PAGE 3️⃣7️⃣

312 12 0
                                    

                          Page 3️⃣7️⃣






__________________________📖 England kawu ya shirya kai ta batare da shawara da kowa ba dan tuni ya babbake kan dukiyar ta dan yace bata da wanda ya fishi a lokacin kuma ba wai ta mallaki hankalin ta bane so ze kular mata da komai zuwa ta girma, ko sati da karɓar ragamar Companies ɗin be yi ba ya sauke Alh Sulaiman daga kan duk abinda yake jagoranta ya canja manajojin da ya ga dama.

Ana ya gobe ze kaita England Alh Sulaiman ya same shi har gida kan be dace ya kai yarinya ƙarama ba wata ƙasa ita kaɗai bayan bata da kowa a can, ƙasar da komai namu ya sha banban da nasu kama daga kan al'adu, addini zuwa wayewa sedai tuni kawu yasa ƙafa yayi fatali da maganganun Alh Sulaiman suka rabu baran baran bayan kawu yayi masa cin mutunci wanda wannan ne yasa Alh Sulaiman ɗin yin fushi be kuma magana ba akan duk abinda ya shafi Kisnah dan kawu ya faɗa masa ƴa dai tasa ce dan haka baya san shisshigi da kalan dangi.

Haka kawu ya kaita makaranta yayi mata registration ɗin komai ya danƙa ta hannun shugaban makarantar da sunan ze dinga turo masa kuɗin komai na buƙatar karatu amma bazata dawo gida ba har se ta gama karatun ta zuwa matakin ƙaramar secondary.

Haka kuwa akai kawu ya dawo gida manya ya bar Kisnah garin da bata da kowa a hannun baturen da be san Allah ba, kamar yadda yace bata dawo manya ba kuwa seda ta gama primary gaba ɗaya sedai batun ilimin addini kuwa babu shi dan tun da ta bar manya ba wanda ya kuma tuna mata akwai abin bautawa da gaskiya wato Allah balle kuma akai ga su karatun Alkur'ani da hukunce hukuncen addinin Islam sedai a karan kanta ta riƙe yin Sallah dan sallah ce abu ɗaya da Nana ta fi jaddada mata fiye da komai hakan yasa duk zamanta a can bata manta da yin ta ba sedai yadda zata yi tan ne bata iya ba so take yin duk yadda taso kawai.

Dawowar ta da ƙyar kawu ya barta ta yi wata biyu a gida lokacin tana shekara goma ya kuma maida ta ƙasar Canada inda tayi karatun secondary gaba ɗaya har ta fara University kafin kuma tashi ɗaya ta gudo ta bar ƙasar shine haɗuwar su da Deeq a restaurant ɗin nan yake faɗar ta gudu  ba sanar wa sedai suka neme ta suka rasa.

Dawowar ta ta nemi admission a nan manya state University department ɗin law inda kuma a nan ta haɗu da duk ƙawayen ta kamar yadda muka ji a baya .

     *Wannan shine tarihin Kisnah*
                 (Mun dawo labari).

Shessheƙar kukan ta da yaji ya ƙara ƙarfi fiye da baya yasa ya juyo ya kai duban sa gare ta, daga zaunen da take ta ƙara takurewa kanta tsakankanin cinyoyin ta tana kukan ta da ya ɗan ƙara ƙarfi dan ta daɗe tana yin sa sedai be kai ƙarfin na yanzu ba.

Mamaki ne ya kama shi ganin yadda jikin ta yake rawa sosai kamar wadda aka watsawa ruwan sanyi a tsakiyar hunturu, gaba ɗaya se yaji jikin sa yayi sanyi, me ya same ta da take kuka haka, bata da lafiya ne ko me? Kamar wanda aka tunawa haka kalmar mara hankalin da ya kira ta ya dawo kansa, to ko shi take wa kuka? Amma in ze tuna an kira ta da kalmar da tafi wannan muni kuma be ko ga ta damu ba balle har ayi batun yin kuka? To amma in ba hakan take wa kuka ba ai ba abinda aka yi mata haka kuma iya sanin sa lafiyar ta ƙalau.

Kawar da kansa yayi daga kanta se kuma yaji baze iya ba, kiran sunan ta yayi a hankali sedai ko ɗagowa bata yi ba balle ta amsa hakan yasa ya sake kiran ta wannan karon cikin ɗan ɗaga murya, a hankali ta fara sassauta kukan har sautin ya dena fitowa gaba ɗaya sedai hawaye kafin kuma ta ɗago kanta gaba ɗaya ta sauke jajayen idon ta da kuka ya rina ya sauya musu kala.

Seda ya ɗan firgita ganin yadda kyawawan fararen sexy eyes ɗin ta suka koma kala mara daɗin kallo, kafe shi tayi da su taƙi janye wa har lokacin kuma hawayen ta basu tsaya ba se shine yayi ƙarfin halin kau da nasa kafin ya shiga mata magana cikin sanyaya Murya

"Lafiya?, me ya same ki?, Wani abun akayi miki?".

Girgiza masa kai tayi alamar a'a dan tasan ko tace tayi masa magana ba iyawa zata yi ba yadda Muryar ta ya dishe haka kuma bata saba faɗawa kowa damuwar ta ba bata kuma jin zata fara yau, a kaf rayuwar ta tana barin damuwar ta a ranta ne dan ba wanda take dashi da zarai sharing dashi, a haka ta taso har girma shiyasa hakan ya zame mata ɗabi'a yayinda take samar wa kanta mafita irin wadda taga ta dace,  bata san me zata ce an yi mata ba tunda ba'a yi mata ɗin ba shiyasa kawai ta zaɓi girgaza masa kan.

SARAKI (The Accused Prince) ✅Where stories live. Discover now