Babi Na Ashirin Da Hudu (24).

882 143 9
                                    


Still not edited. Manage the short chapter 😁
.
*****************
.

Kano, Nigeria.

A hankula tayi sallama kan ta turo qofa ta shiga a hankula amma gani tayi dan karamin living room inda ke attached to Dattijo's bed chamber shuru ba kowa ciki amma kuma tana jin magana daga ciki dan haka ta matsa kusa da qofan bedroom din ta sake sallama.

"Come in my daughter". Ta ji muryar Dattijo.

A hankula ta buda qofan ta shiga gaban ta sai bugu yike ta yi. Sallama tayi kan ta shiga ta same su da Dattijon da Kabeer duka da mug a Hannu suna shan tea ga tray nan an jera different assortment of tea herbs da kwalban zuma da sauransu. Da fara'a Dattijo ya ansa Khayri yace itama taje ta dauko tea cup a cabinet tazo ta hada shayi amm Khayri sai cewa tayi a koshe take. Gyara zaman ta tayi tana satan kallon dakin. It was the first time tun zamanta gida da ta shiga bedchamber din Dattijo. Makeken daki ne wanda a tunanin Khayri girman sa zai kusa girman kaf gidansu can kauye. Tsakiyar dakin wani irin haddaden gado ne da Khayri bata taba ganin irin sa ba a rayuwar ta. Sai daga wani gefe vanity table ne wanda aka arranging skin care products iri iri da turaruka iri iri, da kuma rack din glasses, wrist watches and cufflinks. Komi arranged in an orderly way, sai daga gefe daya kuma, ta inda suke zama kenan an gyara sa ne kamar mini living room, couch ne dogo da zai iya daukan mutum biyu a gefe, facing qaton plasma TV inda ke manne jikin bango, by side na couch din kuma armchair ne sai wani rocking chair kuma sitting opposite to the other chair. A side stool din gefe ga board din chess nan ije a sama sai babban table inda ke tsakiyar mini living room an ije bowl na fruits sama. Can wani gefe kuma cabinet ne da cups and saucers and different varieties of teas, da su honey syrups and all. Komi a dakin ya hadu, da ka gani ka san ba karamin kudi aka zuba a dakin ba.

Tana zaune shuru tana sauraron hirar su Dattijo da kabeer, suna hirar kasuwanci wanda mostly sauraro kawai take ba wai tana wani gane hirar bane. Sosai Ya Kabeer ke bata mamaki in yana tare da Dattijo Koh other members din family din saboda yadda yike sakin fuska da kuma jikinsa da su bayan ita a duk lokacin da ya ganta tamkar ya ga malikul maut, duk ya bi ya bata fuska. Wato dai ita ce baya so.

"Malama Khayri" Dattijo ya kira sunanta "Khayrin Dattijo ce koh ta Baffah?". Ya cigaba da mata kamar yadda ya saba a kullum "Koh kuma ta Muhammad Kabeer ce yanzu koh?" Hakan ya sa ta jin kunya matuka. Kanta a qasa take murmushi bata dago ta kalle Dattijo ba. A haka yayi ta jan su da wasa kan daga karshe ya fara gabatar da agenda dinsa na kiran su.

"Na kira ku ne dama dan in sake tabbatar da komi, dan koh kadan bana situation inda zai taso ace na tauyewa wani cikin ku haqqinsa, tamkar jikar cikina na dauke ki Khayri kuma I want nothing but the best for you. Kai kuma Kabeer ina tabbatar maka da indai har Khayri itace zabin ka toh kayi sa'ar matar aure, she's from a very good background and wallahi your choice gladdens my heart alot. Zanyi farin ciki sosai inga mun hada ku aure. Dan haka har yanzu maganar ku na nan, babu wanda yayi sanjin ra'ayi cikinku?". Dattijo ya tambaya.

Kabeer ya ya dago ya kalla Khayri wadda itama shi take kallo, suna hada ido tayi saurin saukar da kanta qasa saboda tsananin kunya da kuma tsoron sa da take ji ga kuma zuciyar ta da ke raya mata cewa ta fadiwa Dattijo bazata iya auran Ya Kabeer ba dan kwata kwata bata tunanin akwai koh da digon kaunar ta a zuciyar sa. Dan runtse ido tayi zuciyar ta na bugu furiously kamar ya balla ribcage dinta ya fito.

"Ni...". Ta buda zaki tayi magana muryar Ya Kabeer ya katse ta.

"Ni Dattijo da so samu ne ayi auran nan as soon as possible, ina son ta kuma ina farincikin samun ta a matsayin matar aure na". Sosai kalaman Kabeer suka wa Dattijo dadi, dan har wani sanyi yaji ya ziyarci zuciyar sa. Sosai yike murmushi har sai da haqoransa suka fito, wushiryar sa ya bayyana. Dattijo be san me sa yike da having feeling cewa Khayri alkhairi ce a rayuwar Kabeer, ita zata ceto Kabeer daga hatsarin da ya riga ya jefa rayuwarsa, ita zata zamo silar shiryuwan Kabeer.

SANADIWhere stories live. Discover now