I'm usually feeling too lazy to edit chapters after typing these days. Please ignore my mistakes kun ji🤗 you're welcomed to be my editor😁😁
***********************
.
Borno, Nigeria.
Kallon invite inda ke hannunta tayi wani haushi ya kamata. "You win Bakhtiar, you win". Ta fadi a fili "Amma nasarar ka na dan kankanin lokaci ne because I'm coming for you. I'll make sure I destroy you, I'll snatch everything and everyone you care about and by the time I'm done with you, sai ka gwammace mutuwa". Har ta yi shirin destroying invite din dan har ta dan fata squeezing dinsa a hannunta sai kuma wani idea ya zo mata.
Rufe idanunta tayi tana kada kai tare da wani murmushi na mugunta, a plan slowly forming in her head. Bakhtiar Arab ka haqa kabarin ka da kanka, wanda ya aike ka shiga sha'anin Inno Marte. So what if yana da advantage over her? So what in ya san sirrinta wanda babu wani mahaluki a duniya da ya sani? Ba abunda ke sa shi ganin ya fi karfin ta kenan ba? Toh Abunda Bakhtiar be sani ba shine Inno Marte tana nan riqe da babban weapon against him wanda strike daya zata yi ta tarwatsa rayuwar Bakhtiar Arab. And Abdallah El-Yaqoob, wato shi yana ganin ya sha da ita da ya hadata da Bakhtiar yayi exchanging yarinyar sa for a few billions, yayi hurting mata dan ta wanda tafi so fiye da kowa da kuma komi amma babu komi zata dawo kansa, when she's done with Bakhtiar Arab. Tana cikin saqe saqen ta Sudais yayi sallama ya shigo, daga ganin kayan jikinsa ka san daga gym yike. Kissing forehead din mahaifiyar sa yayi hakan ya sa ta dago daga duniyar tunanin da ta sha.
"What's that you're holding Inno?" Ya tambaya. "Let me see" ya sa hannu ya karba invite din daga hannunta. Karantawa yayi kan ya juya ya kalle ta.
"Ka tuna Bakhtiar Arab? Wanda ya kawo mun ziyara kwanaki?" Daga kai yayi alamar ya gane "Toh shi ke gayyatar mu bikin auransa".
"Allah kaimu, we're going" Sudais ya fadi.
"No we're not". Inno Marte ta basa ansa.
"Why not? Ni ina so naje, and besides na kwana biyu ban je Abuja ba". Kallon dan ta tayi dan ta san halin Sudais in ya kafe kan abu.
"Ka dai san wadda zai aura Koh?". Inno ta fadi. Murmushi yayi kan ya ansa ta "Inno I'm over that, dama ba rabona bace. Akwai mata da yawa a duniya, I'll find someone eventually". Sudais kenan, the ever good Sudais. Sai kace ba cikin Inno Marte ya fito ba dan shi kwata kwata babu koh digon mugunta a jininsa, yaro ne shi me tsananin shagwaba amma kuma me sanyin rai, da haquri, yarda da qaddara da kuma son mutane.
Murmushi kawai ta masa kan tace "Shikenan Sudais sai ka tafi kai daya, dama ina da Meeting ne a ranar shi sa nace baza muje ba". Ta san wannan card din will work on Sudais dan saboda soft heart dinsa zai ce he'll stay back with her amma ga mamakin ta sai ji tayi ya ce.
"It's okay, I'll represent you Mom". Ya miqe ya manna kiss ya wuce riqe da invite din a hannu.
Sudais be san me yasa ba tun ranar da ya ga Bakhtiar Arab kawai yaji mutumin ya kwanta masa a rai kuma yana son sanin sa sosai, ya san koh shi wanene, menene kuma alaqar sa da family din Abiso. Corridor inda aka yi arranging family pictures ya wuce, be tsaya ba sai da yazo kan hoton sister dinsa Suraiya Abisa ya dan tsaya. Kallon hoton yayi, cikin duk sisters dinsa ya fi kama da ita kuma duk da be san ta ba, he feels a strong connection to her. Kissing hoton yayi kan ya wuce dakin sa ya fada wanka.
Inno Marte ba haka ta so ba, bata son zuwan Sudais Abuja bikin Bakhtiar amma ba komi dan akwai sauran kwanaki, hopefully kan ranar zata yi convincing Sudais akan zuwan Abuja. Her son never disobeys her after all. Juice dinta ta dauka ta kwankwande kan ta miqe ta wuce office dinta dan fara aiwatar da plan din ta, she has to be careful cause everything has to be well planned. Things have to go accordingly kuma ta riga ta san who her first pawn in the game is going to be: Ni'imatullah El-Yaqoob.
VOUS LISEZ
SANADI
Fiction généraleThere are winds of destiny that blow when we least expect them. Sometimes they gust with the fury of a hurricane, sometimes they barely fan one's cheek. But the winds cannot be denied, bringing as they often do a future that is impossible to ignore...
