Babi Na Saba'in Da Daya (71)

690 136 27
                                    


London, England.

Email ya samu a wayar sa. Kuma koh da ya bude duk da babu suna, Bakhtiar ya riga ya san koh wacece sender din mail din. Contents din message din alone was enough for him to know the sender's identity.

Just watched your short press release. You think that's going to save you, seriously? Ka mance Inno Marte bata abu without proof ba. We're just getting started son-in-law dearest. Warmest regards to Ni'imatullah and the baby.

Ihu ne kawai be yi ba da ya gama karanta saqon. Wai me wannan matar ke so da shi ne? Shi ya zai yi da ita. In da a baya ne when he had nothing to lose, Bakhtiar would've fought her tooth and nail till the very end amma a yanzu he had so much to lose; he had Niima to lose, he had his son to lose. Major abubuwan that mattered to him kenan, he didn't care about his business empire, about his investors drawing out, about his name getting tarnished. The only thing that mattered to him was his family; Niima's trust, he had to restore it even if it meant offering truce to Inno Marte. With that resolve Bakhtiar ya fara typing mata reply. Daga baya dai sai ya fasa ya kirata directly kawai.

"I call truce" ya fadi directly ba tare da ya tsaya wata corner corner ba "Let's settle whatever this is privately".

Dariya me qara Inno ta saki "Bakhtiar kenan ka tuna sanda nace maka muyi solving abun nan like two adults? Ka tuna me ka ce?" Dariya ta kuma saki, abun ya na qara qonawa Bakhtiar rai.

"Lokacin so ya rufe maka ido koh? A nineteen year old had you in firm grip. You have incurred the wrath of Inno Marte, and you'll have to face the music Bakhtiar so keep your truce to yourself. Baka ga komi ba, I swear I will crush you to ashes" tana gama fadi ta kashe wayar Bakhtiar kam ya tsaya dazed gaba daya abun yi. Wara shigowar wani saqo cikin wayar sa ya kuma ji, yana budawa yaga daga ita ne.

I am very sure you will enjoy my next move. It will knock the breath out of you dearest son-in-law. Get ready, tomorrow at 07:00 CAT.

Khayri na kwance kiran Ya Ahmad ya shigo. Iya kokarin ta tayi to sound normal as possible, a tunanin ta Ya Ahmad din be da masaniya akan situation dinsu. Sai da suka gama gaisawa ya dan ja ta da wasa tukun yace ta tattaro hankalin ta ta basa akwai maganar da yike so suyi. Tambayar ta ya fara yi akan abunda ke faruwa, Khayri kawai taji bazata iya fadi ba dan haka ta fara nuna masa cewar things were okay between them.

"Ba sai kinyi mun qarya ba khayri. Kabeer ya riga ya fadin mun komi, shi ya ce na kiraki". Encouraging dinta Ahmad yayi kan ta fadin masa komi da ya faru kar ta ji tsoro koh kunya. A tsanake ta fara mayar masa da komi, tun tana iya riqe hawayen ta, har suka fara zuba tana narrating abunda ya faru tana zubda hawayen baqin ciki. Rarrashin ta Ya Ahmad yayi ta yi, yana bata kalamai masu dadi yana reassuring dinta.

"Yanzu kin san abunda nike so da ke ne?" Ya tambaya tace aah "Ki basa dama ku zauna ku tattauna".

"Ni dai gas....". Katse ta Ahmad yayi.

"Na taba roqar ki wani abu khayri?" Tace masa aah "Toh karki yi denying dina the first time I'm asking you for a favour. Na miki alkawarin in har kuka tattauna and still ba solution to problem din I'll honour whatever wish you have khayri. You're not alone, ina tare da ke ni zan tsaya miki In Shaa Allah". Toh tace masa kan ta masa godia shima godiyar yike mata yana sa mata albarka har suka ije waya.

Daren ranar khayri ta shirya ta futo, har girki ta yi dan su samu su zauna suyi sorting kan su out shikam Kabeer dama an zo an kira sa agent dinsa for an important meeting dan haka he had to leave the house. Har zuwa lokacin Zulaikha bata bar kiran sa ba tana tura masa messages na rarrashi sai dai daga baya she got infuriated again ta fara tura masa messages na cin mutunci. Haushi ya sa shima ya kirata ya caba mata maganganu, tana yi shima yina yi. Bacin ransa ya sa kan ya wuce gida ya tsaya a wani bar which was close to the gallery that presented him. Shiga yayi da niyyar having one quick drink just to cool off the steam. Feeling guilty yayi dan ya san ya ma khayri alkawarin zai daina kuma for the past weeks koh kallon kwalban giya Kabeer be yi ba bare ya sha amma ga shi all it took is a few minutes of exchanging words with Zulaikha to make him break his dry spell. Daga one drink Kabeer yayi ta ordering more har ya zama highly drunk dan da kyar ma ya iya driving kansa zuwa gida.

SANADIWhere stories live. Discover now