Abuja, Nigeria.
Niima da yike da tunanin hoton da ta bari a drawing room din Abban ta ta kwana, gari na wayewa the following day bayan ta idda sallahn asubah can ta nufa dan dauko hoton. Shigan ta dakin ke da wuya taji muryar Umminta, koh kaiwa ga dauko hoton bata yi ba.
"Niima me kike yi nan da sassafe bayan gayi can ana neman ki a qarasa gyara. Oya oya futo mu wuce".
"Ina zuwa Umm....". Bata gama ba Ummi ta katse ta.
"Ban son jin komi Niima, wuce muje. Me zakiyi cikin nan da safe tsaka". Niima bata san meyasa ba kawai taji bata son Ummin ta ta san zancen hoton da ta gani jiya, wanda ya fado daga jakkar Khayri dan haka ta yiwa Ummi karyar cewa tazo duba wani hoton ta ne. "Shekara nawa hotunan nan suke nan Niima, wani irin kallo ne baki musu ba. Ban son fitina this early morning. Ki wuce in baki so raina ya baci". Ba musu Niima da bata da wani option illa na bin mahaifiyar ta ta wuce ta futa daga dakin. Sai dai kan ta kai bakin qofa Ummin ta na lure da ita. Tana noticing dinta har so uku tana juyawa tana kallon wani certain direction ta wajen din wani arm chair. Karimatu da ta gama sanin diyar nata da halayen ta tuni ta gane cewa Niima tana da wani ijiya ne cikin dakin, akwai abunda ta boye dan haka tana raka Niima zuwa dakin ta ta dawo drawing room din da sauri ta wuce direct zuwa direction inda taga diyarta nata kallo. Ganin abu tayi kamar takarda kamar kuma hoto, saboda a kife yike tana iya ganin rubutun da aka yi a baya but she can't make out the words. Duqawa tayi dan ta dau hoton sai dai kan ta kai qasa wayar ta da ke hannunta ta shiga ringing wanda hakan har sai da yayi startling dinta dan haka without paying much attention ta dauko hoton ta dora kan reading desk din Abdallah kan wasu presents da aka kawo ma Niima wanda ta bar su wajen.
"Toh gani zuwa". Ta fadi cikin wayar tayi hanyar futa daga dakin. Daidai bakin qofa ta hadu da me aiki "Dorothy there are some presents inside, take them to my daughters room and keep them with the other gifts". Ta fadi tayi wucewar ta. Ita kam me aiki tana shiga ta dau wrapped boxes din biyu tare da hoton da ke kai ta wuce da su straight zuwa dakin Niima ta hada da sauran tarin presents inda akayi ta kawo wa Niima tayi ficewar ta.
Ita dai Niima har aka yi mata gyara aka gama hankalin ta na can drawing room din Abban ta, bata san me ya sa taji tana matukar son ta qara ganin mutanen da ke cikin hoton ba dan haka tana gama wanka ta saka kayan ta sabbi ful ta wuce drawing room din sai dai kash! Ta duba ta duba kamar me amma bata ga hoton ba. Dole ta haqura ta wuce dakinta cike da takaici. Itama Karimatu tana gama uzurin da ya futar da ita daga drawing room din can take sake komawa dan duba hoton da ta daga amma koh da taje itama bata ga komi ba hakan ya sa ta kira Dorothy amma ita ma tace bata ga komi ba.
"Koh kin hada da kayan da nace ki kai dakin Niima ne?". Ta tambaya amma Dorothy tace sam babu wani hoto koh takarda kan kayan da ta dauka. Haqura tayi zuciyar ya na raya mata cewa ba wani important abu bane kuma bama lallai Niima din ce ta bar shi a wajen ba, it could be a mere coincidence. Dakin Niima din ta wuce ta gan ta an gama gyara ta shirya tsaf cikin wani super wax me green and red designs. Guda ta rangada kan ta fadi "Ma Shaa Allah".
"Amma ya na gan ki haka ina dan kunne?". Ta tambaye ta Niima din tace ai itace bata bata wanda zata saka ba dan haka Karimatu ta jawo hannun diyar nata zuwa personal sleeping chamber dinsu ta buda safe inda suke ije jeweleries and important documents. Wasu simple designs na gold earrings and pendants ta ciro ta cewa Niima tayi making choice a cikinsu. Wucewa tayi ta bar diyar nata nan dakinta. "Zabi sai ki maida sauran sannan ki zauna ki jirani. Ana nema na qasa, I'll be back in ten minutes". Ummi ta fadi tayi ficewar ta. It didn't take Niima long to make a decision dan haka ta dauki sauran boxes na jewelries din guda biyu ta maida su safe. Har ta maida zata juyo wani abu yayi catching attention dinta. Hoto ne tsoho da alama ya dade kuma yarinya ce qarama a hoton. Motsin qofa da taji yasa tayi saurin janyo hoton ta boye a jikinta ta koma ta zauna tana admiring jewelry set inda ta dauka.
DU LIEST GERADE
SANADI
Aktuelle LiteraturThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...