PAGE 9️⃣

308 13 0
                                    

                           Page 9️⃣




_______________________📖 Asibiti aka wuce dasu su duka dan ceto ran su musamman Surayya da tafi su jigata.
Kula sosai ake basu ganin ƴan sanda ne suka kawo su, dressing akayi wa baaba a kan sa tare da ƙafar sa dan bullet ɗin be shiga ƙafar ba yadai shafe ta ne.

Allurai kawai aka yiwa Kisnah da zasu taimaka mata dawowa hayyacin ta da wuri ban da wannan ita kam bata cikin kowane haɗari, Surayya ce dama dai ke cikin matsala kasancewar kwalbar ta shige ta sosai dan se da akayi mata aiki aka cire guntuwar kwalbar da ta karye mata a jiki sannan aka ɗinke wajen, aluran kariya aka yi mata kafin a maida ita ɗakin hutu.

Ta can ɓangaren kawu kuwa yana can yana baccin sa hankali kwance da tunanin koma ina Kisnah take zuwa yanzu an kirea mata warning ɗin da ze tsoratar da ita a kansa.

Tun farar asuba da ya farka ya dannawa gang ɗin nasa kira batare da ya ko duba lokaci ko gabatar da sallah ba da ake ta kira a manyan masallatan kusa da su, seda tayi ringing ta gama har so biyu basu ɗauka kafin ana uku su ɗauka, be ko amsa sallamar da suka yi masa ba ya fara tambayar su batun aikin sa.

"Acan muka kwana oga amma har zuwa ɗazu karfe huɗu bata fito ba kuma kasan ƙarfe uku ake rufe club ɗin, da alamu dai ta lura da muna binta to ta bi wani, hakan yasa dole muka haƙura muka koma maɓoyar mu dan ƴan sanda suna fitowa patrol, sedai a tara gaba".

Cikin wani tuƙuƙin takaici da ɓacin rai kawu ya kashe wayar, tsantsan disappointment na wanzuwa kan fuskar sa dan ba abin da ya tsammaci ji ba kenan daga gare su.

*************

A hankali a hankali ta fara buɗe idanun ta da take jin sun mata nauyi sosai, dishi dishi take gani dole ta sake maida idaun ta rufe kan ta sake buɗewa, a sannu a sannu har ganin ta ya daidaita ta fara ganin komai normal, ƙarewa ɗakin kallo take cikin tunanin me kuma ya kawo ta asibiti dan a cikakken kallo ɗaya da tayi wa  ɗakin ta tabbatar asibiti ne saboda gadajen dake jere a ɗakin, ƙarafan ƙarin ruwa da arin magani da ɗakin ke yi.

Da ƙyar ta iya miƙewa tsaye dan nauyi da ko ina na jikin ta yayi mata, canular ƙarin ruwan dake hannun ta ta fisge har jini na rushing daga inda aka saka allurar amma bata damu ba,  band ɗin kanta ta cisge ta ɗaure hannun dashi wanda hakan yasa doughnut ɗin da tayi wa gashin ta bajewa ya kwanta lamɓan a bayan ta.

Ƙafafunta ta zuro ƙasa da niyyar miƙewa sedai da sauri ta ɗauke cike da ƙyanƙyamin floor ɗin asibitin da yai jurwayen ƙura, hannu ta zura ta janyo takalman ta da bata san waye ya cire mata ba ta maida abin ta ƙafar ta sannan ta sauka, batare da tsayawa neman inda wani likita yake ko wanda ya kawo ta asibiti ba ta fice daga ɗakin, cikin Sa'a ba wanda ta haɗu dashi cikin ƴan sandan da suka kawo su ko likitan da ya karɓe su dan haka ta fice har bakin titin da ke gaban asibitin, napep ta tsayar ta shiga bayan ta faɗa masa inda ze Kaita, this is the first time of her being a motar haya kowace iri ce kuwa, kalle kalle take a titin har ta gane unguwar da take kafin ta sauke ajiyar zuciya.

Tun da ta shigo motar mayen ƙamshin ta da ya kama jikin ta ko da bata saka ba balle ta ƙara wani yake tashi yana cika masa hanci, lumshe idanun sa yayi dan Allah yayi shi mutum me matuƙar so da ƙaunar ƙamshi sedai nata yayi ƙarfi da yawa shiyasa yake tashi sosai dan ko daga nesa mutum ze iya jin sa.

Kamar kullum yau ma t-shirt and jeans ne a jikin sa sedai masu ɗan tsada ne dan duk kuɗin da yake samu a sallamar sa tarawa yake yana ƙara sutura dan mutum ne shi me son ƙyale ƙyale a jikin sa, kansa na ƙasa bakin sa na ɗan motsi hannun sa sanye da counter yana pressing alamar dai tasbih yake yi.

Tun zaman ta bata san akwai wani a cikin napep ɗin ba se da traffic ya tsaida su daidai gaban wani me ɗan kiosk a gefen titi, ƙishirwar da ta addabe ta yasa ta neman ruwan da zata sha hakan yasa cikin muryar ta da bata gama dawowa daidai ba tai wa me napep ɗin magana dan ba ko sisi a hannun ta

SARAKI (The Accused Prince) ✅Where stories live. Discover now