Page 4️⃣9️⃣
_________________________📖 Yana fita ta shiga kallon wayar zuciyar ta na ƙissima mata wani abu, so take ta kauce sedai tuni zuciyar ta ta rinjaye ta ta kai hannu ta ɗau wayar tare da duba wanda ya kira shi ɗazu, number ce mara suna alamun ba'a yi saving ɗin ta ba, wani ƙarin shakku ta kuma ji akan kiran dan baya ajiye number mara suna haka a wayar sa se gashi taga wannan kuma da alamu ba baƙuwar number bace tun da ga kiran ta nan a logs jiya da shekaranjiya, da sauri ta jawo tata wayar ta kwafe number sannan ta ajiye ta tan a gefe ta shiga watsapp ɗin shi, messages ɗin da me number ta turo ba kaɗan bane so kawai ta karanta iya wanda zata iya kafin ya dawo wanda duk nuni ne kan son da take masa ya daure ya kula ta, duk yadda ranta ya kai ga ɓaci haka ta danne tare da maida masa wayar ta ajiye a inda ta ɗauka ta ɗau tata tayi saving number da investigation.
Ko da ya dawo bata nuna masa komai ba suka gama normal life activities ɗin su suka kwanta bacci bayan ya mata ƙari a karatun ta kamar yadda suka saba.
Ko da safe ma bata canja masa ba har ya gama hidimar shi ya fita kafin ta shiga ayyukan ta, sefa ta gama komai tayi wanka sannan ta jawo wayar ta kasance war ranar juma'a babu makaranta.
Number ta nemo cikin wayar ta ta ƙura mata ido tana shawarar abinda ya kamata tayi, kira zata yi ko kuwa tayi message ta watsapp ne?, da sauri ta bawa kanta amsar tayi watsapp message ze fi sauƙin dan in Kira ne ɓacin ranta kan iya rinjayar ta ta ɓata komai batare da ta kai ga gano wace ƴar iskar bace.
Cikin yarda da shawarar ta shiga Google play store tayi downloading watsapp da bata dashi dan tun da yace be yarda ta buɗe ba se ta ma manta da batun sa a ranta, yana gama installing ta shiga tayi register a take sannan ta nemo number ta tura mata da message
_"Assalamualaikum warahmatullah, barka da rana sis"_.
Ajiyar zuciya ta sauke tare da zama kan carpet tana jiran reply ganin me number na online, shiru shiru ayi mata reply amma ba'a yi ba har ta shafe ten Minutes da tura message ɗin, sake typing yikike tayi ta tura, kusan minti biyu kafin taga blue ticks alamun an buɗe messages ɗin kafin taga typing indicating ana shirin turo mata reply, ko da message ɗin ya shigo se da ta fi mintuna kafin tayi summoning courage tai clicking on enter,
_"Waslm, barka kadai, lafiya"._
Sake maimaita message ɗin tayi over and over kafin ta yardar wa kanta tabbas fa macece, shiru tayi tana sake bitar message ɗin a kan ta cikin shawarar me zata rubuta mata kafin wata dabara ta faɗo mata
_"ƙawata ce ta bani number ɗin ki dan naga wasu kaya kuma tace a wajen ki ta siya shine nima nake so."_
Wanann karon kam ba'a ɗau lokaci ba ta turo mata da reply
_"kaya wane iri, kayan abinci amma ko"_.
_"eh su fa, tace wai kina bada su kan farashi me sauƙi kuma wai kina bada jinga, ina nufin in aka bada rabin kuɗin se a cika ragowar rabin zuwa gaba"._
Haka ta samu kan ta da rubutawa cikin son confirming yanayin alaƙar ta da mijin ta.
_"tabbas haka ne sedai kamar ke baƙuwa bazan iya baki kaya ba kuɗi ba tun da ba sanin ki nayi ba, dole se kin samo wanda ze Miki guarantor".
_"okay to shikenan zan yi hakan insha Allah, amma kafin nan Please ki yi min voice note na sunan ki da kuma irin kayayyakin abincin da kike siyar wa ɗin dan na kunnawa mijina yaji ya tabbatar saboda ko da na faɗa masa cewa yayi wai wasa ƙawar tawa ke min"._
Batare da tunanin komai ba matar tayi voice message ɗin me nauyin mintuna goma ta turo, da ƙyar ta danni ranta ta tura mata thanks zata ji ta zuwa anjima, ta daɗe riƙe da wayar a hannun ta amma ta rasa ƙarfin gwiwar buɗewa, ganin tana ɓata lokaci gashi juma'a ce se iya dawowa soon yasa ta daure ta buɗe.
YOU ARE READING
SARAKI (The Accused Prince) ✅
General FictionSarauta and all its hypocritical actions.