_________________📖 Tafiya yake a nutse cikin kwanciyar hankali kai baka ce yana cikin damuwa ba alhalin a lokacin inda za'a bincika zuciyar sa to fa sai an tadda ta tafi gawayi baƙi saboda baƙin cikin sharrin da akai masa.
Duk yadda ya tsani kallo yau dole ya haƙura ya kau da kai domin kuwa ya san sai an kalle shin dan yau yasan sharrin da akayi masa ke trending a garin nasu. Tuno da facemarks ɗin da ke cikin aljihun wandan sa yasa ya saki ajiyar zuciya kafin ya laluba ya ciro shi kana ya maƙala a fuskar sa.
Ta ƙofar baya ya fice daga gidan sarautar dan yasan ƴan jarida nacan cike a main ƙofar shikuma a halin da ake ciki bazai so yin magana dasu ba, bawai dan ba shida abun faɗar ba, a'a sai dan yin biyayya ga umarnin mahaifin sa.
Cikin takunsa na nutsuwa ya ƙarasa Save more Bank dake kusa da unguwar sarki wato unguwar su, ATM ɗin sa ya zaro wanda yake ɗan ajiye kuɗi aciki sa'i da lokaci dan lalura in ta taso, bai san nawa ne ainahin yawan kuɗin ciki ba shi dai kawai yana zubawa ne ashe zai masa amfani a rana irin ta yau.
Dubu Ashirin yai withdrawing kana ya tare ɗan acaɓa ya kai shi tasha sai dai in da matsalar take ba wasu garuruwa ya sani ba a ƙasar ta Hawarya dan kaso mafi yawa na rayuwar sa ba anan yayi ta ba.
Jin wani karen mota na ta maimaita sunan Garin Manya yasa kawai ya nufi motar dan haka kawai yaji sunan yayi masa kuma ya na san zuwa garin.
Kuɗin mota ya biya 10k dan Garin Manya yana arewacin ƙasar Hawarya ne yayin da Garin Giwa ke kudanci dan haka akwai tazara sosai tsakani.
Tafiyar kwana da wasu awanni ce ta kai su garin na Manya, garin da akewa kirari da "BABBA DA YARO KOWA DATTIJO NE, MANYA MASU HALIN MANYAN MUTANE DA MUTUNTAKA, HAWARYA IN BA MANYA KANGO CE!Sosai Yarima Saraki ke yawatawa da idanunsa kusufi kusufi ganin yadda Garin yake a cike, kowa se sana'ar sa yake ba ruwan kowa da kowa in ba neman arziƙi ne ya haɗa ba, masu dako, masu abinci , masu ruwa har ma da masu shayi duk acikin tashar.
Ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin ina zai nufa dan ba inda ya sani a wannan garin, hasalima bai taɓa jin ko sunan ba sai ko yau balle ayi batun zuwa.
Driver ɗin motar da ya sauke su ne ya ganshi har lokacin ya na tsaye yayin da duk ragowar fasinjoji sunyi nasu wuri, bai masa magana ba sai da ya gama ƙare masa kallo tare da nazartar sa kana ya matsa kusa dashi.
Sallama yai masa suka gaisa bayan ya amsa, nan yake tambayar sa ina zashi yayinda take Saraki ya amsa masa da baisan inda zashi ba bashi da kowa a garin arziƙi ya zo nema.Ƙare masa kallo driver ɗin yayi tun daga sama har ƙasa sai dai shi sam baiga alamar talauci ko wahala a jikin sa ba dan duk wahalar zaman motar da yasha bai hana sheƙi da ƙyallin da fatar sa keyi bayyana ba, sai dai banda haka ba wani kayane mai tsada a jikin sa ba, simple shirt and trousers ne wanda suka ɗan cukurkuɗe saboda zaman mota.
Gyaɗa kansa yayi bayan ya tabbatar wa da kansa insha Allah mutumin kirki ne dan sosai nutsuwa da hankali ke bayyana kansu a tattare dashi, wayar sa ya fito da ita daga aljihu tare da dialing number ƙanin sa ya Kira shi kan yazo yana neman sa.
Kallon Saraki yayi yana masa bayanin ga ƙanin sa nan zai zo ya rakashi inda zai sami wajen zama na haya in Yana so tare da ɗan aikin da baze gagara ba dan dillali ne shi amma na kasuwa.
Cikin yabawa da karamcin mutumin Yarima Saraki yai masa godiya.Cikin mintuna ƙalilan ƙanin driver ɗin ya ƙaraso, yaro ne matashi dan bai wuce sa'an Sarakin ba, gaisawa sukai kana ya'yansa yai masa bayani, cikin fara'a ya jagoranci Saraki zuwa jerin wasu shaguna dake bakin kasuwar durumi wadda itace babbar kasuwar garin, ya kawo shi nan ne dan yaji sauƙin fita neman kuɗin sa tun da yace arziƙi yazo nema.
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.