Page 5️⃣7️⃣
_________________________📖 English wears ta siya a mall ɗin hotel ɗin da ta sauka tun farko dan har lokacin bata saki ɗakin ba, ta dai rufe shi amma tana cigaba da yin billing ana kuma gama Shari'ar su gimbiya Rumana ta koma, wani hadadden black jumpsuit na boujra jarrar,da small slide jackect dinshi da black veil nayin rolling, jaka da takalmin channel mai tsini sosai ta ɗaure a ƙafar ta, she look very beautiful and charming, so so takeaway.
A ranar gimbiya Haleematu ta taɓa ganin ainahin kamannin Kisnah ba wai Sakeena da suka sani ba a baya, sosai ta yaba da irin tsarin kyau da jiki irin na yarinyar, godiya kam tayi mata shi kamar ba zata daina ba tun Kisnahn na faɗin ta daina gode mata har tayi shiru.
Ƙarfe bakwai na safe motoci na alfarma suka kai su har airport dan ta jirgi zasu je, su biyar ne zasu je, ita, Jamal, waziri, Galadima, se Turaki, a yadda aka tsara ranar da zasu dawo za su sanar se a shirya tawagar jama'a da motocin da zasu tarbi Yarima Saraki a airport.
Wayar ta ta zaro daga jakan ta ta shiga typing masa message dan bata san kiran sa ta fi son ta ƙara sa ta ganshi ido da ido taji daddaɗar Muryar sa a fili
_*On my way home, in less than 2 hours insha Allah*_.
Tana ganin message ɗin ya tafi ta katse wayar gana ɗaya tare da lumshe ido ta kwantar da kanta jikin seat, yarima Jamal da yake kallon ta ta cikin madubin gaban mota ya sauke ajiyar zuciya cikin wasu irin tunanika da suke yawo a zuciyar sa.
He wish yayan sa ze auri this beauty goddess ɗin dan yasan they'll make a perfect match sedai sanin yayan shi da irin halin sa yasa ya bar abin a ransa amma Allah ya sani shi kam tana burge shi ba kaɗan ba kuma ze so ganin ta cikin family ɗin su.
Awa ɗaya da mintuna goma sha uku ya kawo su garin manya, jirgin su yayi landing safely a Manya state Airport, cab ta tare musu dan basu sanar da ko Sarkin garin shigowar su ba, alk they need and want a lokacin shine ganin ɗan su, ɗan uwan su and at the other side ita kuma mijin ta, shiyasa they all are dressed our traditional attire excluding rawani and alkyabba.
Tun da suka ɗau hanya Jamal ke ta bin garin da ido, a ganin farko zaka san garin babbar cibiya ce ta kasuwancin dan ko ina hada hada ce ke tashi haka kuma ba ruwan kowa da kowa.
Mota uku suka yi, Kisnah ita kaɗai da driver, Jamal da waziri, Galadima da turaki, yayinda motar su Kisnah ce kan gaba tunda ita ta san wajen, tafiya me ɗan tsayi suka yi ta at least 15 mins sannan suka ƙaraso gidan, tun da suka sauka wani sabon shauƙi ya mamaye ruhin ta na farin cikin ganin sa da zata yi at the same time ga farin cikin ya sami daidaito da iyayen sa, yanzu kuwa data ke hango gidan gani yake kamar me motar baya gudu dan se taga kamar ana sake jan gidan baya har take jin kamar ta ɓalle motar ta zura da gudu har se ta kai, at long last cabs ɗin suka yi parking a bakin ƙofar gidan, bata jira komai ba ta buɗe murfin motar ta fice da saurin da ya bawa Jamal mamaki, shima be iya ya jira su baba waziri ba ya bi bayan ta da sauri cikin zumuɗin sake son ganin yayan sa bayan kusan shekara biyu ba kaɗan.
Saraki kam tashin sa kenan a bacci ya ci karo da Sms ɗin da ta turo masa dan tun jiya yake jin sa cikin wani irin farin ciki da ya kasa gane na menene haka kuma ya samu baccin da ya daɗe be yi mai daɗin sa ba shine yar da makara dan se lokacin da agogo ya nuna ƙarfe takwas da mintina Ashirin ya farka, istigfar yayi ya maza ya gabatar da sallar asuba tare da ɗaukar wayar sa dan yin order breakfast shine fa ya ci karo da message ɗin ta, daskarewa yayi a wajen tsaye ya ma rasa me ze yi se kawai bin wayar hannun sa yake yi yana ƙifta idanu, ko kafin ya motsa har sun kai ga ƙarasowa.
Kiran sunan sa da Jamal yayi da ƙarfi yasa ya ɗago da sauri yana kai kallon shi bakin ƙofar da yaji Muryar, a maimakon ya sauke idon sa kan Jamal se idanun su suka sarƙe da na juna, wasu irin feelings da emotions ne ke ratsa kowannen su yana sa su jin kamar zasu shiɗe, ji suke zuciyoyin su na narkewa cikin wani ƙaton kogi yayinda wani abu me matuƙar zafi game da junan su ke ratsa jinin jiki da ran su.
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.