Page 5️⃣6️⃣
__________________________📖 A rikice kuma jiki na rawa take tafe tana duban duk hanyar da ta bi wajen komawa ɗakin ta sedai bata ga komai ba, kusan sawu uku tayi amma kamar ƙyallin ta bata gani ba.
Tunanin ta shiga yi where possible it could be kafin ta iya tuno lokacin da vase ya riƙo mata zani, hankali a tashe ta nufi hasashen Fadeela praying ba wanda ya gani balle ya ɗauka sedai ina ko da ta dudduba an riga an ɗauke.
Motsin matsar da vase ɗin da tayi yasa Jamal fitowa yana kallon ta fuskar sa a haɗe
"Lafiya?".
Seda ta ɗan haɗiye miyau kafin ta saki yaƙe
"A'a ba komai dama ina neman abina da na yar lokacin da nake gyaran falon ne".
Ƙure ta da ido Jamal ya yi yana sake haɗe fuskar sa fiye da farko
"Mene ne shi abun".
In Ina ta shiga yi cikin son Nemo abinda zata faɗa
"Am..ehmm...eh..dama..dama ɗan kunne na ne".
Kautar da kan shi yayi daga gare ta dan daga iya ƙinƙinar da take ya gane bata da gaskiya kuma ita ce me wancan na'urar
"Okay se bari kizo ki takura mana saboda ɗan kunnen ki ya ɓata kenan".
Da sauri tayi hanyar ƙofa tana bashi haƙuri dan ta gane nufin sa ta fice ta bar masa part ne, ko da ta fita kasa tsaye tayi ta kasa zaune cikin taraddadi, ba wai ɓatan na'urar ne matsala ba dan ko yanzu ta samu bayanan da take so haka kuma ta tura su a wayar ta, wanda ze tsinci abar ne matsala dan tasan duk wanda yake hulɗa da jama'a yana kallon abar yasan amfanin ta haka kuma fargabar ta kar a saurari abinda ke ciki balle har a cutar da ta Annabi ko a yi ƙoƙarin ɗauke su asabe daga unguwar da suke dan kar asirin wanda suka ƙulla sharrin ya tonu.
Jamal da ya biyo bayan ta dan rufe part ɗin ya hango yadda take ta kai da kawo alamun tashin hankali ya ƙara tabbatar wa da kansa ita ce me abar haka kuma bata da gaskiya ko kaɗan, yana kulle ƙofar ya koma ciki da son Sanin me ta naɗa da cikin na'urar da ya sa hankalin ta tashi haka, fatan sa ɗaya Allah yasa ba cutar dasu ta zo yi ba.
Laptop ɗin sa ya janyo yayi connecting ɗin ta da recorder ɗin kana ya fara bincikar recordings ɗin ciki wanda guda biyu ne kaɗai ya gani, na farko ya shiga inda farkon hirar ta da ta rasulu ce har wajen da take faɗar zata faɗa mata waye ya shirya sharrin nan gaba, se kuma ɗayan da address ɗin su asabe ne a ciki.
Tsam Jamal yayi bayan ya gama sauraren recording ɗin zuciyar shi tana bugawa da ƙarfi da ƙarfi, tunani ya shiga yi a ransa na wacece wannan matar, me ya kawo ta cikin masarauta har ta ke bincike kan Saraki, to ko dai ta sanshi ne?.
Wannan tunanin da yayi yasa ya miƙe da sauri har yana tuntuɓe ya maida jallabiyar sa da ya cire tare da kai duban sa kan Fadeela dake kwance tana bacci har lokacin dan ba ƙaramin gajiya ya tara mata ba daren jiya, na'urar ya ɗauka ya fice da sauri har ya kai bakin ƙofar part ɗin su se kuma ya canja shawara ya koma da baya, wanka yayi ya canja kaya kafin ya ɗaga waya ya kira jakadiyar Mami dan yaji ita ta kawo matar, tana ɗauka ya bata umarnin ta faɗawa me aikin Fadeela ta shirya tabi driver dake jiran ta cikin ash ɗin mota a ƙarƙashin bishiyar guava zasu musu siyayyar kayan abinci masu ya kusa ƙarewa.
Cikin ladabi jakadiyar ta amsa kafin ya kashe wayar sa ya fice da sauri zuwa motar da ya faɗa mata ya zauna jiran ƙarasowar ta, tun daga nesa ya hango ta tafe haka kuma yana hango tashin hankalin ɓatar na'urar da be bar fuskar ta ba har lokacin, tana ƙarasowa ta buɗe gidan baya ta shiga dan a tunanin ta driver ne kamar yadda jakadiyar ta ce mata sedai ko gama rufe motar bata yi ba sassanyan ƙamshin turaren sa ya kaiwa hancin ta ziyara, ɗan tsam tayi kamar me tuannin sedai ko kafin tayi magana tuni yaja motar hakan yasan ta ƙarasa rufe ta da sauri.
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.