shikam Ya Kabeer dama clearly ya nuna mata cewar baya buqata ta dinga masa girki, duk abunda zata yi dama tayi daidai iya cin ta amma shi baya son abun ta. Ranar da ya fadi mata khayri har kuka tayi dan takaici. Wani irin aure ne wannan da mijinta baya zama gida da ita, baya raba daki da ita sannan kuma baya cin abincin ta. Ranar koh da ya dawo ya same ta zaune tana kallo gaida shi kawai tayi ta kauda kanta. Zuwa lokacin itama khayri ta koyi futa harkar sa, in ya wuce gaisuwa bata cika shiga sabgogin sa ba. Ansa mata yayi sama sama kamar yadda ya saba.

SANADILa tua prossima ossessione. Scoprilo ora