Page 1️⃣0️⃣
_____________________📖 "Hasbunallah wani'imal wakeel". Ya faɗa yana dafe kansa, shiru shagon yayi cikin jimamin tsaka me wuyar da ta same su lokaci ɗaya daga sama, dukkan su tagumi ne suka yi da hannu bibbiyu barin ma Alh Musa me shagon.
A hankali Alh Musa ya ɗan motsa kafin ya fara magana cikin muryar dake bayyana ainahin damuwar da yake ciki
"Wannan abu da ya faru damu rubutacciyar ƙaddara ce da bawa baze iya guje mata ba, na daɗe da sanin muna da magauta da mahassada cikin kasuwar nan kuma abokan sana'ar mu ne sedai ban ɗauka abin ze iya kaiwa har haka ba".
Numfashi yaja ya sauke a ɗame kafin ya cigaba cikin ƙarfin hali
"Ina me baku haƙuri domin nima ba haka naso ba sedai ba yadda muka iya da hukuncin Allah, ina me baƙin cikin sanar daku na sallame ku gaba ɗaya a yau, Allah ya baku wasu hanyoyin samu ya yiwa rayuwar ku albarka ya saka muku da alkhairi bisa zaman amanar da kuka yi dani da junan ku, duk wanda na ɓatawa a zaman mu ya yafe min dan ɗan adam ajizi ne, nikam baku taɓa min komai ba koma kun min na yafe muku duniya da lahira".Shiru duk sukayi wasu na sharar hawaye, ko a shekaran jiya basu taɓa kawo tunanin haka na iya faruwa dasu ba, sedai in akace kana da magauta da mahassada to fa se kariyar Allah kawai.
Abin da ya faru kuwa shine ragowar maƙota da wasu daga cikin abokan kasuwancin Alh Musa ne suka fara fito masa da hassadar su ƙarara dan sun daɗe suna ɓoye ta sedai zuwan Saraki yasa suka kasa riƙe kansu ganin yadda al'amura da kasuwancin Alh Musan suka ƙara bunƙasa, yasan suna masa hassada sedai be ɗauka zasu iya cutar dashi har haka ba, akwai kayan da yayi order Wanda in suka zo ana sa ran ba ƙaramin roba za'a samu ba shine suka yi masa shune custom suka kama kayan wanda bana ƙananan kuɗi bane, kusan dukkan jarin shi ya tattare dan babbar order ce se Gashi custom sun kama kayan a shekaran jiya da daddare, hankalin da ya tashi sedai bisa tunatar war me ɗakin sa yasa ya barwa Allah komai ya cigaba da addu'a dan ko yaran da be sanar dasu ba, a jiya ne kuma abokan kasuwancin nasa dake son ganin bayan shi suka tada ɓallin son ya biya su bashin da suke binsa na kayan da ya karɓa kamar yadda ƴan kasuwa ke yi in sun karɓi Kaya su biya rabi daga baya su cika, be ja da nisa ba ya haɗa ragowar kuɗin hannun da ya basu tare da sauran kayan da ba'a siyar ba, hakan yasa yau shagon ya tashi kusan ba komai a ciki se tsirarun takalman da basu wuce a irga ba, wannan shine dalilin sallamar su Saraki da yayi tun da ba kaya a shagon yana son kwashe ragowar kayan sa ya saki rumfar dan dama suna watan biyan kuɗin hayar sabuwar shekara da za'a shiga ne.
A sanyaye Saraki ya ɗago kansa dake sunkuya ya fara tausar megidan nasu da kawo masa hadisai da ayoyin da suka tabbatar da nasara ga duk wanda yayi haƙuri yayi tawakkali ya kuma Ubangiji yadda ya kama ta, wannan ne karo na farko ga duk wanda ke shagon da yaji Saraki yayi doguwar maganar da ta wuce sentence biyu zuwa uku, cike da kewa da tausayi Alh Musa sukai sallama bayan sun taya shi kwashe ragowar kayan sa zuwa gidan sa kowa ya nufi hanyar da ya fito.
Ya daɗe zaune a ɗaki yana tunanin da be san inda ze ɓulle masa ba ba'a kan komai ba se kan sana'ar da ze kama nan gaba se dai be san ta Ina ze Fara ba, ajiyar zuciya ya sauke bayan sunan Idris ya faɗo ransa, tabbas ya zama dole ya sanar dashi abinda ake ciki tunda shine yai masa hanyar zuwa shagon.
Without any hesitation yai dialing number Idris Wanda bugu daya ya ɗauka da sallama Muryar sa cike da farin cikin ganin yau Saraki ya kira shi duk da dama yakan kirashi sa'i da lokaci.
Gaisawa suka yi kafin a nutse Saraki yai masa bayanin halin da ake ciki zuwa zaman da yake ba abin yi, sosai Idris ya jinanta faruwar hakan ya kuma tabbatar masa da zeje yayi wa Alh Musan jaje kafin a ƙarshe ya ƙarƙare da insha Allah cikin satin nan za'a samowa Sarakin wani aikin.
Ajiye wayar Idris yayi a gefen sa kafin ya sanar da yayan sa da suke tattauna batun gyaran motar shi (drivern da ya tuƙo motar da saraki ya hau daga Giwa zuwa Manya) karayar arziƙin da ta sami tsohon maigidan sa Alh Musa, sosai yayan sa shima ya jimanta abin tare da Allah wadai da mahassada kafin ya dubi ƙanin nasa
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.