Babi Na Arba'in Da Bakwai (47).

661 130 27
                                        

Unedited chapter.

*********************

Kano, Nigeria.

Tun wannan rana kam khayri da Kabeer suka fara hide and seek, haduwa tsakaninsu sai ya zama dole amma koh da wasa basa bari su hadu, indai khayri ta san Ya Kabeer na wuri gudun wurin take shima haka Kabeer baya waiwayar inda take duk takan abunda ya faru.

Dattijo ne ya buqaci Kabeer da yaje yayi sallama da surukansa sannan ya kai khayri ta ga gida dan haka ana sauran four days ya wuce suka tafi dutsen safe. Sosai su Baffah suka yi murnan ganinsu. Shopping na azo a gani Kabeer ya yi musu da kuma yaje ya saki jiki dan zuwa wannan lokacin ya saba da Baffah Mansur, sosai suka sha hira ranar. Duk wanda wani dan uwa koh abokin arzikin su Malam Mansur kam sai da suka leqo suka gaisa da surukinsu shikuma Kabeer din ya dinga musu alkhairi dan kusan duk wanda ya gaisa da shi sai ya sa hannu a aljihu ya masa kyauta. Haka Inna itama ba karamin farin cikin ganin khayri tayi ba musamman yadda ta ganta ta qara kyau fiye da last time da suka ganta. Hakan ba karamin dadi yayiwa su Inna ba dan sun san ana treating diyarsu yadda ya kamata. Haka yan uwa da maqota da suke ta shigowa gaisawa da ita, duk wanda ya ganta sai yayi sha'awan ta ana ta sakawa iyalan Alhaji Muhammad Dikko albarka yadda suke riqon ta da zuciya daya. Sai yamma Kabeer ya kama hanyar Kano bayan yayi sallama da Khayri ya bar ta ita zatayi two days kan driver din gidan ya dawo ya dauke ta. Haka kuwa aka yi, ana gobe tafiyar Kabeer driver yazo da safe ya dauki khayri suka koma Kano.

Kashe gari tun da safe yan uwa suka fara shigowa sallama da Kabeer. Maamah tun safe ta taho gidan dan sallama da dan lelen ta. Ranar gaba daya family din aka taru gidan Dattijo dan yi masa sallama, Khalid da matar sa da yaran sa sunzo har wasu daga cikin yan uwan mahaifiyar su Kabeer da ke garin Kano sunzo dan su masa sallama, harma Zulaikha ranar tun safe tana gidan a cewar ta tare da ita zaa raka best friend dinta airport. Ita kam khayri tunda ta ganta ta rasa saqat gashi dama ranar ta tashi da mixed feelings ne, on one side tana murna da tafiyar Ya Kabeer, ta wani side din kuma bata so ya tafi tana ji kamar wani bari na jikin ta ne zai rabu da ita. Gaba daya ranar kasa gane kanta aka yi. Kasancewar flight din dare zai bi zuwa sanda aka yi sallar isha aka fara shirin kaisa airport lokacin yan zuwa masa sallama suka fara watsewa, ya rage daga su Maamah da Billie da Ahmad sai Zulaikha dan har Khalid da iyalin sa tafia gida suka yi shikuma dama uncle Sadiq kwata kwata baya qasar. Tunda taga an fara futar da luggages dinsa, khayri ta wuce cikin daki ta kwanta shuru ta rasa me ke mata dadi, sai kace ba ita ce just last week take ta murnan komawar sa ba take ta yin kirgen kwanakin da suka rage ya tafi ta samu ta sha iska.

Maamah da kanta ta biyo khayri har cikin dakin ta same ta tace mata bazata zo ta raka mijin ta ba. "Ki tashi ki shirya kar mu makara". Maamah ta fadi tana dan shafa kafadar ta dan tun safe take lura da khayri, ta san cewa separation anxiety ne ke damunta. Yar murmushi kawai Maamah tayi a zuci tana fadin 'zaki zo ki saba wataran'. Jiki ba karfi khayri ta miqe ta zura baqin abaya da veil dinsa ta futo. Motar Ahmad suka shiga ita da shi da Maamah da ta zauna a baya tare da khayri. Sai su Mahra da Billie suka shiga motar Zulaikha sai Dattijo da Adda Manga driver ya tuqa su. Tunda suka kama hanya basu tsaya koh ina ba sai Malam Aminu Kano international airport kuma basu bar airport din ba sai da aka fara boarding flights tukun. Bata yi tsammani ba Kabeer ya jawo ta into his arms for an embrace, bayan yayi releasing dinta ya manna mata kiss a saman goshin ta. "Take good  care of yourself" ya fadi mata softly into her ears. Hakan ba qaramin ciwo yayiwa Zulaikha ba. Zuciyar ta susa yayi ta mata yadda taga kwata kwata ma Kabeer din kamar be san sa kasancewar ta a wurin ba hannayen sa cikin na matarsa. Maamah ce ta matso kusa da Kabeer ta fara ja masa kunne ana gargadin sa akan aikata abunda be kamata ba.

"Ka kula mun da kanka kaji?". Ta fadi har zuwa lokacin hannunta be bar kunnen sa ba da ta kama gam.

"Ke sakin masa kunne kan ki cire masa". Adda Manga ta fadi duka aka kwashe da dariya. Wurinta Kabeer ya matsa ya zuquna to reach her, kwalla yaga ta fara zubarwa ya shiga rarrashin ta. "The last you left sai da kayi shekaru baka waiwayo mu ba, dan Allah Kabeer ka dinga zuwa gida kaji, kazo in dinga ganinka ina jin dadi". Hawayen ta ya share yana fadi mata zai dinga zuwa akai akai.

SANADIStories to obsess over. Discover now