Page 5️⃣9️⃣
🔜🔜🔜🔜🔜
_________________________📖 Da ƙyar ta iya kai kanta ɗaki ta faɗa kan bed, wani irin numfarfashi kawai take sauke wa dan kukan ma ya gagara, irin zafin da take ji a ƙirjin ta gwara ma ta zafin ƙuna so dubu dashi, jujjuya kai kawai take dan bata san irin tunanin da zata fara ba.
A can wajen su Mami kuwa har seda Kisnah ta fice gaba ɗaya amma Saraki be iya ya daina kallon ƙofar ɗakin ba, kallon sa Mami take tana sake yardar ma kanta ba ƙaramin so ɗan nata ke wa matar sa ba sedai ba yadda zata yi itama ba'a son ranta zata shiga cikin rayuwar su ba sedai itama Laylah abar a tausayawa ce, tsawon shekara guda da rabi tana zaman jiran shi alhalin ba wai rasa masoya tayi ba kuma har zuwa yanzu tana da masu son ta ita dai ce kawai bata son su.
Gaba ɗaya hankalin sa yayi kanta cikin tuannin wane hali take ciki yanzu wanda tun Mami na jiran sa ko ze dawo hayyacin sa da kansa ta ga alamar hakan baze yiwu ba ta shiga kiran sa.
Da idanun sa da suka fara canja kala ya juyo ya dube ta kana ya sunkuyar da kai, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara magana cikin sigar alamun roƙo
"Kayi haƙuri Saraki, ba wai ina son shiga tsakanin ka da matar ka bane sedai na riga nayi alƙawari batare da Sanin hakan na iya faruwa ba, kuyi min haƙuri dan nasan ban yi daidai ba sedai dan Allah kar kace ba zaka auri yarinyar nan ba, itama kyakkyawa ce ko da bata kai matar ka ba kuma tana da tarbiyya har ma fiye da ita Sakeena......".
Tuni ta katse Mami jin zata kawo wani abu dangane da labarin Kisnah da ya bata
"Mami itama fa ba ita ta zaɓa wa kanta waccan rayuwar ba kuma ba wai ƴar iska bace, yanayin rayuwar ta ne kawai irin na turawa amma ba yadda kike tunani bane, ni na san ta sosai, above all bana tunani akwai wadda zata iya fin ta nutsuwa yanzu ko a ina kuwa dan kin shaida haka few minutes back".
Murmushi ta sake ganin yadda ko jiran yaji me zata ƙarasa cewa beyi ba ya tare ta dan ba matar sa kariya
"Am sorry Saraki na, nima ba wai wani abu nake nufi ba, yanzu that aside ka amsa zaka aure ta for your Mami's sake ko?".
Shiru yayi kafin ya gyaɗa mata kai zuciyar sa na masa nauyi dan ba wadda yake hangowa cikin ransa se Kisnah, ji yake kamar tana zaune ta ƙura masa ido taji me ze ce ne sedai bashi da wani zaɓi face na faranta wa mahaifiyar sa da kuma kare mutuncin ta
"Na yarda Mami dan bazan so duk abinda ze zubar miki da mutunci ba".
Ya furta can ƙasa yana jin kamar yaci amanar Kisnah ne dan yafi kowa sanin irin yadda take da kishi a kansa dan a kan haka ne suka yi faɗan da basu taɓa makamancin sa ba tun yana matsayin driver ɗin ta har ya zama mijin ta, duk albarkar da Mami ke sa masa be sa yaji yayi wa Kisnah adalci ba so har ya bar kilisar Mami ransa a jagule yake, ya daɗe tsaye a ƙofar flat ɗin su amma ya kasa shiga dan be san a wane yanayi ze same ta ba haka kuma be san me zata yi akai ba.
Masallaci ya wuce jin ana kiran sallar Azahar, ko da ya idar ya daɗe yana addu'ar Allah ya sassauta mata zafin kishin ta ya sa mata dangana a ranta, kamar wani ɓarawo haka ya shiga gidan da sanɗa, ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya kai ɗakin sa ya maida ƙofa ya rufe, wanka ya shiga yayi ya canja kayan jikin sa zuwa marasa nauyi na zaman gida kafin ya fito dan yunwa yake ji sedai cikin ransa yana gaya wa kansa yau kam baze samu Abinci ba dan shi da Mami sun yi laifi duk da ba'a san ransa bane.
Kayan abincin da ya hanga jere kan dining shi yasa jikin sa sake yin sanyi ya kasa jurewa ya wuce ɗakin ta, kwance ya same ta sanye da beautiful drop shouder jimmy choo top baki da white tite rimmed jeans da multi colour crown scarf, ringingine tayi kanta na kallon sama ta saka pillow ta danne fuskar ta, wani sabon tausayin ta ne ya tsirga masa ya shiga taka ƙafar sa kan haɗaɗɗen marbles ɗin dake malale a ɗakin har ya kai bakin gadon ya zauna, ɗan ranƙwafawa yayi kanta ya sa hannu ya cire pillown a tausashe, fuskar ta ya shiga bi da kallo most especially kumburarrun idanunta dake rufe, kallo ɗaya zaka musu kasan ba ƙaramin kuka tasha ba, a hankali ta fara buɗe idanun har ta buɗe su gaba ɗaya ta sauke a kansa, ɗan yamutsa fuska tayi jin kanta ya sara mata kafin ta miƙe zaune hakan ya kuma basu kusanci sosai dan yana rankwafen be ɗago ba.
ESTÁS LEYENDO
SARAKI (The Accused Prince) ✅
Ficción GeneralSarauta and all its hypocritical actions.