PAGE 5️⃣8️⃣

490 18 9
                                    

                          Page 5️⃣8️⃣










_______________________📖 Wani irin busa da kiɗa ne ya sake gauraye harabar gidan Sarautar da yake ƙara sa Kisnah tana sake shigewa jikin sa, shikan sa he's feeling somehow ill at ease, after a full one and half year yau gashi ya dawo gidan su cikin family ɗin sa, gidan da aka kore shi a ciki bayan an ci masa zarafi an zubar masa da ƙima da daraja a idon jama'a, be san da wane idon yanzu ze dubi mutane ba after all that happens.

Buɗe ƙofar side ɗin sa da akayi yasa ya ɗago kansa da yayi resting a bayan kujera ya zubawa fuskar Kisnah ido cikin son janye ta sedai tun da idon sa ya sauka kanta yaji ya manta me yayi niyya, kallon beautiful, elegant and charming face ɗin ta yake admiring all that's contained in it, ƙura wa luscious lips ɗin ta ido yayi dan ba tun yau ba suke tsokane masa ido sedai yau ɗin nan that they're so wet with saliva and lipgloss se yake jin kamar ana jan shi towards them, a hankali ya dinga kusantar da fuskar sa towards her har ya zamana suna iya jin numfashin  juna, kamar kuma wanda aka kira ya ja baya da ɗan sauri yana sauke numfashi akai akai.

Se da ya daidaita kansa kafin ya shiga tapping bayan ta a hankali yana kiran sunan ta cikin siririyar low voice da yasa ta ji shigar kiran har tsakiyar kanta kafin tsigar jikin ta ya shiga tashi, a hankali ta buɗe idanun ta ta zuba masa take idanun su suka shige cikin na juna dan idan sa na kanta ne dama, wani irin duba suke wa junan su me ɗauke da zazzafar ƙauna da shaƙuwa sedai ga Saraki har wa yau be san yana son ta ba, basu dawo hayyacin su ba seda Jamal ya ƙaraso tare da kiran sunan yayan shi da ƙarfi dan suna zuwa driver ya fita ya bar motar, a ɗan daburce ya janye idanun sa ya mayar kan Jamal dake bakin ƙofar motar, danne dariyar sa yayi ganin yadda cikin ƙanƙanin lokaci idanun yayan nasa suka kaɗa sun canja kala ya shiga faɗa masa shi ake jira tun ɗazu, gyaɗa masa kai yayi kafin ya ɗan daidaita kansa ya fita daga motar bayan ya janye ta a jikin sa kana ya zaga ya inda take zaune ya buɗe mata ƙofar tare da miƙa mata hannun sa alamun ta sa nata a kai.

Cikin maɗaukakin farin cikin da take ji ta zuro ƙafarta a hankali kafin ta ɗora tafin hannun ta kan nasa, daga shi har ita seda suka saki ajiyar zuciya lokacin da ɗumin hannun junan su ya ratsa su, damƙe hannun ta yayi ya taimaka mata ta fito daga motar kana ya rufe ya taya ta gyara zaman doguwar rigar jikin ta da ta tattare saboda zaman mota, dogara wa ne suka kare su gaba da baya dan kar aga yarima guda da taya mace aiki a filin Allah.

Takawa suka shiga yi cikin ƙasaita da izzar da yana shigowa cikin gidan su yaji kamar an ƙara masa ita ne, Jamal na gefen hagun sa ita kuma na gefen daman sa, basu tsaya a ko ina ba se ƙofar sashen baban sa da ya tabbatar kowa yana can ana jiran sa, da sallama suka saka kai dan shiga falon sedai tuni tashi ta maƙale jin sa jikin mahaifiyar sa, farin cikin sa, alfaharin sa haka kuma rayuwar sa, wani irin rauni ne ya lulluɓe shi a lokacin jin yadda take sake ƙanƙame shi with every strenght she got, kukan ta ke ratsa shi yana jin kamar ana sa guduma ana dukan sa ne hakan yasa ya rasa duk wani ƙarfi nasa, hannun wa sa yasa ya zagaye ta giving her more access to him, sun daɗe a haka kafin Mami ta sake shi tana murmushin dariya ga kuma hawaye da ya kasa tsayawa a fuskar ta, kallon sa take yi ganin yadda ya ƙara girma a idanun ta looking so adorable and responsible fiye da lokacin da ya bar gida, da ƙyar ta iya dena kallon sa kafin ta ja hannun sa zuwa gaban mahaifin sa dake zaune yana kallon su fuska cike da farin ciki, har ƙasa ya durƙusa cikin gaisar da Mahaifin nasa sedai be amsa ba se hannu da yasa ya ɗago shi ya rungume shi, bubbuga bayan sa Abiy ya shiga yi alamun ban haƙuri wanda shi Sarakin ya gane dan kusan ya san duk wata halayya ta mahaifin sa, janye jikin sa yayi ya ruƙo duka hannun Abiy ya haɗa da nasa kana ya shiga girgiza masa kai alamun ya dena bashi haƙuri kafin ya sake rungume baban nashi.

Seda duk suka rungume rungumen su  shi da ƙannen sa tare da lallashin masu kuka kafin ya ɗaga ido cikin neman Kisnah, can ƙofar falo ya hango ta tsaye har lokacin kanta a ƙasa bata iya ɗagowa ta kalli kowa da ke ɗakin ba haka bata zauna ba  dan ba'a bata izini ba, da sauri ya sake hannun princess ya na miƙewa, da tambayar ina zashi duk suka bishi sedai be amsawa kowa ba ya ƙara sa inda take wanda se lokacin jama'ar falon suka ankare da ita, hannun f aya kamo hakan yasa ta ɗan ɗaga kai kaɗan ta kalle shi kafin ta maida kanta yadda yake, jan ta ya shiga yi har ya ƙaraso da ita tsakiyar falon inda kusan duka ƴaƴa ke zaune kan carpet ya zauna tare da zaunar da ita gefen sa hakan ya saka ruɗani sosai a zuƙatan iyayen sa da ƴan uwan sa banda Jamal da ya san komai.

SARAKI (The Accused Prince) ✅Donde viven las historias. Descúbrelo ahora