PAGE 5️⃣2️⃣

417 19 2
                                    

                          Page 5️⃣2️⃣








_________________________📖 kawu na gama parking Khamees ya taho da sauri ya buɗe masa mota ya matsa baya, fitowa kawun yayi yana baza babbar rigar sa dan fa likkafa ta cigaba kaya kam fallesu yake kamar ba gobe.

Yana fitowa Khamees ya matsa ya ɗau briefcase ɗin sa tare da rufe masa motar, seda ya raka shi har bakin ƙofar falon su kafin ya tsaya tare da miƙa masa jakar bayan ya durƙusa, karɓar jakar kawu yayi ze wuce Khamees ya tsaida shi

"Ga wannan Alhaji, masinjan kotu ne ya zo ya kawo yace a baka".

Cak kawu ya tsaya kafin ya juyo ya kalli takardar batare da ya karɓe ta daga hannun khamees ɗin ba ya shiga maimaita sunan kotu da ya ambata, tunani ya shiga yi kan me ya haɗa shi da kotu da har za'a aiko masa da takarda daga can, iya tunanin sa be hango ko tuno komai ba so kawai yasa hannu ya karɓa tare da wucewa ɗakin sa.

Ajiye takardar yayi ya shiga rage manyan kayan jikin sa kafin ya nemi waje ya zauna tare da ɗaukar takardar dan fa hankalin sa ya kasa kwanciya da ita, a hankali ya farke ta sedai ya kasa buɗe wa se aukin juya ta yake kan yi a hannun kafin ya iya buɗe ta da ƙyar, to abinka ga mara gaskiya.

Yana buɗe wa ya shiga karanta abinda ke rubuce gaban sa na ɗan faɗuwa, wani irin rawa jikin sa ya ɗauka da yasa takardar ta suɓuce daga hannun sa ta faɗi, ana ƙarar sa akan zargin kisar ƴar ɗan uwan sa.

Wani irin kakkauran miyau ya haɗiya da ƙyar yana zarar ido kamar wanda ke gaban kotun tun yanzu, tunanin wa yake ƙarar tasa ya sa ya kai hannun sa dake rawa ya ɗau takardar da ƙyar se dai ta kasa zama saboda yadda hannun sa ke ɓari, barin ta yayi  har ya ɗan samu nutsuwa kafin ya sake ɗauka.

Ai a mugun zabure ya miƙe tsaye ganin sunan dake kan takardar, anya kuwa idanun sa gaskiya suka nuna masa, kai anya ba makuwa yayi ba? In ba haka ba taya ya zega wannan suna? Lallai makuwa ɗin yayi.

Ajiyar zuciya ya sauke ya tashi zuwa banɗaki yayi wanka ya canja kayan sa zuwa marasa nauyi yaci abinci kafin ya tashi ya kuma ɗauko ta, shigowar Mommyn Maigado yasa ya dakata yana kallon ta, sanye cikin wata dakakkiyar shaddar da tasha aiki hannu da wuya har ƙasa.

Zama tayi a gefen sa cikin sakar masa makirar murmushi kafin ta shafi fuskar sa cikin kissa da kisisina, duban sa tayi tana kashe murya da ido

"Sannu da zuwa mu love, ashe ka dawo, naga almaun ma har kaci abinci ko?".

Gyaɗa mata kai yayi kawai ya shiga sake buɗe paper ɗin, ɗan leƙowa tayi da son karantawa sedai wurgin da yayi da takardar ya hana ta wannan access ɗin se tayi saurin cafewa ta ajiye tana kallon shi, hannu biyu a ka ya shiga kai da kawowa cikin matsanancin tashin hankali da ɗimuwa, wani irin rawa ƙafafun sa suka ɗiba da yasa yayi saurin kujerar kusa dashi ya kai zaune har lokacin hannun sa duk biyu ɗore a kansa.

Da sauri ta tashi ta koma kusa dashi tana ruƙo hannun sa ganin yadda gaba ɗaya ya fita hayyacin sa,

"Wai meke faruwa ne baban Maigado, meye ya tashi hankalin ka haka, faɗa min mana dan Allah".

Kallon ta yayi kamar ze ce wani abu se kuma taga yayi zumbur ya tashi, wayar sa ya ɗauko ya dawo ya miƙa mata bakin sa na ɓari ya shiga yi mata magana

"Ki..ki..ki..kirawo min Alh..ehm...ehm Alh Haladu".

Karɓar wayar tayi ta shiga logs ɗin ta tayi masa dialing number Alh Haladu ta saka a speaker sannan ta ajiye masa a hannun kujerar kusa dashi yadda zeji sosai.

Be amsa sallamar da Alh Haladu ke masa ba ya shiga bayyana masa dalilin kiran har lokacin jikin sa da Muryar sa gaba ɗaya rawa suke yi yanayin da ya alamtawa Alh Haladun tabbas akwai matsala.

SARAKI (The Accused Prince) ✅Where stories live. Discover now