Page 1️⃣6️⃣
________________________📖 Sallar Isha ya idar a masallaci amma be dawo ba se da ya gama duk tasbih ɗin da ya saba, fitowa yayi a hankali ya saka takalmin sa ya nufi komawa gidan yana me duba agogon hannun shi, its 8:45 pm.
Yana shiga compound wayar da aka kawo masa ɗazu me kyau da ita madaidaiciyar Android kamfanin Samsung matsayin wayar da ake bawa kowane ma'aikaci da sim da komai ta fara ringing, ɗan kallon screen ɗin yayi kafin yai sliding ya amsa
"Ya Saraki ka fito da motar gani nan fitowa"
"Okay" yace yana ending call ɗin tare da ƙarasawa ɗakin sa ya ɗauki key ɗin motar da kuma kuɗin da ta bashi ɗazu dan yana son yin siyayya.
Warming up motar yayi kafin ya matsa da ita kusa da flat ɗin nasu ya kashe yana jiran fitowar ta.Cikin wata dark blue ɗin guntuwar gown iya ƙasan gwiwa kaɗan ta fito, rigar tasha adon silver stones masu matuƙar kyau se ɗaukar ido take tana walwali, gashin kanta parke cikin blue ribbon se ta sake shi ta baya kana ta ɗora p-cap akai, kyakkyawar farar ƙafarta kuwa sanye take cikin dogon blue Hill shoe da igiyoyin sa suka kai har kusan rabin ƙaurin ta, kyawawan hannun ta saye da agogo shima dari blue se ɗayan da ta sakawa siririyar sarƙar hannu ta kuma ƙawata yatsun ta da zobuna.
Tun da ta fito ƙamshin ta ya cika ko ina a harabar gidan har ya kai ga hancin Saraki da ya saukar da glass ɗin side ɗin sa, girgiza kai kawai yayi yana mata addu'ar shiriya dan tabbas saka irin waɗannan turaren dole ya haddasa fitina a ban ƙasa.
Tun a ɗazu da ta kira shi da Ya Saraki yaji wani irin abu ya tsarga masa, ba abun da yazo ransa a lokacin face ƙanwar sa ɗaya tilo da ita kaɗai ce mace dake kiran sa da sunan, hakan yasa yaji a ransa kamar ita ɗin ce ta kira shi sedai yasan ba itan bace, tun a lokacin yaji a ransa wata ƙanwar ce ya samu, ƙani, ƙanwa, yaya mace, wa namiji kai har ma iyaye ana iya samun su a duniya base wanda kake da blood relation ne kaɗai family ba, a hadisai da ayoyi da dama Allah da Manzon sa sun nuna mana so da ƙaunar juna, sun nuna mana duk wani musulmi ɗan uwan musulmi ne dan haka ya amshe ta as ƙanwa kamar Miemie da suka fito ciki ɗaya da baze iya barin any harm yaje gate ta ba, haka baze so yaga rayuwar ta ta lalace ba, he'll treat her as an elder brother that will protect his little sister ko ta wane hali sedai yasan for now ba komai zece dole ze yi magana kan se ta gyara ba dan abun ya riga ya shiga jikin ta da dole se an bi a hankali.
Cikin wannan tunanin yayi nisa da har be san ma ta ƙara so har ta shiga ba se da ta bubbuga bayan kujerar da yake kai tana kiran sunan sa
"Yaa Saraki mana, am late fa".
Buɗe ido yayi a kanta kafin ya bi shigar jikin ta da ido sannan ya janye ya maida fuskar ta da ba wata kwalliya banda lip balm se mascara da eyeliner, kauda Kai yayi ya maida gaban motar yasa hannu ya kunna sannan ya nufi gate suka fice, seda suka hau titi sosai kafin ya ɗan kalle ta a kaikaice
"Zaki makara? Makaranta zaki je?".
"Wane irin makaranta a wannan late hours ɗin, clear screen cinema za muje".
Jijjiga kai kawai yayi ganin bata ma fahimci baƙar magana ya faɗa mata ba, be kuma cewa komai ba har suka ƙarasa, be shiga parking lot ba ya tsaya a gefe kaɗan da gurin dan fita yake son yi
"Ya ka tsaya a nan, kaga fa zan daɗe kawai ka shigar da ita parking lot kar muyi blocking wasu".
Hakan da ta faɗa se ya tuna mata dasu Abeed da gaba ɗaya ta manta da batun su wanda ta san for sure suna nan a kulle dan in har bata sake su ba ba wanda ya isa yasa a sake su, dole yau insha Allah zata sa a sake su dan badan ta manta ba da tun kwana uku da ka masu zata sa ayi freeing din su.
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.