Page 4️⃣2️⃣
_________________________📖 Se da tayi kukan ta ya ishe ta kafin ta share hawayen ta shiga tunani har bacci ya kwashe ta bata sani ba.
Acan waje kuwa sosai suka zazzaga unguwar shi da dillalin gidan suna tafe suna hira yana ganin yadda komai na unguwar yake, kusan awa biyu suka yi kafin su yi nufin dawowa bayan sun gama shawarar sana'ar da ya kamata ya fara wato buɗe provision store dan daga layin su har zuwa layuka bibbiyu na gaba da bayan su babu me provision sedai ƴar treda na siyar da kayan yara irin su alwala biscuits da dai sauransu, amma ko awo zasu yi se sun sha tafiya kafin su kai provision ɗin dake layi na biyar a gaban su ga shi mutumin na da tsada shiyasa da yawa suka gwammace hawa machine su biya talatin zuwa kasuwar dake gaban unguwar.
Ƙarfe ɗaya saura ta farka daga baccin saboda sallama da ake ta doka mata a ƙofar ɗaki, se da ta ɗan zauna bakin katifa na sakanni dan gujewa jiri sannan ta tashi ta ƙara sa ƙofar ɗakin ta ja ƙofar baya dan dama tura ta kawai tayi bata rufe ba, tambaya tayi waye yaron ya amsa da sunan sa Habu, maman sa ce ta aiko shi, ɗaya labulen tayi ya ƙarasa cikin ɗakin ya ajiye mata kwano a rufe wai inji maman sa.
Godiya tace yayi mata kana ta koma ta saka hijab tare da ɗaukar brush da MacLean ta fita da biya ta ɗebi ruwa a buta, wanke baki tayi can baya da inda taga passage ɗin su yake dan ba zata a iya tsugunna wa a can ba, tana gama wa ta ɗau buta zata koma ɗaki se ga sauda ta fito
"Ah amarya kin tashi ashe ko da yake habu yace min shi ya tashe ki da sallamar sa".
"Aikuwa dai, barka da rana maman habu".
"Barka kadai amarya, ya kwanan baƙunta".
"Alhamdulillah, naga abu an gode Allah ya saka da alkhairi".
"Laah ba komai amarya, zaman taren kenan ai". Maman habu ta kamar yadda ta zaɓi kiran saudah ta amsa da ƴar dariya kan fuskar ta.
Bata kuma tsayawa wata maganar ba ta wuce ɗakin su dan hijab ɗin jikin ta ya dame ta, babba ne har yana ɗan jan ƙasa shiyasa se faman tattare shi take.
Tana shiga ta cire ta jefa shi kan katifa tana hararar sa kamar wanda yasan me take yi, kwanon abincin maman habu ta buɗe, shinkafa ce da miya sedai tun a ido sam abincin be yi wa Kisnah ko kyan gani ba balle tayi sha'awar ci, rufe wa tayi ta ajiye a can gefe kafin ta matsa wajen kayan abincin su ta fito da taliya dan fa jallof sphagetti take sha'awar ci, tun da is one of her favorites balle yanzu da aka daɗe ba'a haɗu ba.
Rashin kayan cefane ne yayi mata cikas, zama tayi cikin tunanin ya zata yi dan ba zata iya jira har se ya dawo ya kawo na wajen sa ba saboda yunwar da ta ke ji, wani tunani ne ya faɗo mata ta kuwa tashi da wuri ta ƙara sa wajen jakar sa ta buɗe cikin neman kayan da ya cire, hamadala tayi ganin kuɗin da ta ciro a aljihun sa da yawan su, ƙirgawa tayi sannan ta zari dubu ɗaya dan dubu shida ne se ta maida masa sauran wandon sa kana ta maida kayan jaka.
Hijab ɗin ta kuma maida wa ta fita wajen maman habu neman yaron da zata aika, Sultan yayan habu saudah tace ta aika dan yafi su hankali ze fi riƙe mata kuɗi da kyau.
Rubuta masa duk abinda ze siyo mata tayi a takarda ta bashi ya tafi, cikin mintuna ƙalilan kuwa ya dawo hannun sa riƙe da ledoji, sosai tayi mamakin yawan kayan da ya kawo dan ita ko da ta rubuta na ɗari bibbiyu ta zata za ta gan shi ɗan kaɗan can ƙasan leda ne ashe haka suke arha.
Ita kuwa naman habu da kallon mamaki ta bi ta ganin yadda ta siyo kaya masu uban yawa haka wai har na ɗari bibbiyu alhalin zata iya siyan komai a ɗari uku kuma ya wadace ta.
Karɓa tayi ta yiwa Sultan godiya tare da bashi ₦100 amma maman sa ta hana ta ce yayi yawa, da ƙyar ta bari ya karɓi hamsin tana mitar ai ko bata bashi kuɗi ba shi me yi mata aike ne, ba kaɗan ba taga mutuncin maman habu a lokacin dan a yadda mutane idon su ya buɗe da son kuɗi bata yi zaton akwai me hali irin nata ba.
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.