PAGE 4️⃣7️⃣

458 14 2
                                    

                          Page 4️⃣7️⃣











_______________________📖 Tsananin kishin da sa'adah taji tare da takaicin yarfa ta da yayi a lokacin baze misaltu ba, ƙarin takaicin ta yadda ya ɗauke ta kamar wata jaririya yana zura hannun sa cikin hijab ɗin ta, runtse ido tayi lokacin da ta hasaso hannun sa na shafa jikini Kisnah cike da sha'awa da muradi me girma, wani irin kuka ne ya kubce mata ta shige ɗakin yayar ta da gudu tana yin sa (sa kai😜😜).

A can ɗakin su kuwa suna shiga ya dire ta bayan ya gama juyi da ita, zaman wata uku da kwanaki da suka yi a garin nan ba ƙaramin shaƙuwa ce ta saka shiga tsakanin su ba haka kuma sosai yake jin ta yanzu a ranshi, duk da matsayin ƙanwa ya bata a zuciyar sa sedai ya tabbatar a cikin ƙannen ma ita ɗin ta musamman ce.

Tsananin kulawa da kyautatawar da take masa yasa ba ya son ganin ɓacin ranta ko yaya kuwa, duk yadda yake jin haushin fitar ta ba niqab haka ya haƙura ya daure lokacin da ta sanar masa ba zata iya ɗaura shi ba dan yana hana mata numfashi, a ko yaushe be da buri illa na ya kyautata mata yasa ta farin ciki kamar yadda take ƙoƙarin yi masa kullum.

Bashi da wata matsala da ita se abu a waje uku, yanayin shigar da take yi, yawan son shigewa jikin sa, salon murya da shagwaɓar da take masa, wannan sune matsala uku da yake fuskanta a zaman sa tare da ita dan sosai hakan ke sa shi cikin wani hali sedai ya kan kore duk wani tunani da hasashe daga ransa a duk lokacin da hakan ya bijiro masa tare da tunatar da kan sa ita ɗin ƙanwar sa ce, sedai ta riga tayi masa illa babba dan yanzu baya iya bacci se ya jita a jikin sa ɗan ta sanar masa da hakan, duk daren da zata kai wajen bitar karatu se ya jira ta komai baccin da yake ji kuwa dan ko ya kwanta baze iya barcin ba, haka kuma yawan rungumar da take masa yasa shima ya saba har be ɗauki hakan wani abu ba yanzu sedai yanayin da yake shiga ne ya kasa sabawa dashi, taste ɗin abincin ta kuwa ya daɗe da kama harshen sa dan daga kallo a ido ma yana iya banbance girkin ta da ba na ta ba, ƙamshin turaren ta kuwa ko cikin turaruka dubu za'a sashi se ya zaƙulo shi tsabar yadda hancin sa ke kwadayin ƙamshin a ko da yaushe.

"Sannu da zuwa Yaa, ya shagon?".

"Yauwa sannu my Keenah, shago lafiya lau alhamdulillah, hope kema kina lafiya".

"Lumi yaa nah, cire kayan muje kayi wanka". Ta faɗa tana taya shi da cire rigar jikin sa da take ta shaddah dark ash, lakace hancin ta yayi

"See you, muje kayi wanka kamar wani ɗan yaro ko ƙanin ki".

"Dan ma bance zan yi maka ba, muna nan da kai watarana da kai na zan maka dan ka dinga fita sosai".

Nauyin da maganar tayi masa ya sa yayi shiru tare da cigaba da rage kayan kawai, ya kan yi mamaki yadda maganganu irin haka basa yiwa harshen ta nauyi, so da yawa in ta furta se ta barshi da jin kunyar ita kam ko a jikin ta da bata nuna ta san ta faɗi wani kalma ko sentence da be dace ba balle ta ji kunya.

Bata kuma cewa komai ba har ya rage kayan jikin sa ya koma daga shi se boxers kafin ta miƙa masa jallabiyar wankan sa ya saka, tun yana kunyar cire kaya a gaban ta har ya sallama dan ita bata nuna wani damuwa a kan ganin sa da iya boxers, har ƙofar banɗakin ta raka shi da basket ɗin wankan a hannun ta, duk yadda yayi da ita ta koma ɗaki ƙi tayi a ranta tana ayyana bazata koma ɗaki sa'adah ta kuma tare shi ba, ko da ya fito jingine jikin ginin toilet ɗin ya same ta, be ce komai ba ya wuce ɗaki ta bishi sedai ya lura walwalar ta ba kamar ta ko yaushe ba ya gano she's just faking it amma be tambaya ba tukun ya bari ya gama shiryawa.

Ko a wajen cin abincin shi ya matsa mata taci cokali shida da ƙyar dan tun tuni yunwar ta kama kanta kamar yadda yake kasancewa duk in tana cikin damuwa, tunda ya ga haka ya kuma tabbatar da hasashen sa na akwai abun da yake damun ta dan shi kam be kawo batun sa'adah ba dan baya mata kallon me hankali se taɓaɓɓiya, ture abincin gaban su tayi gefe tare da kurɓar kunun ayar da ta haɗa sannan ya fuskance ta sosai

SARAKI (The Accused Prince) ✅Where stories live. Discover now