Bata ankara ba taji saukar mari me dan banzan zafi kan kumatun ta, kan brain dinta ya gama processing abunda ya faru ta sake jin saukan wani marin a dayan kumatun. Nan da nan idanun Khayri suka fara fidda ruwa, hannunta daya kan kumatun ta gaba daya ta mance da zancen wani lalle da ke hannunta. Ahmad ya matso kusa yana kokarin magana Kabeer ya galla masa wani irin harara gami da daga masa hannu alamar kar ya shiga cikin zancen."Dan Allah kayi haq....." Bata kai ga gama maganar ta ba Kabeer ya katse ta.
"Baki da hankali ne? Kinga yadda kika bata mun fuska da kayana" ya fadi yana duban farar shaddar sa wanda ya sha aiki duk a damalmale da lalle "Wai jakar ina ce ke?" Ya fadi ya fusace yana watsa mata wani kallo wanda ke dauke da matukar tsana ita kam tayi qasa da kanta tana zubda hawaye.
"Ballagaza kawai" ya fadi bayan ya miqe. "Kuma ki yi hanzarin wucewa dakina dama yanzu yanzu dinnan, ki jira ni a can. Wallahi wallahi in kika bari na riga isa dakin duk abunda na miki ke kika siya". Ya fadi, gaba daya haushin da yike ji a ranar zai sauke kan Khayri. Jin abunda ya fadi ya sa ta miqe da sauri ta fara hanzarin zuwa dakinsa.
"Haba Kabeer, what's this? Yaushe ka zama haka ne". Ahmad ya fadi. Ba tare da ya tsaya sauraron abunda Kabeer din zai fadi ba ya ruga a guje bayan Khayri wadda tafia take da sauri sauri zuwa hanyar dakin Kabeer. Hannunta kawai taji an kamo, koh da ta juya sai taga Ahmad ne.
Tun kan yayi wata magana ta tare sa "Dan Allah ka bari na tafi, kar ka qara mun laifi" ta fadi tana goge hawayen da ke ta faman zarya kan kumatun ta. Gashi fuskar yayi jazur ya kumbura abunka da farar fata. Ahmad yana shirin magana ta fusge hannunta ta ruga a guje sai dakin Kabeer.
Karo na farko kenan da ta shiga dakinsa wanda iya matuka ya hadu amma halin da take ciki na bacin rai da tashin hankali be ma bari ta tsaya duba kyaun dakin ba bare har ta yaba. Gefen guda ta samu ta tsaya. Tana jin ya budo kofar ya shigo tayi saurin rusunawa, kai a qasa ta qura kallonta kan persian rug inda yayi adorning a reasonable portion of the well tiled floor. Koh ta kanta be bi ba ya wuce hanyar bathroom dinsa. Wanka ya wuce yayi, kuma lokaci sosai ya dauka wajen wankar Kamar yadda ya saba. Ya fito daure da towel da wani towel din wrapped around his torso. Khayri har zuwa lokacin kan ta na qasa bata koh daga ta kallesa ba, a hankula hawayen ta na zuba kan cinyoyinta sai ji tayi ya watso mata kayan da ya cire.
"Ki tafi ki wanke shi tas, kuma da hannunki har sai gaba daya stain inda kika sa mun ya fita. In banga kayana Kamar yadda suke da ba wallahi sai kin gwammace kida da karatu". Ita dai bata ce komi ba ta miqe da kayan a hannu zatayi hanyar waje sai tsawa ya daka mata wanda sosai ya razana ta. "Ina zaki Kuma? Dallah wuce bayi na ki wanke shi. Salon na bari ki tafi da su ki ba masu aiki su wanke. Toh karyarki, mahaukaciya kawai". Ya ja tsaki ya koma closet neman kayan da zai sa ita kam Khayri koh da ta shiga bathroom din ta fi minti goma a tsaye ta rasa inda zata danna, gaba daya bayin sa daban yike da irin wanda ke dakin ta da dakin Mahra. Gashi tana tsoron tambayar sa, gashi lokaci na wucewa kuma Dattijo ya buqaci ganin kowa sannan kuma ta san kayan dole sai an dan jiqa su na dan wani lokaci.
Sosai hawayenta suka qaru dan gaba daya ta rasa abun yi. Ga dai bathtub nan babba wannan ta san wanka a shiga ciki a yi, ga kuma bidet nan ta gani na alwala, sai kuma can ta ga wani basin Kamar zaa iya wanki a nan sai dai kuma bata san yadda zatayi ba, koh inda zata danna ta sama ruwa bata sani ba dan haka kawai ta shiga the only place she thought she could operate a whole of bathroom din, wani dan cubicle ne haka. Koh da ta shiga, by mistake hannunta ya danna wani button. Bata ankara ba sai ji tayi ruwa ta shower din sama ya fara fitowa duk ya bi ya jiqa ta. Gaba daya ta rude ta rasa ina ma ta danna bare ta kashe ruwan, kankame kayansa da ke hannunta tayi kukan ta na qaruwa. Toh ita yanzu ya zata yi gashi ta jiqe shakaf gashi ruwan sosai yike saukowa kanta.Shikam Kabeer closet dinsa ya duba ya ciro wani grey coloured v-neck shirt da black shorts. Ya gama sa shorts din kenan yana combing kansa yaji noise sosai daga bathroom dinsa, Kamar ruwa na rushing. Da Kamar bazai duba ba sai kuma wani zuciyar ya raya masa da ya duba.
KAMU SEDANG MEMBACA
SANADI
Fiksi UmumThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...