Babi Na Biyu (02).

2.4K 321 19
                                    

28TH AUGUST, 1994.
Katsina State.

Ana kammala Addu'ar kwana Bakwai na Bilkisu, Alhaji Dikko wanda mutan gidansa suke kira da Dattijo ya hau hanya tare da driver dinsa, basu tsaya ko ina ba sai a katsina, wata karamar kauye me suna Dutsen Safe, wadda take karkashin karamar hukumar Kaita. Suna isa gidan Malam Mansur kaita suka nema, kasancewar garin ba me girma ba yasa nan da nan suka sama wanda zai kai su gidan. Tun daga zauren gidan suka taradda mutane, da alama har zuwa wannan lokacin ana kai gaisuwar rashin ďa, Suruka da kuma jika da yayi. Gaisawa da mutan wajen Alhaji Dikko yayi wanda a ciki wasu suka gane koh shi wanene kasancewar sa sannanen mutum all thanks to his business empire me sunan Argon oil and gas, da kuma Argon mines banda kuma sauran business investments dinsa.

Matsowa yayi kusa da malam Mansur wanda ke zaune shuru maganar sa ciki ciki yike fitowa a sanadin kukan da ya sha cikin ýan kwanakin biyun nan. Gaisuwa ya fara masa muryar sa cike sa tausayawa bawan Allahn.

"Haquri zaka yi, haka Allah ya so. Nima dana zo tun a ranar in ba dan rashin surukata da nayi ba wadda ta rasa ranta gun haihuwa". Dattijo ya musu bayani. A nan kuma aka koma ana masa ta'aziyya shima. Ya dan jima yana zaune kan ya tambaya koh yana iya ganin marainiyar da aka bari. Ya dade yana riqe da ita a hannunsa, for no reason kawai yaji wani so da tausayin yarinyar na qara shiga ransa. Without thinking much about it ya buqaci da in ba matsala a basa khayri ya kula da ita amma sai malam Mansur yayi nuni da baza su iya hakan ba.

"A gaskia Alhaji, mahaifin wannan marainiyar Allah shi daya muka haifa gashi kuma mun rasa sa. yanzu ita daya ta rage mana. Baza mu iya bada ita ba. Gwamandi zata shiga wani hali". Yayi masa bayani. Dattijo yace ba komi. Da ya tashi tafia kudi masu tarin yawa ya bawa malam Mansur akan ya qara da Jarinsa dun khayri ta sama kulawa me kyau, sannan in akwai wata matsalar kar su taba yin kokonton neman sa.

"Allah ya raya ki Baiwar Allah". Dattijo ya fadi ita kuma ýar yarinyar tayi masa dariya kamar ta san abunda ya fadi. Har ya shiga mota zasu wuce sai kuma ya kuma leqo kai ya yi magana.

"Malam Mansur" ya kira cikin muryar sa me sanyi "Dan Allah a kula da ita, ban so tayi rashin komi, karka ji kunya a duk sanda kake da wata buqata ka nime ni nikuma na maka alkawarin zan taimaka maka indai be wuci karfi na ba". Ya fadi kan ya shige mota driver ya ja suka wuce ya bar mutanen cike da al-ajabin irin saukin kai da Allah yayi masa. Duk kudin sa yazo ya zauna cikinsu, irin abincin da suka ci aka basa shima ya ci, yayi sallah tare da su gashi kuma yanzu yana maganar kulla zumunci da su. Ina ma ace duk masu kudi haka suke.

.
☆☆☆☆☆
.

SEPTEMBER 21ST, 1994.
Kano State.

"Look, look what a cute baby you have there Rumaisa". Carlissa wadda ta matukar sabo da Rumaisa a zaman su na wata daya a Nigeria ta fadi. Zaune take kan wani kujera a cikin dakin asibitin taje wa Rumaisa wadda ta haihu a ranar Barka. A ranar da aka yi wata daya cur da rusuwar babbar kawarta kuma matar dan uwanta, Bilkisu. "Have you thought of a name?". Carlissa ta kuma tambayar ta.

"Yes". Ta ansa mata idanu cike da kwalla "Bilkis, she shall be called Bilkis". Ta fadi. Suna cikin haka sai ga Abubakar, mijin Rumaisa ya shigo tare da yaran, Zulaikha and Iliyas inclusive, kasancewar gidan da Taneem ya siya ba wani nisa da gidansu Rumaisa, hakan ya sa both families suka zama really close. Nan yaran suka fara rigima akan wanda zai riqe baby din first. Daga baya da aka kashe rigimar sai suka fara wata akan wanda tafi kama da a cikin brothers dinta.

SANADIWhere stories live. Discover now