Page 4️⃣6️⃣
______________________📖 Tun daga ranar Kisnah ta samu dama kan Saraki, su kwana tare rungume da juna da safe su karya tare su fita tare, da yamma kafin ya dawo ta gyara ɗaki ta gama girki tare da ɗaukan wanka na jan hankali dan ma bata da kayan matsu sosai haka kuma yaƙi siyo mata kayan kwalliya yace bai da kuɗi wanda ba wai babun bane baze siyo ta nemi kashe shi da ran sa bane.
Kullum last one hour ɗin ƙarshe na school Malama Hajara ke musu lecture akan rayuwar aure da yadda mace zata tafi da gidan auren ta, a wajen Kisnah kam ba abinda zata ce da Malama se godiya tare da fatan Allah ya saka mata da alkhairi, ɓangaren karatu ka alhamdulillah tana ganewa sosai haka kuma Saraki na taimaka wajen sake biya mata da yi mata dalla dalla yadda komai ze zauna a kanta, sosai yake ganin ƙoƙarin ta dan a yadda ta girma ba tare da ko Foundation na ilimin addini ba da wata ce ba zata dinga saurin iya wa ba kamar ita shiyasa so da yawa ya ke faɗin she's talented and gifted.
A hankali rayuwa ta dinga gudu batare da sun lura ba zuwa yanzu har sun shafe wata uku da kwanaki a garin na makwan, i zuwa wannan lokacin kuwa tuni Kisnah ta iya haɗa baƙi ta karanta rubutun larabci, dake tana da karambani Suratul baƙara ta fara koya da kanta, tana haɗa baƙi tana biyawa tare da saurarar audio a wayar ta, se gashi cikin yardar Allah har tayi nisa a suratul baƙara ɗin, ranar da saraki ya sani kuwa taga ɗumbin mamaki kan fuskar sa irin wanda bata taɓa gani ba, a ƙasa kuwa sun yi nisa dan har sun kai Suratul mulk haka shima a ƙarin da yake mata sun kawo suratul munafiƙun dan tun da ta iya baƙi ya faro mata daga hizib na bakwai wato suratul Rahman, ragowar littatafai kuwa har ta sauke Hadith na biyu yanzu suna ƙoƙarin shiga umdatul Ahkam ne, so da yawa in tana karatu Saraki kan zauna yana kallon ta ne kawai cikin tuno rayuwar da tayi a baya yana jinjina hukuncin Ubangiji me yin yadda yaso, ba wanda ze ga Kisnah a yanzu ya haɗa ga da ta baya sedai a kira su identical twins amma masu mabanbantan halayya da ɗabi'u.
Ɓangaren lakcar Malama kuwa har yanzu ana yi dan sun yi nisa sosai haka kuma tana ƙoƙarin ganin ta yi komai da Malama tace duk da da yawan abubuwa yana hanata yace baya so amma ba komai take denawa ba, a nashi ɓangaren ma alhamdulillah dan shagon shi kullum ƙara haɓaka yake yi yana samun cigaba, daga layukan nesa da su ma aiko yara ake shagon Ahmad me kanti kamar yadda suke ce masa dan yana da sauƙi da arha akan komai hakan kuma na ƙara jawo masa customers, yanzu kam har masu abincin siyarwa ke karɓar kaya wajen shi.
Rana ce ake ƙwallawa sosai yau da ta hana su maman habu zaman tsakar gida, tashin ta kenan daga bacci kasancewar yau Alhamis ba makaranta shiyasa ta samu damar yin baccin rana, miƙa ta saki a hankali tana ƙoƙarin ɗaga labulen ɗakin ta dan zuwa toilet hannun ta ɗauke da buga, doguwar riga ce mara nauyi a jikin ta da tabi jikin ta ta lafe dan shaking materials ne, mayafin rigar kawai ta saka a kanta dan a matse take da shiga toilet ɗin shiyasa bata tsaya neman hijab ba, da ɗan sauri ta ƙarasa toilet ɗin tana fatan Allah yasa ba su lalata shi ba dan kafin ta kwanta ta wanke shi da zata yi wanka.
Ba laifi ba'a ɓata shi sosai ba hakan yasa ta shige da sauri tare da rufo ƙofa, duk da ba wani kaca kaca aka yi masa ba bata iya tsugunna wa a floor ɗin ba dan malama ta faɗa musu amfani da toilet irin haka na kawo infection kuma ko ba haka ƙyankyamin ta baze barta ta iya tsugunnnawa ba, ruwa ta kwara wa jikin ta bayan ta gama fitsarin dan a tsaye tayi shi a jikin ta bayan ta ɗage rigar ta cire pant ɗin ta.
Fitowar ta yayi daidai da shigowar wata budurwa jaye da akwati, fara ce irin farin kantin nan dan gashi nan yayi mata dabbara dabbara, matsakaiciya ce dan bata fiya tsawo ba haka ba wata kyakkyawa bace, kadaran kadahan dai, kallo ɗaya Kisnah tayi mata ta ɗauke kai tayi hanyar dakin ta daidai lokacin da matan gidan suka fito kusan a tare jiyo sallamar budurwar, da kallo suka bi Kisnah dukkan su cikin ƙare mata kallo dan wannan shine karo na farko da suka ganta da irin wannan kayan masu bin jiki kuma ba hijab a tare da ita.
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.