Another unedited chapter. I mostly type at night, by the time na gama barciiiiii sosai so I end up not editing. A cigaba da mun afuwa, in nace sai nayio editing zan iya wata ban yi update ba. I'll get round to editing the whole book some day soon In Shaa Allah. Thanks for reading, cheers!
*****************
Kano, Nigeria.
Wani dogon numfashi Sudais ya ja kan ya fara saukowa a hankula daga cikin jirgi. Karo na fari kenan da Sudais Aadam Abiso yike samun kansa cikin tension about meeting a lady. Be san kuma me sa Billie take sa shi jin haka ba. Ita koh Billie a nata gefen gaba daya ta mance da zuwan Sudais, tana zaune a daki tare da Mahra suna karatu sai kawai suka ji hayaniya a qasa. Koh da suka leqa ta window sai ganin shigowan motoci uku harabar gidan suka yi. Suna tsaye suna kallo Sudais ya sauko daga mota.
"Ya Allah" Billie ta fadi tana sakin wata iriyar ijiyar zuciya "He's so fine" ta sake fadi hakan ya sa Mahra sakin yar dariya. Ashe dama can kina so. Duka dariya suka yi kan Billie ta shiga dan mini panic cewar gaba daya ta mance da zuwanshi dan haka bata shirya komi ba na karbar shi. Tun kan Maamah ta aiko a kira ta ta wuce closet neman kayan da zata saka Mahra dai tana ta kallon ta tana mata tsiya.
"Barin je na duba koh Maamah tana buqatar taimako da wani abu". Mahra ta fadi kan ta fice da saurin ta ba tare da ta tsaya sauraron abunda Billie zata ce ba. Kitchen ta sama Maamah tana ba masu aiki orders ana kokarin hada tray din refreshments for Sudais and his entourage. Bakin gas Mahra ta wuce ta anshi tuyan su samosa daga hannun Maamah ta cigaba da yi ita kuma Maamah ta kama yin wani abun. Nan da nan aka hada komi aka kai ma baqi kan Maamah tace Mahra ta koma sama tayiwa Billie magana ta sauko. Surprisingly sai Maamah da ke ta having doubts akan Inno Marte ta ji Sudais ya kwanta mata sosai, nutsuwar shi da yadda yayi presenting kansa to them ya burge ta. Hira sosai Ahmad wanda yana gida tunda weekend ne suka shiga yi da Sudais har sai da Billie ta sauko tukun kowa ya tashi dan a basu wuri su samu su zan ta.
"Mu je kitchen ki soya mun nawa snacks din". Ahmad ya fadi yana jawo hannun Mahra, catching her unaware.
"Ka saki mun hannu kar Maamah ta gani". Mahra tace masa.
"In ta gani sai me? Yau ta saba ganin ina riqe miki hannu?". Murmushi tayi kan ta ce masa ai da da yanzu ba daya ba.
"Me ne ya sanja?" Ahmad ya tambaya with a mischievous grin. Share sa Mahra tayi ta jawo pan ta zuba mai a ciki ta dora kan wuta shikuma ya jawo stool ya zauna yana ta kallon ta tana kai da kawowa a cikin kitchen. Freezer ta wuce ta buda ta dauko pack din snacks ba tare da ta tambaye sa wanne yike so ba; ta riga ta san preference dinsa. Aikin ta ta shiga yi shikuma ya tsaya sai kallon yadda take komi nata a natse yike ta yi. Tana gamawa ta miqa masa plate din tace zata wuce ta duba koh Maamah na buqatar help with anything. Da saurin sa ya kamo ta yana fadin "Baki bani ansa na ba".
"Na mene?". Ta tambaya.
"Na ce menene ya sanja tsakanin mu?". Murmushi tayi tace masa ai itama bata sani ba shikuma Ahmad ya ce baya sakin ta sai ta fadin masa ita koh Mahra ta dage akan bata sani ba.
"Toh yaushe zan zo Dattijo ya aura mun ke ki zama nawa gaba daya".
"Ya Ahmad!" Ta fadi a kunyace "Ka rabu dani dan Allah".
"Sai kin ansa mun tambaya ta".
"Nima ban sani ba amma in ka ga Dattijo kana iya tambayar shi".
"Shikenan gobe zanje har gida na masa magana tunda haka ne". Yana fadin haka ya sake ta. Sakin ta da yayi yayi daidai da shigowar Maamah kitchen din. Already dama ta kama yan snippets of their conversation amma sai dakewa tayi kamar bata ji komi ba, sai da ta juya musu baya tayi yar murmushi. Ahmad kam plate din snacks dinsa ya daga ya miqe zai wuce Maamah tace masa "Sai da na shigo ka san zaka futa, munafuki kawai".
VOCÊ ESTÁ LENDO
SANADI
Ficção GeralThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...
