PAGE 2️⃣8️⃣

306 16 0
                                    

                           Page 2️⃣8️⃣






________________________📖 murmushi ya saki ganin yadda ta zama so speechless se kallon screen ɗin kawai da ta cigaba da yi kamar har lokacin vidion be ƙare ba bayan tuni ya ƙare dan It's a short video of 4 minutes.

Sake duban ta yayi daidai lokacin da hawayen da suka cika idanun ta suka shiga zubowa ba ƙaƙƙauta wa, wani irin yanayi ya tsinci kan sa a ciki na matsanancin tausayin ta, ya sani ita not easy abin da ya faru dan ze yi sanadin rufe kamfanin ne haka kuma ya ɓata wa ragowar Companies ɗin suna sedai be zaci zata ɗauki abin with much seriousness ɗin da har se kai ga zubar da hawaye ba abinda ze iya cewa so biyu kwai ya taɓa ganin kukan ta cikin tsawon zaman watanni da suka yi tare.

Girgiza mata kai ya shiga yi kafin ya miƙa mata handky ɗin sa, karɓa tayi ta damƙe cikin tafin hannun ta batare da ta share hawayen ba, cikin sanyin murya ya shiga lallashin ta da malamai masu taushi da daɗi gami da kwantar da hankali.

"Ba kuka ya kamata kiyi ba, kama ta yayi mu godewa Allah da ya bayyana mana abin da muke ta wahalar nema cikin duhu se gashi cikin lokaci ƙalilan ya haskaka mana komai gami da bayyana mana abin da muka jima muna nema, its not easy I know but you have to be brave so you can face your enemies da duk kind of sharrin da suke nufo ki dashi har ki sami damar tare wa da magance shi, wipe away those tears my dear, you're a brave lady so courageous kar ki basu dama ko ƙofar ganin gazawar ki, kar ki yadda su san weakness ɗin ki if not ni kaina se na miki dariya har da gwalo, raguwa kawai".

Hawayen ta shiga share wa da handky ɗin da ya bata tana murmushi ganin yadda yayi mata gwalo calling her Coward, ajiyar zuciya ya saki silently feeling relieved seeing her smile and knowing he's the reason behind the smile.

Gyaran murya yayi kafin ya soma mata bayani

"After tafiyan jami'an binciken can da suka sanar damu deadline ɗin da suka bamu na two days, am so confused seeing duk wata hanya da muke ganin zata ɓulle mana bata aiki, duk inda muka kamo zaren se ya tsinke, i just sat at that corridor frustrated not knowing what to do again se gashi cikin hukuncin Ubangiji while viewing the whole building something just came up to my mind, that old building, the garden and also the backyard, it just ring in my mind we haven't checked the CCTV's  their, muna can muna faman duba na wajen haɗa drinks ɗin da compound zuwa offices ɗin staffs bamu kawo wancan wajejen ba, then I decided in duba can in gani in zamu sami wani clue ko yaya ne, ban faɗa miki a lokacin ba dan kar in baki hope Kuma azo ba'a sami komai ba you'll be broken so I go ahead personally, at first na ɗan sha wahala dan ban sami komai ba a garden haka da backyard, gashi ban san kan old building ɗin ba wanda seda ƙyar na sami gane inda CCTV's ɗin wajen suke, and here it comes out the criminal da yake hiding their Yana commiting all his evil act, da na zurfafa bincike a kan sa se na gano he's a former employee a 'Cool mind drinks' , sedai iya bincikena na kaso gano who's his boss dan dole akwai someone da ya san sirrin Company ɗin nan da yake ɓuya a inuwar sa, sedai most importantly yanzu mu fara kai shi wa jami'an bincike, in muka fita daga case ɗin nan then we go further investigate his boss".

Kallon sa kawai take ba ko ƙiftawa har ya kai ƙarshen bayanin sa, tsananin farin cikin da take ji yasa ta faɗa kan shi kawai hugging him tightly dan haka kawai take jin zata yi ya hana ta kurma ihun murnar da take ƙoƙarin hana kan ta yi.

Runtse idon sa yayi da sauri cikin kiran sunayen Allah kafin da sauri ya miƙe tsaye ya ɗaga hannun sa da niyyar cire ta jikin sa se kuma ya fasa tun da ba muharramar sa bace da ke taɓa ta, abin dariya in me karatu yaga yadda yake kiran ta sake shi yayin da ita kam bata ma san yana yi ba dan tuni ta tafi tuannin hukuncin da zata sa ayi wa Emeka, seda ta gama murnar ta dan kan ta kafin ta sake shi tana koma wa seat ɗin ta ta zauna bakin ta a washe kamar me tallan MacLean

SARAKI (The Accused Prince) ✅Where stories live. Discover now